Yadda sabon bashin dala biliyan 20 da Tinubu ke son karɓowa ya tayar da ƙura

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Ƴan hamayya da wasu masu sharhi kan harkokin tatalin arziki a Najeriya na ci gaba da sukar sabuwar buƙatar shugaban Najeriya Bola Tinubu ta karɓar sabon bashi.

A ranar Talata ne Shugaba Tinubu ya aike wa majalisar dokokin ƙasar sabuwar bukatar karɓo rancen dala biliyan 20.51 daga ƙasashen waje.

A cikin wasiƙar buƙatar da ya aike wa majalisar, Shugaba Tinubu ya ce za a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen magance matsalar ƙarancin kayayyaykin more rayuwa da kuma cike giɓin kuɗaɗen da ake nema a muhimman fannoni na tattalin arziki da walwalar jama'a.

Shugaba Tinubu ya ce fannonin da za a fi mayar da hankali a kansu sun haɗa da wutar lantarki da sufuri da kiwon lafiya da ilimi da noma da samar da ruwa da tsaro da samar da ayyukan yi da kuma gyaran tsarin tafiyar da harkokin kuɗi.

Ya kuma ce an zaɓi ayyukan ne bayan tantancesu, domin tabbatar da cewa za su taimaka wajen rage talauci, bunƙasa ƙwarewa da sana'o'i, da kuma ƙarfafa samar da abinci a ƙasar.

A cikin wasiƙar, Tinubu ya ce ya miƙa wa Majalisar Dokoki buƙatar neman ƙarin rancen ne domin ta samu damar amincewa da wuri, saboda a fara aiwatar da ayyukan da aka tsara.

To sai shirin ya gamu da sukar yan hamayya, waɗanda ke zargin gwamnatin da ɓoye bayanan ainihin abin da za ta yi da kuɗin.

Martanin Atiku Abubakar

Jagoran hamayyar ƙasar, kuma ɗantakarar shugaban ƙasar na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya buƙaci Majalisar Dokokin ƙasar kada ta amince da buƙatar sabon bashin har sai gwamnatinsa ta bayyana cikakkun bayanan ayyukan da za a aiwatar da kuɗaɗen.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Atiku ya ce bai kamata majalisar ta amince da "ko dala ɗaya ba" sai gwamnati ta fitar da bayanan kowane aiki ko kwangila da kuɗin gudanarwa da sunan ɗan ƙwangila da sharuɗɗan bashin da kuma yadda za a biya shi.

Sanarawar ta kuma ce Atiku ya ce wannan buƙatar ta tabbatar da gargaɗin da ya yi tun ranar 12 ga Oktoba kan shirin gwamnatin na neman bashin da zai kai kusan dala biliyan 20.

Ya kuma soki Shugaba Tinubu bisa rashin gabatar da cikakken bayani kan yadda za a kashe kuɗaɗen bashin, yana mai cewa ambaton manyan fannoni kawai bai isa ya tabbatar da dacewar neman irin wannan gagarumin bashi ba.

Me jam'iyyar NDC ta ce?

Ita ma jam'iyyar NDC ta soki shirin karɓo bashin, tana mai cewa babu da hakan zai ƙara wa Najeriya illa koma-baya.

A hirarsa da BBC daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar, Ibrahim Hussaini Abdulkarim ya zargi gwamnatin Tinubu da mayar da Najeriya ƙasar da ta mayar da hankali wajen cin bashi.

''Ƙasa ce ta rikici kullum ba abin da ake ji sai neman bashi, wannan al'amari ya sa ƴan ƙasar sun rikici'', in ji shi,

Ya ƙara da cewa jam'iyyarsu na mamakin yadda gwamnatin ƙasar, wadda ta ce ta ɗauki matakan inganta tattalin arziki amma ta koma ci gaba da karɓo bashi.

''Gwamnatin ce fa ta cire tallafin man fetur, ta kuma ƙara kuɗin haraji, duk a yunƙurinta na inganta tattalin arziki, amma kuma har yanzu ta ci gaba da karɓo bashin manyan kuɗaɗe'', in ji Shi.

Me masana tattalin arziki ke cewa?

Dokta Murtala Abdullahi Kwara, malami a Jami'ar Umaru Musa Ƴar'adua da ke Katsina ya ce buƙatar shugaban ƙasar na karɓo sabon bashi bai ba shi mamaki ba.

''Ai dama idan an tuna a kasafin kuɗin da shugaban ya gabatar a shekarar da ta gabata ya nuna cewa kaso mai yawa na kudin kasafin za a samu su ne ta hanyar bashi'', in ji shi.

Wasu ƴan ƙasar da dama dai na zargin gwamnatin da rashin amfani da kuɗaɗen bashin ta hanyar da ta dace, wani abu da Dokta Kwara ya ce suna da hujjar yin hakan.

''Gwamnatin da ta kwashe fiye da shekara uku a kan karagar mulki ba ta iya aiwatar da kashi 30 na kasafin kuɗin da take yi kowace shekara ba, ai kowane ɗan ƙasar zai fahimci cewa su ke kiɗansu kuma su yi rawansu'', in ji shi.

Masanin tattalin arzikin ya ci gaba da cewa ya kamata waɗanda ke amincewa da karɓo bashin su riƙa tambayar shugaban me ya yi da kuɗaɗen da ya karɓa a baya, kuma wane amfani zai yi da wanda zai karɓa yanzu.

Wane illa bashi ke yi wa Najeriya?

Dokta Murtala Abdullahi Ƙwara ya ce bashin da gwamnatin Najeriya ke ci gaba da karɓa na yi mata illa ta fannonin tattalin arziki da dama.

''Na farko a baya-bayan nan ne fa Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF ya ce kuɗin ruwan da ƙasar ke biya saboda basuka ya zarta kuɗin shigar da take samu'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa idan aka samu irin wannan yanayi to ƙasa na cikin barazanar tattalin arziki.

Haka ya ce idan ƙasa ta yi ƙaurin suna a karɓar bashi, to takan rasa ƙima a idanun duniya.

''Za kuma a samu ƙarin farashin dala da karyewar darajar kuɗin ƙasar, lamarin da zai haifar da ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi ga ƙasar'', in ji shi.

Hanyoyin da Najeriya za ta rage cin bashi

Masanin tattalin arzikin ya kuma lissafa wasu hanyoyin da yek ganin idan Najeriya za ta bi su, to za ta iya daina yawan cin bashi.

Hanya ta farko da malamin jami'ar ya bayyana ita ce magance matsalar tattalin arziki.

''Sannan kuma gwamnati ta tsaya ta yi wa kanta duba na tsakani ta rage yawan kuɗin da take kashewa wajen gudanar da harkokin mulki'', in ji malamin jami'ar.

Sannan kuma ta yi ƙoƙarin magance matsalar hauhawar farashin kayayyaki da samar da ayyukan yi ga ƴanƙasarta.