Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko alƙawarin miliyan 10 da Wike ya yi wa kansilolin APC ya saɓa dokar Najeriya?
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya yi alƙawarin ba wa kowanne kansila naira miliyan 10 idan Shugaba Bola Tinubu ya yi nasara a mazaɓarsa a babban zaɓen 2027.
Wannan ya haifar da muhawara mai zafi kan abin da dokokin Najeriya suka ce game da amfani da kuɗi wajen sayen ƙuri'u.
Wike ya yi alƙawarin ne a wani taron ƙungiyar Rainbow Coalition a ƙarƙashin ƙaramar hukumar Kwali da ke Abuja a ranar Litinin, domin ƙarfafa gwiwar kansilolin domin su tabbatar da nasarar Tinubu.
Ya ce: "Duk kansilan da ya sa Tinubu ya yi nasara a mazaɓarsa, zai samu naira miliyan 10 a matsayin la'ada."
Wasu na ganin irin wannan mataki ya saɓa wa kundin tsarin mulki da dokokin zaɓe, yayin da wasu kuma ke cewa ba haka ba ne.
Me dokar Najeriya ta ce?
Sashe na 22(c) na Dokar Zaɓe ta Najeriya ya bayyana cewa: "Duk wanda ya saya ko ya sayar da ƙuri'a, ko ya yi ikirarin saya ko sayar da ƙuri'a, ko da kansa ko a madadin wani, ya aikata laifi."
Hukuncin karya wannan doka shi ne tarar naira miliyan biyar ko ɗaurin shekaru biyu a gidan yari, ko kuma duka biyun. Haka kuma, ba zai iya tsayawa takarar wani muƙamin zaɓe a Najeriya ba na aƙalla shekaru goma.
A wani ɓangaren kuma, Sashe na 125 na Dokar Zaɓe ya yi magana kan cin hanci da rashawa da bayar da cin hanci yayin zaɓe.
Wannan sashe ya haramta wa mutum yin wata kyauta, ba da rance, alƙawari ko kulla wata yarjejeniya domin jan hankalin wani ya mara wa wani ɗan takara baya ko ya yi wani tasiri a zaɓe.
Sashe na 125(d) na Dokar Zaɓe ya ce: "Bayan zaɓe, duk wanda ya karɓi kuɗi ko wata aba mai daraja, ko da kansa ko ta hannun wani, saboda ya yi zaɓe ko bai yi zaɓe ba, ko kuma ya sa wani ya yi zaɓe ko bai yi zaɓe ba ga wani ɗan takara, ya aikata laifi."
Idan an same shi da laifi, hukuncin da zai fuskanta shi ne tarar naira miliyan biyu ko ɗaurin shekara guda a gidan yari, ko kuma duka biyun.
End of Lee akụkọ ndị ọzọ ga-amasị gị ebe a
Abin da masana shari'a ke cewa
Wani lauya, Inibehe Effiong, ya shaida wa BBC cewa alƙawarin da Nyesom Wike ya yi bai dace da doka ba.
Ya ce: "Abin da Minista Wike ya yi shi ne ƙoƙarin nemo hanyar sayen ƙuri'un 'yan Najeriya ta hanyar amfani da kansiloli da goyon bayansu."
Wani lauya kuma, wanda ya nemi a sakaye sunansa, ya ce: "A zahiri wannan shi ne abin da lamarin yake nufi, babu wata ma'ana dabam da za a iya ba shi."
Lauyan ya ƙara da cewa: "Wannan na iya haifar da wata yarjejeniya ko haɗin baki da zai sa a yi amfani da hanyoyi daban-daban, ciki har da cin hanci da tashin hankali, domin tabbatar da cewa shugaban ƙasa ya yi nasara a mazaɓunsu, domin su samu ladan naira miliyoyi masu yawa."
A zaɓen shugaban ƙasar Amurka na baya-bayan nan, Shugaba Donald Trump ya yi alƙawarin ba da dala 5,000 idan jam'iyyarsa ta Republican ta lashe rinjayen kujeru a majalisar dattawa da kuma majalisar wakilai.
Lauyan ya kuma ce kaɗa ƙuri'a a tsarin dimokuraɗiyya ya kamata ya kasance bisa ra'ayi da zabin mutum, ba wai saboda alƙawarin samun kyauta ko wata lada ba.
Me ƴan Najeriya ke cewa?
'Yan Najeriya da dama sun ce ya kamata hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta gwamnati ta binciki kalaman Nyesom Wike, saboda suna ganin sun saɓa wa doka.
Wasu kuma sun ce wannan ya nuna cewa Wike na fargabar cewa Shugaba Bola Tinubu na iya shan kaye a zaɓen shekarar 2027. Sai dai akwai waɗanda suka ce babu wani laifi a cikin kalaman nasa.
A cewar mai sharhi mai suna SportsDoctor, Jihar Rivers tana da kansiloli 319. Idan dukkansu suka sa jam'iyyar ta yi nasara a mazaɓunsu, hakan na nufin Wike zai biya jimillar naira biliyan 3.19.
Ya rubuta cewa: "Idan EFCC na gudanar da aikinta yadda ya kamata, ya kamata ta binciki wannan batu."
Wani mutum mai suna Moses Paul, wanda kuma fitaccen mai goyon bayan tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ne, ya rubuta cewa:
"Dimokuraɗiyya ba kasuwanci ba ce. Ƙarfin jama'a ba hajjar da ake saye a kasuwa ba ce. Babu wani ɗan siyasa da ke da ikon sayen lamirin al'umma ko ikon kaɗa ƙuri'arsu."
Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya ce Wike bai karya wata doka ba. Ya ce bai ba kowa kuɗi domin ya sayar da ƙuri'arsa ba, sai dai ya ƙarfafa wa mambobin jam'iyyarsa gwiwa ne su yi aiki tukuru domin tabbatar da nasarar Shugaba Tinubu a zaɓen.