Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 16/10/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Juma'a 16 ga watan Oktoban 2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Badriyya Kalarawi

  1. Muna shirya yaƙi ta sama ko ta ƙasa ko ta ruwa - Iran

    Mostafa Izadi, mataimakin kwamandan dakarun Juyin-Juya-Halin Musulunci na Iran (IRGC), ya ce rundunonin sojin Iran suna cikin cikakken shiri a dukkan fannoni na gwabza yaƙi.

    Ya ce: "Dakarunmu suna shirye a dukkan ɓangarori: ko ta ƙasa ko ta teku ko ta sama, da ma ɓangaren tsaro da kariyar ƙasa baki ɗaya, kuma an gina ƙaƙƙarfan garkuwar kariya a faɗin ƙasar."

    A cewarsa, idan wata ƙasa ta kai wa Iran hari, za su ci gaba da ƙoƙari wajen kare ƙasar har zuwa ƙarshe.

    Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito Izadi yana cewa:

    "Idan maƙiyi ya kai wa ƙasarmu hari, za mu yi tsayin daka mu kare ta har zuwa ƙarshe."

    Jami'in na IRGC ya kuma ƙara da cewa: "Maƙiyi yana cikin mawuyacin hali, kuma domin ya ɓoye wannan yanayi ne yake ci gaba da yin sabbin ikirari da zarge-zarge lokaci zuwa lokaci."

  2. Barka da Juma'a

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa, barkanmu da safiyar yau Juma'a.

    Kamar kullum, yau ma shafin zai kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar, da yankin Gabas ta Tsakiya da ma duniya bakiɗaya.

    Za kuma ku iya leƙa shafukanmu na sada zumunta kamar Fesbuk da X da Instagram da ma Youtube domin kallon bidiyo da tafka muhawara.

    Da fatan za ku kasance tare da mu.