'Muna fargabar El Niño za ta iya kashe mu'

    • Marubuci, Thomas Mukhwana
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa correspondent
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Wata mata mai shekara 62 da ke zaune a unguwar Kibera, ɗaya daga cikin manyan matsugunan marasa galihu a Kenya, ta bayyana fargabar da take ciki sakamakon yiwuwar sake samun mummunar ambaliyar ruwa a ƙasar.

Agnes Shikoli ta shaida wa BBC cewa har yanzu tana cikin damuwa kan ambaliyar da ta afku a watan Maris, wadda ta yi sanadin mutuwar ƙanwarta mai suna Beatrice Khalayi, mai shekara 58, tare da lalata gidaje da dama.

A cewarta, ruwan ambaliyar ya kai tsakiyar bangon gidanta, wanda ke kusa da kogin Ngong da ya ratsa unguwar Kibera a birnin Nairobi.

Har yanzu tana kallon ragowar ɓarnar da ambaliyar ta yi, ciki har da talabijin dinta da ruwan ya lalata.

Shikoli ta ce mutuwar ƙanwarta ta girgiza ta matuƙa.

Ta ce: "Duk lokacin da na ga hotonta, nakan shiga damuwa. Shi ya sa na ajiye hoton a inda ba zan riƙa ganinsa ba."

Yanzu haka, yayin da ake shiga lokacin daminar ƙarshen shekara a Kenya, Shikoli na fargabar yiwuwar sake samun ambaliyar ruwa sakamakon sauyin yanayi ta El Niño, wadda mas hasashen yanayi ke gargaɗin cewa za ta iya haddasa ruwan sama mai tsanani.

Ta ce: "Ina jin kamar wannan lamarin zai iya hallaka mu. Gidajen nan ba na duwatsu ba ne, za su iya rugujewa a kanmu, ko kuma ruwa ya iya nutsar da mu."

Gargaɗin yiwuwar ƙaruwar ruwan sama ya sa hukumomi da al'ummomi a Kenya kara kokarin rage illolin ambaliyar ruwa.

A unguwar Kibera, wasu ma'aikata sanye da rigunan kariya masu haske sun duƙufa wajen kwashe shara da tarkacen da suka taru a cikin kogin Ngong, domin hana su kawo cikas ga gudanar ruwa.

Aikin na ƙarƙashin wani shiri mai suna Climate Worx, wanda ke ƙarƙashin ofishin Shugaban Kenya, William Ruto, da nufin tsaftacewa da farfaɗo da kogunan birnin Nairobi.

An ƙara yawan ayyukan tsaftace kogunan tun daga watan Agusta, bayan gargaɗin masana yanayi kan yiwuwar El Niño ta bana ta haddasa mummunan yanayi.

Masana sun yi hasashen cewa guguwar El Niño ta bana na iya kasancewa cikin mafi ƙarfi da aka taɓa samu, kuma hakan na iya jawo matsanancin yanayi a sassa daban-daban na duniya.

A kudancin Kenya kuwa, babban abin damuwa shi ne yiwuwar samun ruwan sama mai yawa fiye da yadda aka saba, wanda ka iya sake haddasa ambaliyar ruwa da jefa rayukan al'umma cikin haɗari.

A halin yanzu, ana ci gaba da aikin cire tarkace da suka toshe magudanan ruwa a sassa daban-daban na birnin Nairobi, wanda ke da faɗin gaske kuma aka gina shi a kan tuddai, akwai kuma koguna uku manya da suka ratsa cikinsa.

Sai dai ma'aikatan da ke gudanar da aikin na fuskantar babban ƙalubale, ganin yawan tarkacen da suka toshe hanyoyin ruwa.

An ɗora alhakin yawan asarar rayukan da aka samu a ambaliyar farkon wannan shekara kan toshewar magudanan ruwa da kuma rashin ingantaccen tsarin zubar da shara. Hakan ya sa ruwan sama mai yawa ya kasa samun hanyar kwarara, wanda ya haifar da ambaliya.

