Fitattun ƴansiyasar Najeriya 6 da ke takara tun 2003

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Yayin da ake tunkarar babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027, an sake fara nazari kan wasu fitattun ƴan siyasa da suka shafe shekaru suna neman samun wasu muƙaman zaɓe, amma har yanzu ba su cimma burinsu ba.

Tun bayan komawar Najeriya kan tafarkin mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999, bayan shekaru masu yawa na mulkin soja da juyin mulki, ƴan siyasa da dama sun dinga fafutukar neman manyan muƙamai ta hanyar zaɓe.

A zaɓen shekarar 1999 ne aka zaɓi Olusegun Obasanjo a matsayin shugaban ƙasa, lamarin da ya buɗe sabon babi a siyasar ƙasar. Tun daga lokacin ne wasu ƴan siyasa suka rika neman wasu muƙamai da dama amma suka kasa samun nasara, yayin da wasu kuma suka samu wasu mukaman daban ba wanda suka fi so ba.

Wannan rahoton ya yi nazari kan wasu daga cikin fitattun ƴan siyasar da suka daɗe suna neman takara ko kuma neman wani muƙamin zaɓe tun shekarar 2003.

Atiku Abubakar

Ko da yake Atiku Abubakar ya zama mataimakin shugaban ƙasar Najeriya a ƙarƙashin shugabancin Olusegun Obasanjo, tarihin siyasarsa ya nuna cewa babban burinsa shi ne zama shugaban ƙasa.

Tun kafin komawar Najeriya kan mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999, Atiku ya yi takarar neman kujerar shugaban ƙasa a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar SDP, wanda daga ƙarshe aka tsayar da Moshood Abiola a matsayin ɗan takara a zaɓen 12 ga Yunin 1993.

Ko da yake an gudanar da zaɓen kuma mafi yawan ra'ayoyi na nuna cewa Abiola ne ya yi nasara, gwamnatin mulkin soja ta Ibrahim Babangida ta soke sakamakon zaɓen tare da ci gaba da riƙe madafun iko.

A lokacin da sojoji suka shirya miƙa mulki ga farar hula, Atiku ya yi takarar gwamnan jihar Adamawa a ƙarƙashin jam'iyyar PDP kuma ya samu nasara. Sai dai daga baya Obasanjo ya zaɓe shi a matsayin abokin takararsa, lamarin da ya sa ya zama mataimakin shugaban ƙasa bayan nasarar da suka samu a zaɓen 1999.

Da wa'adin mulkin Obasanjo ya zo ƙarshe a 2007, Atiku ya nemi tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP amma ya sha kaye a hannun marigayi Umaru Musa Yar'Adua.

Tun daga wannan lokaci, sunan tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kasance cikin jerin ƴan siyasar da ke neman zama shugaban ƙasa a kusan kowace zagayowar zaɓe. Ya tsaya takara a ƙarƙashin PDP a zaɓen 2023, sannan a yanzu a zaɓen 2027 yana neman shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar ADC.

Donald Duke

Bayan kammala wa'adinsa na biyu a matsayin gwamnan jihar Cross River a shekarar 2007, Donald Duke ya mayar da hankali kan kujerar shugaban ƙasar Najeriya.

A shekarar 2007 ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, sai dai daga bisani ya janye daga takarar tare da mara wa Umaru Musa Yar'Adua baya, wanda daga ƙarshe ya lashe zaɓen.

Daga baya, a zaɓen shekarar 2019, Duke ya sake neman shugabancin ƙasar a ƙarƙashin jam'iyyar SDP, amma bai samu nasara ba.

Yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027, Donald Duke shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PRP.

Peter Obi

Peter Obi na cikin fitattun ƴan siyasar Najeriya da suka daɗe suna neman manyan muƙamai a duk lokacin da za a yi zaɓe.

Kafin ya shiga takarar shugaban ƙasa, ya yi gwamnan jihar Anambra daga shekarar 2006 zuwa 2014, bayan da aka sake zaɓensa karo na biyu.

A zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2019, ya yi mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar PDP.

