Hanyoyi biyar da za a gane yara sun fara mu'amala da masu tsattsauran ra'ayi

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Ana ci gaba da tattaunawa kan hanyoyin da ake bi wajen jan hankalin matasa su fara sha'awar shiga ƙungiyoyin masu tsaurin ra'ayi, inda masana ke ganin yanar gizo na taka muhimmiyar rawa.

A duniya, cigaban fasahar zamani ya zo da wani sabon sauyi, inda fasahar zamani ta zama ɓangare na rayuwar yau da kullum ga miliyoyin matasa, duk da cewa akwai masu amfani da ita a ɓangarorin da suka dace, wasu kuma fakewa suke yi da kafofin wajen ayyukan da ba su dace ba.

Masana na cewa masu tsauraran ra'ayi yanzu ba sa buƙatar tarurruka ko ganawa ta kai-tsaye kawai kamar yadda aka saba a baya wajen jan hankalin matasa, inda yanzu suke iya shiga cikin rayuwar matasa ta hanyar amfani da kafofin sadarwa.

Masana sun ce matasa na cikin rukunin da suka fi kasancewa cikin haɗarin fadawa irin wannan tarko, musamman idan suna fama da kaɗaici da rashin kulawa daga iyaye, ko kuma neman amsoshin wasu tambayoyi game da rayuwa, addini ko zamantakewa.

Shugaban kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Afirka, Kabiru Adamu, ya ce akwai wasu alamomi da iyaye za su iya lura da su domin gane ko yaransu na kusa da faɗawa cikin tasirin ƙungiyoyin masu tsauraran ra'ayi.

Sa ido kan harkokin yara

Kabiru Adamu ya ce mataki na farko shi ne tabbatar da cewa yara, musamman waɗanda ba su balaga sosai ba, suna ƙarƙashin kulawar iyaye matuƙa, musamman harkokinsu na yau da kullum.

"Kafin yara su balaga, misali kafin su kai shekara 16, bai kamata a sake su suna shiga duk inda suke so ba. Iyaye ya kamata su san inda yaransu ke zuwa da kuma waɗanda suke hulɗa da su."

Ya ce hakan ba yana nufin tauye wa yara ƴanci ba ne, sai dai kariya daga haɗurran da za su iya fuskanta.

A cewarsa, idan iyaye ba su san wuraren da yaransu ke yawan zuwa ko mutanen da suke hulɗa da su, hakan na iya ba wasu masu mugun nufi damar kusantar su cikin sauƙi.

A san abin da yara ke yi a yanar gizo

A cewar Kabiru Adamu, mafi yawan sadarwar da matasa ke yi yanzu tana faruwa ne ta wayoyin hannu da yanar gizo.

"Yaro yawanci yana kan waya, musamman a yanar gizo. Don haka yana da muhimmanci iyaye su san irin wuraren da yake shiga da kuma mutanen da yake tattaunawa da su."

Ya ce iyaye su riƙa nuna sha'awa ga irin manhajojin da yaransu ke amfani da su da kuma irin abubuwan da suke kallo ko karantawa a kullum.

Masanin ya bayyana cewa yawancin masu ɗaukar sabbin mambobi zuwa ƙungiyoyin masu tsauraran ra'ayi suna anfani da kafafen sada zumunta da zaurukan tattaunawa wajen kusantar matasa.

A kula da shafukan da yaro ke yawan shiga

Wata muhimmiyar alama da Kabiru Adamu ya ce ya kamata ta ja hankalin iyaye ita ce idan yaro ya fara nuna tsananin sha'awa ga wani shafi ko wani mutum a yanar gizo.

"Idan yaro ya fara bin wasu shafuka na musamman ko wani mutum a yanar gizo, har ya fara yawan ambatonsa ko kare ra'ayinsa, ya kamata a bincika a san ko wane ne ko kuma wane shafi ne," in ji shi.

Ya ce akwai buƙatar iyaye su fahimci cewa ba duk wanda ke bayyana kansa a yanar gizo ba ne haƙiƙanin mutumin da yake ikirari.

