Atletico na harin Martin Zubimendi, Leeds na son Dominic Calvert-Lewin

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan Arsenal Martin Zubimendi, na iya komawa Atletico Madrid, a watan Janairu, idan aka fara musayar ƴan wasa. (Sport - in Spanish)

Makomar Viktor Gyokeres da Mikel Merino a Arsenal na iya shiga rashin tabbas sakamakon yadda Arsenal ɗin ke duba aljihunsu. (AS - in Spanish)

Sai dai Gunners ɗin na samun ci gaba a yunƙurinsu na cimma sabuwar kwantaragi da Martin Odegaard, sai ɗan wasan Netherlands Jurrien Timber, sannan Declan Rice, inda ake sa ran kammala tattunawar kafin watan Janairu. (Teamtalk)

Leeds United na duba yiwuwar ƙara ruɓanya tattaunwarsu kan Dominic Calvert -Lewin don tsawaita kwantaraginsa zuwa 2030. (Teamtalk)

Ian Maatsen, na dab da tsawaita kwantaragin zamansa a Aston Villa. (Football Insider)

Everton na cikin ƙungiyoyin da ke Turai da ke son ɗaukar Samuel Lino. (4-4-2)

Manchester United da Liverpool na harin ɗan wasan Juventus Andrea Cambiaso. (TuttoJuve)

Barcelona na zawarcin ɗan wasan Bayern Munich Jonathan Tah, sai dai Bayern Munich ɗin ba ta da shirin siyar da ɗan wasan, inda shi ma ɗan wasan ba shi da shirin barin ƙungiyarshi ma. (Sky Sports Germany)

Mai tsaron ragar Bayern Munich Manuel Neuer, zai iya yin ritaya a ƙarashn kakar wasanin nan, inda Bayern Munich ɗin ke duba yiwuwar ɗauko ɗan wasan Schalke 04 Lorius Karius, da na Fulham Bernd Leno, a matsayin waɗan da za su taimakawa Jonas Urbig. (Sky Sports Germany)

Napoli na shirye-shiryen ganin sun siyo Gustavo Varela, da ke taka leda a Monza, inda ya ke ci gaba da ɗaukar hankulan ƙungiyoyo masu yawa. (Gazzetta dello Sport - in Italian)