Daga baya kuma ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2023 a ƙarƙashin jam'iyyar Labour Party, inda ya zo na uku a sakamakon zaɓen.

A yanzu a zaɓen 2027, Peter Obi na neman shugabancin ƙasar a ƙarƙashin jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC).

Adamu Maina Waziri

Adamu Maina Waziri na daga cikin ƴan siyasar da suka shafe shekaru suna neman samun kujerar gwamnan jihar Yobe, amma ba su yi nasara ba.

A zaɓukan shekarun 2003 da 2007, ya tsaya takarar gwamna a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, sai dai ya sha kaye a hannun ƴan takarar jam'iyyar ANPP.

A shekarar 2011, ya sake yunƙurin zama ɗan takarar gwamna na PDP, amma ya sha kaye a zaɓen fidda gwani da Usman Albishir. Daga baya, a shekarar 2015, ya samu tikitin takarar gwamna na jam'iyyar PDP, amma bai lashe babban zaɓen ba, inda Ibrahim Gaidam na jam'iyyar APC ya yi nasara.

A zaɓen shekarar 2019, Waziri ya sauya akala zuwa takarar kujerar Sanata. Sai dai duk da cewa wani ɓangare na jam'iyyar PDP ya bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani, Hukumar Zaɓe ta INEC ba ta amince da shi a matsayin halastaccen ɗan takarar jam'iyyar ba.

A zaɓen 2027, Adamu Maina Waziri, wanda ya taɓa riƙe muƙamin minista sau biyu a gwamnatin tarayya, na neman takarar kujerar ɗan majalisar wakilai a ƙarƙashin jam'iyyar ADC.

Sanata Rabiu Kwankwaso

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na daga cikin fitattun ƴan siyasar Najeriya da suka nemi shugabancin ƙasa sau da dama a tsarin mulkin dimokuraɗiyya na ƙasar.

Kwankwaso ya yi gwamnan jihar Kano a wa'adi biyu, daga 1999 zuwa 2003 da kuma daga 2011 zuwa 2015. Ya kuma riƙe muƙamin ministan tsaro, sannan ya wakilci Kano ta Tsakiya a majalisar dattawa.

A shekarar 2014, Kwankwaso ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar APC domin zaɓen 2015, amma Muhammadu Buhari, ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa. Bayan haka, Kwankwaso ya mara wa Buhari baya a zaɓen.

Daga baya ya koma jam'iyyar PDP, inda ya sake neman tikitin takarar shugaban ƙasa a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar gabanin zaɓen 2019, amma bai samu nasara ba.

A zaɓen shekarar 2023 kuwa, Kwankwaso ya tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), amma bai yi nasara ba.

A yanzu da ake tunkarar babban zaɓen 2027, Kwankwaso ne mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC Peter Obi.

Rochas Okorocha

Rochas Okorocha na daga cikin ƴan siyasar Najeriya da suka sha neman muƙamin zaɓe kafin su kai ga cimma wasu daga cikin burinsu na siyasa.

Kafin ya zama gwamnan jihar Imo, Okorocha ya nemi kujerar gwamna sau da dama. Ya tsaya takarar gwamnan jihar a shekarar 1999 a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, sannan ya sake neman tikitin jam'iyyar a shekarar 2007 amma bai samu nasara ba.

Daga bisani ya kafa jam'iyyar APGA a Imo tare da tsayawa takarar gwamna a ƙarƙashinta, inda ya yi nasarar lashe zaɓen shekarar 2011. Daga baya kuma an sake zaɓensa a wa'adi na biyu a shekarar 2015.

Bayan kammala wa'adinsa na gwamna, Okorocha ya zama sanata mai wakiltar Imo ta Yamma a Majalisar Dattawa.

A shekarar 2022, ya shiga sahun masu neman tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC gabanin zaɓen 2023, amma bai samu tikitin takarar ba.

A zaɓen shekarar 2027, Rochas Okorocha na ci gaba da kasancewa cikin fitattun ƴan siyasar da suka nemi manyan muƙaman zaɓe a Najeriya a lokuta daban-daban.