Shugaban hukumar kula da bala'o'i ta jihar Nairobi, Bramwell Simiyu, ya shaida wa BBC cewa an shafe shekaru da dama ba tare da kula da magudanan ruwan ba.

Ya ce kwashe shara da tarkacen da suka toshe su zai taimaka wajen ceton rayukan jama'a tare da rage illolin ambaliya.

Unguwannin da ba su da ingantaccen tsarin gine-gine a Nairobi ne suka fi fuskantar barazanar ambaliya, musamman waɗanda ke kusa da koguna, kamar Kibera da Mathare.

A mafi yawan waɗannan unguwanni, gidaje na da tazarar ƴan mitoci kaɗan ne daga bakin koguna. Wasu mazauna, ciki har da Agnes Shikoli, sun gina gidajensu a gangaren da ke gefen kogunan sakamakon ci gaba da faɗaɗar waɗannan matsugunai.

Idan aka samu ambaliyar ruwa kwatsam, ruwan kan kwashe gidajen, lamarin da ke jefa rayukan waɗanda ke cikinsu cikin haɗari.

Wani babban ƙalubale shi ne yadda ba a sabunta tsarin magudanan ruwan Nairobi ba, duk da ƙaruwar al'umma da bunkasar gine-gine da ababen more rayuwa da aka samu cikin shekaru da dama.

Simiyu ya ce an tsara tsarin magudanan ruwan da ake amfani da shi yanzu ne kimanin shekara 30 da suka wuce, domin kula da birnin mai al'umma kusan miliyan 2.5.

Sai dai a cewarsa, yanzu birnin na ɗauke da mutane kusan miliyan bakwai da rana, yayin da adadin ke kai wa miliyan 5.5 da daddare.

Ya ƙara da cewa ana buƙatar zuba jarin da ya kai dala miliyan 192 domin sake gina tare da inganta tsarin magudanan ruwa da na zubar da shara baki ɗaya.

Sai dai har yanzu babu wata alama da ke nuna cewa gwamnatin tarayya ko ƙaramar hukumar birnin, waɗanda ke fama da ƙarancin kuɗade, za su iya samar da irin wannan maƙudan kuɗaɗe.

Wani shirin gwamnati mai suna Nairobi River Basin Regeneration Programme, wanda aka kafa domin farfaɗo da kogunan birnin, ya gano cewa gina matsugunai a kusa da koguna, tare da rashin tsaurara bin dokokin gine-gine, na ƙara haɗarin fuskantar ambaliya.

Shirin ya ba da shawarar samar da wani yanki na kariya a gefen koguna domin hana gine-gine kusantowa, da kuma mayar da al'ummomin da ke cikin haɗari zuwa wasu wurare cikin mutunci bisa la'akari da buƙatunsu.

Sai dai ƙaruwar talauci na daga cikin dalilan da ke tilasta wa mutane da dama zama a kusa da koguna, duk da haɗarin da hakan ke tattare da shi.

Simiyu ya ce bisa hasashen mafi munin yanayi, kimanin mutane 100,000 da ke zaune a unguwannin masu ƙaramin ƙarfi na iya fuskantar barazanar ambaliya.

Ya ƙara da cewa ko da a hasashen matsakaicin haɗari, kimanin gidaje 5,000, waɗanda ke ɗauke da mutane kusan 20,000, na iya kasancewa cikin barazana.

Har yanzu babu wanda ya san takamaiman lokacin da damina za ta fara sauka ko kuma yawan ruwan da za a samu a Kenya.

Sai dai hukumar hasashen yanayi ta ƙasar ta yi gargaɗin cewa watan Nuwamba ne aka fi samun ruwan sama mai yawa a lokacin daminar ƙarshen shekara, wadda yawanci take farawa daga Oktoba zuwa Disamba.

A wani hasashen yanayi da hukumar raya yankin gabashin Afirka ta IGAD ta fitar a watan Satumba, ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar kashi 81 cikin 100 na samun mummunan yanayi na El Niño mai tsananin ƙarfi tsakanin Oktoba da Disambar 2026.

Ko da yake ba a samu ruwan sama mai tsanani kamar yadda aka yi hasashe ba kawo yanzu, masana yanayi na ci gaba da nuna damuwa kan yiwuwar faruwar hakan.

