Jiragen sojin Amurka sun fice daga sansanin Sojin Bitaniya
Aƙalla jiragen saman sojin saman Amurka guda goma masu ɗaukar man fetur sun bar wani sansanin soji da ke Birtaniya, inda bayanan sa ido kan zirga-zirgar jirage suka nuna an mayar da su zuwa wasu sansanonin Amurka da ke Turai.
Jaridar Wall Street Journal ta ruwaito cewa an kwashe jiragen ne daga sansanin RAF Mildenhall da ke gabashin Ingila saboda wata barazana daga Iran, sai dai ba a tabbatar da hakan a hukumance ba.
Ficewar jiragen a ranar Litinin na zuwa ne makonni kaɗan bayan da Amurka ta janye wasu jiragen yaƙi masu ɗaukar bama-bamai daga wani sansanin soji a Birtaniya, sakamakon wata barazanar tsaro da ake zargin tana da alaƙa da Iran.
Gwamnatin Birtaniya ta ce sansanonin sojinta na da tsaro, kuma ta jaddada cewa ana ci gaba da nazarin barazanar tsaron tare da ɗaukar matakan kariya akai-akai.