Manchester United ta fuskanci ɗaya daga cikin mafi munin wasa a gasar zakarun Turai a tarihinta bayan da Como ta doke ta 4-1 ranar Laraba, lamarin da ya ƙara matsin lamba kan kocin ƙungiyar, Michael Carrick, wanda ke cikin mawuyacin hali.
Kwana takwas bayan an zura mata ƙwallo a minti na farko a wasan da ta buga da Atletico Madrid, an sake karya tsaron bayanta cikin daƙiƙa 118 kacal a wannan wasa, inda fitaccen dan ƙasar Argentina, Nico Paz, ya ci ƙwallonsa ta farko cikin biyun da ya zura.
Hakan ya sa Manchester United ta zama ƙungiyar Ingila ta farko a tarihi da aka zura wa ƙwallo cikin mintuna biyun farko a jere a manyan wasannin Turai,
Lokacin da United ta lashe Champions League a karo na ƙarshe a shekarar 2008, Como tana buga wasa ne a Serie D. Wannan na nuna irin bambancin da ke tsakanin ƙungiyoyin biyu a yanzu.
Paz ya ci ƙwallaye biyu, sannan ya taimaka aka ci ta uku ta hannun Tasos Douvikas, kafin Jacobo Ramon ya ƙara ta huɗu da kai.
Kadan ya rage United ta yi kan-kan-kan da tarihi mafi muni da aka zura mata kwallo 5-0 a hannun Sporting ta Portugal a shekarar 1964.
An cire kyaftin ɗin ƙungiyar, Bruno Fernandes daga wasan aka saka Joshua Zirkzee, an kuma sauya Matheus Cunha da Andrey Santos daga fafatawar.
Zirkzee ya tsallake tarkon satar gida da ya bashi damar zare daya daf a tashi, har sai da aka duba VAR - amma dai Como ce ta yi nasarar cin 4-1 a Italiya.