Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴan Najeriya 5 da suka samu kujeru a majalisar dokokin Amurka
An gudanar da zaɓen Majalisar Dokokin Amurka ranar Talata, 3 ga watan Nuwamba, 2026, domin zaɓen mambobin majalisar biyu, wato Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai.
Sakamakon zaɓen ya nuna cewa jam'iyyar Democrat ta samu kujeru fiye da jam'iyyar Republican, wadda Shugaba Donald Trump yake wakilta.
A yayin zaɓen, an samu wasu abubuwa da ba a yi tsammani ba, ciki har da nasarar 'yan Najeriya da sauran Baƙaƙen fata da suka samu kujeru a majalisun dokokin Amurka.
Fiye da 'yan takara goma sha biyu ’yan asalin Najeriya sun samu nasarar lashe kujerun wakiltar mazabu daban-daban a Amurka, ciki har da waɗanda ke jihohin Maryland, Texas, Pennsylvania da Georgia, da kuma birnin Washington DC.
Wasu daga cikin waɗannan 'yan takara sun haɗa da Will Jawando da Junior Ezeonu da Oye Owolewa da Carol Kazeem da Segun Adeyina, Dukkaninsu sun tsaya takara ne a ƙarƙashin jam'iyyar Democrat:
Will Jawando -Montgomery County, Maryland
Will Jawando ya samu nasarar lashe zaɓen shugabancin gundumar Montgomery da ke jihar Maryland, bayan ya kayar da Esther Wells ta jam'iyyar Republican.
Ofishin babban jami’in tsaro na gundumar Montgomery ya naɗa Jawando a matsayin sabon shugaban rundunar 'yan sandan yankin.
Jawando mamba ne a Majalisar Gundumar Montgomery. Dan asalin Najeriya ne, kasancewar mahaifinsa ɗan Najeriya ne, yayin da mahaifiyarsa Ba'amurkiya ce.
Junior Ezeonu - Texas
A jihar Texas, Junior Ezeonu mai shekaru 27 ya samu nasarar lashe zaɓen kujerar wakilcin mazaɓa ta 101 a Majalisar Wakilan Jihar, bayan ya kayar da ɗan majalisar mai ci, Chris Turner, a zaɓen fitar da gwani.
An haifi Ezeonu a Onitsha, jihar Anambra ta Najeriya, amma ya koma jihar Texas da ke Amurka yana ɗan shekara biyu.
A shekarar 2021, an zaɓe shi a matsayin mamba a Majalisar Ƙaramar Hukumar Grand Prairie. Daga baya kuma ya zama mutum mafi ƙarancin shekaru da ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin magajin garin na wucin gadi a tarihin birnin.
Carol Kazeem - Pennsylvania
Carol Kazeem, 'yar jam'iyyar Democrat, ta sake lashe zaɓen kujerar wakilcin mazaɓa ta 159 a Majalisar Wakilan Jihar Pennsylvania.
Kazeem na daga cikin 'yan siyasa baƙaƙen fata na farko da suka samu nasarar lashe kujerun majalisa a Amurka a zaɓen shekarar 2022.
Oye Owolewa - DC
A birnin Washington DC, Oye Owolewa ya samu nasarar lashe ɗaya daga cikin kujerun wakilci na bai ɗaya a Majalisar Gundumar Columbia.
Owolewa, wanda masani ne a fannin harhaɗa magunguna, iyayensa sun fito daga jihohin Kwara da Osun ne na Najeriya, waɗanda suka yi hijira zuwa Amurka.
A baya, ya riƙe muƙamin wakilin je-ka na-yi-ka Gundumar Columbia (Shadow Representative).
Kundin tsarin mulkin Amurka ya tanadi cewa Gundumar Columbia za ta kasance jiha mai cin gashin kanta. Sai dai har yanzu ba ta da cikakken ikon kaɗa ƙuri'a a Majalisar Wakilan Amurka.
Segun Adeyina - District 110
Adeyina, wanda aka haifa a Najeriya kuma mamba ne a jam'iyyar Democrat, ya sake lashe zaɓe domin komawa Majalisar Dokokin Jihar Georgia.
An fara zaɓen Adeyina zuwa Majalisar Wakilan Jihar Georgia ne a shekarar 2022, inda yake wakiltar wasu sassan gundumar Gwinnett.
Shi ne babban daraktan kwamitin ba da shawarwari ga al'ummar Najeriya mazauna Amurka (Nigerian American Public Advisory Committee), wata ƙungiya da ke wayar da kan jama'a kan muhimmancin zaɓe, tare da taimaka wa baƙin haure da ke zaune a Amurka wajen yin rajistar zaɓe.
Shi ma Gabe Okoye na jam'iyyar Democrat ya sake lashe zaɓe, inda zai koma Majalisar Dokokin Jihar Georgia domin ci gaba da wakiltar mazaɓa ta 102.