"Wasu lokutan mugayen mutane suna amfani da sunayen bogi da wasu bayanai na ƙarya domin su ja hankalin mutane."

Fahimtar dabarun masu tsauraran ra'ayi

Kabiru Adamu ya ce ɗaya daga cikin dabarun da masu tsauraran ra'ayi ke amfani da su ita ce ɓoye manufarsu ta haƙiƙa.

A cewarsa, mutum na iya fara tattaunawa da matashi kan batutuwa na yau da kullum, amma daga baya ya fara nuna masa wasu akidu ko tunanin da ka iya kai shi ga tsattsauran ra'ayi.

"Saboda haka idan iyaye suka lura akwai wani mutum ko wata ƙungiya da ke da tasiri sosai a kan yaro, ya kamata su yi bincike su san ko su wane ne da kuma abin da suke yaɗawa."

Ya ce gano irin waɗannan alamomi da wuri kan taimaka wajen dakile matsala kafin ta tsananta.

Iyaye su samu ilimin yanar gizo

Kabiru Adamu ya ce kariyar yara a zamanin yau ba za ta yiwu ba idan iyaye ba su fahimci yadda fasahar zamani ke aiki ba.

"Wani abu shi ne iyaye su zama suna da ilimin yanar gizo."

Ya ce iyaye ba lallai sai sun zama ƙwararru a fasahar zamani ba, amma yana da muhimmanci su fahimci yadda kafafen sada zumunta, manhajojin aika saƙo da sauran dandalin sadarwa ke aiki.

"Idan iyayen ba su fahimci duniyar da yaransu ke rayuwa a ciki ba, zai yi wuya su gane lokacin da wani ke ƙoƙarin rinjayar su."

Me ya kamaci iyaye?

Kabiru Adamu ya yi gargaɗin cewa da zarar iyaye sun gano yaro na mu'amala da masu tsauraran ra'ayi, kada su ɗauki mataki cikin fushi ko amfani da ƙarfi kawai wajen sauya tunaninsu.

"Muhimmi shi ne a ƙarfafa yaro, a ilimantar da shi, a nuna masa illolin abin da yake yi da kuma haɗarin da zai iya biyo baya."

Ya ce manufar farko ita ce a sa yaron ya fahimci matsalar da kansa maimakon a tsoratar da shi.

"Iyaye suna da damar horo da ladabtar da yaro idan ya kauce, amma ya kamata a yi hakan cikin hikima da tausayi."

Shagaltar da yara a intanet

A cewar masanin tsaron, bincike ya nuna cewa tsaurin hukunci ko amfani da ƙarfi kaɗai kan haifar da akasin sakamakon da ake nema.

"Amfani da ƙarfi bincike ya nuna ba ya aiki. Idan aka matsa masa sosai, zai fara aikata abubuwan ne a ɓoye, sannan ya ci gaba da hulɗa da mutanen da ke tasiri a kansa ba tare da iyayensa sun sani ba."

Ya ce mafi dacewa shi ne tattaunawa, gina amana da kuma sa yaro ya ji cewa iyayensa na son taimaka masa ba wai azabtar da shi ba.

Kabiru Adamu ya ce ɗaya daga cikin hanyoyin da suka fi tasiri wajen janye matashi daga irin waɗannan mutae shi ne samar masa da wasu abubuwan da za su shagaltar da shi cikin amfani.

"A yi anfani da wasu hanyoyi da za su maye gurbin abubuwan da yake yi, musamman a fannin fasaha da za su ɗauke hankalinsa."

Ya ƙara da cewa: "Yana da muhimmanci a samar wa matashi damar koyon sana'a ko wata fasaha da zai iya anfani da ita wajen samun kuɗin halal."

A cewarsa, idan matashi yana ganin yana da makoma, yana samun kulawa daga iyaye kuma yana da abin yi mai amfani, zai fi wuya ya faɗa tarkon masu tsauraran ra'ayi.