A yankin gabashin Afirka, ana kwatanta El Niño ta bana da wadda aka samu a shekarun 1997 zuwa 1998, wadda ta haddasa mummunar ambaliya da ɓarna a ƙasashen Somalia da Kenya.

Wata mai hasashen yanayi, Jemima Gacheru, ta shaida wa BBC cewa dalilin yin wannan kwatanci shi ne kamanceceniyar yanayin zafin ruwan tekun Indiya a lokacin El Niño ta shekarar 1997 da kuma wanda ake samu a yanzu.

A cewarta, irin wannan sauyin yanayi a tekun Indiya na iya haifar da ruwan sama mai tsananin yawa.

Gacheru ta ce: "A wannan daminar, muna fuskantar El Niño mai matuƙar ƙarfi a tekun Pasifik, sannan kuma akwai wani sauyin yanayi mai ƙarfi a tekun Indiya da ake kira Indian Ocean Dipole."

Wannan yanayin, wanda wasu ke kira da 'Indian Niño', yana da alaƙa da bambancin zafin ruwan saman teku a ɓangarori biyu na tekun Indiya, kamar yadda El Niño ke faruwa a tekun Pasifik.

Ta ƙara da cewa ana sa ran samun ruwan sama mai yawa a sassa daban-daban na ƙasar.

A wani ɓangaren kuma, Hukumar Kula da Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM) ta yi gargaɗin cewa kusan mutane 900,000 a Kenya na iya rasa matsugunansu a bana, galibi sakamakon ambaliyar ruwan da ake hasashen za a samu.

Ƙasashen Afirka na fargabar illolin da El Niño za ta iya haifarwa

Kenya ba ita kaɗai ba ce ke cikin fargabar fuskantar illolin da sauyin yanayi ta El Niño za ta iya haifarwa ba, domin sauran kasashen Afirka ma na nuna damuwa kan barazanar da ke tafe.

A makwabciyarta Somalia, hukumar kula da bala'o'i ta ƙasar ta yi gargaɗin cewa kusan mutane miliyan 1.2 na fuskantar barazanar rasa matsugunansu sakamakon matsanancin sauyin yanayi, wanda zai iya haddasa ambaliyar ruwa da kuma fari.

Bayanan Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) sun nuna cewa ambaliyar ruwan da ta auku a Somalia a shekarar 1998 ta yi sanadin mutuwar mutane 2,000, yayin da wasu 250,000 suka tsere daga gidajensu.

Haka kuma, ambaliyar ta lalata kusan kashi 80 cikin 100 na amfanin gona a wasu sassan ƙasar.

Hukumar sa ido kan barazanar yunwa ta Majalisar Ɗinkin Duniya, IPC, ta kuma yi gargadin cewa akwai yiwuwar ƙaruwar matsalar ƙarancin abinci a Somalia, sakamakon matsalolin samar da kayayyaki da kuma tasirin El Niño da ka iya ƙara ta'azzara lamarin.

A wasu sassan nahiyar Afirka kuwa, masana hasashen yanayi na fargabar cewa El Niño za ta iya haddasa tsananin zafi da kuma tsawaita lokacin da ake ɗauka ba tare da samun ruwan sama ba.

Wannan na iya jefa manoma cikin mawuyacin hali a wasu sassan yammacin Afirka, musamman yankin Sahel mai ƙarancin ruwan sama da ke kudancin hamadar Sahara.

Haka kuma, ana fargabar irin wannan yanayi a kudancin nahiyar Afirka, inda ake ganin akwai babbar barazanar lalacewar amfanin gona sakamakon rashin isasshen ruwan sama.

Masana na kuma nuna damuwa kan cewa illolin El Niño za su iya ƙara tsananta matsalolin da al'ummomi da dama ke fuskanta tun tuni.

Alal misali, mazauna unguwanni irin su Kibera a Kenya na fama da matsalar gidaje marasa inganci da kuma tsananin talauci, yayin da wasu sassan Somalia ke fama da mummunan fari.