Wakilan Amurka za su gana da Putin a Moscow
Wakilan Shugaba Trump na musamman - Jared Kushner da Steve Witkoff - za su gana da Shugaba Vladimir Putin a birnin Moscow.
Matakin na zuwa ne bayan sun shiga tsakani a tattaunawar kwana biyu tsakanin wakilan Rasha da na Ukraine a birnin Abu Dhabi.
Ana sa ran wakilan na Amurka za su gabatar da shawarar faɗaɗa tattaunawa kan yaƙin na Ukraine, ta yadda za a sanya wakilan ƙasashen Turai a ciki.
Ya zuwa yanzu, Rasha ba ta nuna sha'awar karɓar wannan shawara ba.
Daga nan, wakilan biyu za su nufi ƙasar Ireland domin ganawa da Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, wanda a baya ya shaida wa manema labarai cewa gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen samun ci gaba a kan cimma yarjejeniya a cikin wannan shekarar.