Dortmund na son ɗaukar aron Nwaneri daga Arsenal
Borussia Dortmund ta tuntuɓi Arsenal kan batun ɗaukar Ethan Nwaneri a matsayin aro zuwa ƙarshen kakar wasan bana.
Arsenal dai ta shirya barin Nwaneri ya tafi aro kafinrufe kasuwar musayar ƴan wasaa ranar Talata, kuma ana ci gaba da tattaunawa tsakanin ƙungiyar ta Premier League da takwararta ta Bundesliga.
An fahimci cewa Dortmund ta gabatar da tayi ga Arsenal, kuma ana sa ran za a yanke hukunci kan wannan tayi a gobe da safe.
A farkon wannan watan ne BBC Sport ta bayyana cewa Arsenal za ta fi ba da fifiko ga tayin ɗaukar Nwaneri a matsayin aro, kasancewar ƙungiyar ba ta son sayar da matashin ɗan wasan na ta kan yarjejeniyar dindindin.
Makomar ɗan wasan mai shekara 19 ta kasance batun da ake ta ce-ce-ku-ce a kai a wannan bazarar, inda matashin da ya taso daga makarantar horas da matasa ta Arsenal ya ja hankalin manyan ƙungiyoyi a gasar Premier League da sauran sassan Turai.