Aƙalla mutum 29 ne suka mutu yayin da kusan 30 suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a yankin Morogoro da ke gabashin Tanzania.
'Yansanda sun ce hatsarin ya faru ne bayan wata babbar mota ɗauke da itatuwa ta yi yunƙurin wuce wata mota, inda ta yi karo da wata motar fasinja.
Motar fasinjan ta kama da wuta nan take, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 28 da ke cikinta, yayin da mutum ɗaya a cikin babbar motar shi ma ya mutu.
Mutanen da suka jikkata na samun kulawa a asibiti, yayin da jami'ai ke ƙoƙarin gano waɗanda suka mutu.
A wani hatsari na daban da ya faru a yankin a wannan rana, mutum huɗu ciki har da 'yansanda uku sun mutu, yayin da wasu bakwai suka jikkata.
Zan ɗauki matakan kawo ƙarshen yaƙin Iran - Putin
Asalin hoton, AFP via Getty Images
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce ƙasarsa a shirye take ta ɗauki "duk matakan da suka dace" domin taimakawa wajen kawo ƙarshen yaƙin Iran.
Putin ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da shugaban Iran Masoud Pezeshkian a Turkmenistan, inda ya ce Rasha za ta yi duk mai yiwuwa domin warware rikicin.
Ya kuma yi zargin cewa Iran ba ita ce ta haddasa rikicin ba, tare da yaba ci gaban dangantaka tsakanin Tehran da Moscow.
A nasa ɓangaren, Pezeshkian ya ce Iran na ci gaba da neman mafita ta hanyar tattaunawa da Amurka, amma ya jaddada cewa ƙasarsa ba za ta amince da matakan bai-ɗaya ba.
Ya kuma ce burinsu shi ne kawo ƙarshen yaƙin tare da kare haƙƙin al'ummar Iran bisa dokokin ƙasa da ƙasa.
NDLEA ta gano bindigogi 40 da jabun takardun kuɗi a Kogi
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Hana Sha
da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) reshen Jihar Kogi ta ce ta kama
sama da tan 10 na miyagun ƙwayoyi tare da ƙwato bindigogi 40 da harsasai 874
daga waɗanda ake zargi da fataucin miyagun ƙwayoyi tun daga ƙarshen shekarar
2025.
Hukumar ta kuma
ƙwato jabun takardun kuɗi na Naira, Dala da Fam, da kuma jabun magunguna, waɗanda
aka miƙa wa hukumomin da suka dace domin ci gaba da bincike.
Shugaban hukumar NDLEA
a jihar, Mista Umar Yahuza, ne ya bayyana hakan a Lokoja yayin da yake zantawa
da manema labarai jim kaɗan bayan miƙa makaman da harsasan da aka ƙwato ga
Cibiyar Kula da Ƙananan Makamai da Ƙananan Makamai.
Daily Trust ta ruwaito cewa makaman da aka ƙwato sun haɗa da bindigogi ƙanana guda biyar da wasu bindigogi
35. Ya ce an kama mutane da dama da ake zargi da hannu a fataucin miyagun
ƙwayoyi da sauran laifuka masu alaƙa da hakan a tsukin lokacin.
Ya ƙara da cewa
da yawa daga cikin waɗanda ake zargin suna fuskantar shari’a a Babbar Kotun
Tarayya da ke Lokoja, inda maza suka kai sama da kashi 80 cikin 100 na masu
fuskantar tuhumar.
Yahuza ya ce
miyagun ƙwayoyin da aka kama sun haɗa da tramadol, hodar Iblis, methamphetamine
da tabar wiwi inda tabar wiwi ta fi yawa a cikin adadin da aka kama.
Ya bayyana cewa
an ƙwato wasu daga cikin makaman ne daga hannun mutanen da ake zargi da noman
tabar wiwi, waɗanda suka mallaki makaman domin tunkarar jami’an tsaro yayin
ayyukan sintiri da kama masu laifi.
Shugaban NDLEA na
jihar ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da yaƙi da masu fataucin
miyagun ƙwayoyi da sauran masu aikata laifuka. Ya kuma buƙaci jama’a su riƙa
bai wa hukumomin tsaro bayanan da za su taimaka wajen yaƙi da laifuka.
Haka kuma ya
gargadi mazauna jihar da su guji taimaka wa masu laifi, yana mai jaddada cewa
fataucin miyagun ƙwayoyi da amfani da su ba bisa ƙa’ida ba na ƙara haddasa
matsalolin tsaro, garkuwa da mutane da sauran laifuka a cikin al’umma
An rufe wasu makarantun Malaysia sakamakon hayaƙi daga gobarar daji
An rufe makarantu a wasu jihohin Malaysia a yau Juma'a,
sakamakon hayaki daga gobarar daji a Indonesia, wanda ya sa gurbatar iska ta
kai matakin da ke barazana ga lafiya.
Yankunan da lamarin ya shafa sun haɗa da babban birnin ƙasar,
Kuala Lumpur, da kuma cibiyar gudanarwar gwamnati ta Putrajaya.
A Singapore ma,
an samu gurbacewar iska mafi muni a kasar.
Indonesia na fama
da gobarar daji mafi muni a cikin sama da shekara goma.
Za a nuna hukuncin kisa ta hanyar harbi kai tsaye a Amurka
Asalin hoton, AFP via Getty Images
Sakataren harkokin Tsaron Amurka,
Pete Hegseth, ya ce za a bai wa jama'a damar kallon yadda za a zartar da
hukuncin kisa ta hanyar harbi kan Nidal Hasan, wanda aka samu da laifin kai
harin bindiga a sansanin sojin Fort Hood a shekarar 2009.
Wani jami'in ma'aikatar tsaron
Amurka ya tabbatar da cewa za a watsa yadda za a zartar da hukuncin kai tsaye
ta intanet.
Hasan, wanda tsohon likitan masu
fama da matsalar ƙwaƙwalwa ne a rundunar sojin Amurka, ya kashe sojoji 13 tare da
raunata wasu 32 a harin da ya kai a Fort Hood da ke jihar Texas.
Wakiliyar BBC ta ce an shirya
zartar da hukuncin kisan ne a sansanin soja na Fort Hood da ke jihar Texas a
ranar 3 ga watan Disamba, kuma zai zama karo na farko da sojin Amurka za su
zartar da hukuncin kisa ta hanyar harbi tun bayan kawo karshen Yaƙin Duniya na
Biyu
Salam Alaikum!
Masu bin mu a wannan shafi na Kai Tsaye da BBC Hausa ke kawo muku a kowace rana, barka da warhaka.
Da fatan mun wayi gari lafiya. Kamar kodayaushe, a yau ma za mu ci gaba da kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a duniya – musamman a Najeriya da ƙasashe maƙwabta.
Za ku iya garzayawa shafukanmu na sada zumunta – Fesbuk da Tuwita da kuma Instagram inda a nan ma muka wallafa ƙarin labarai da bidiyo.