Liverpool na zawarcin Verbruggen, Bayern Munich na harin Ngumoha

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Liverpool na duba yiwuwar ɗauko mai tsaron ragar Brighton Bart Verbruggen, sakamakon rashin tabbasa kan makomar takwaransa na Brazil Alisson Becker, da kwantaraginsa za ta ƙare a kakar wasanni mai zuwa. (Football Insider)

Bayern Munich na ci gaba da tattaunawa da Rio Ngumoha, bayan ganawar farko da ɗan wasan na Liverpool inda suke fatan komawarsa ƙungiyar a kakar musayar ƴan wasa mai zuwa. (Christian Falk)

Liverpool na tsananin son ɗauko ɗan wasan Brighton Luka Vuskovic, yayin da suke neman wanda zai gaji Virgil van Dijk. (Daily Briefing)

Chelsea da Liverpool na harin ɗan wasan Brentford da Senegal El Hadji Malick Diouf. (4-4-2.ch - in German)

Crystal Palace, da Everton da Leeds United na sa ido kan ɗan wasan Tottenham Conor Gallagher, duk da cewar akwai yiwuwar Spurs ba lallai ta bar dan wasan ya tafi ba. (Football Insider)

Chelsea na iya shiga tattaunwa da ɗan wasan Ingila Levi Colwill, da kwantaraginsa za ta ƙare a 2029, yayin da Barcelona ke duba yiwuwar siyar da ɗan wasan a watan Janairun idan an buɗe kakar siyar da ƴan wasa. (Caught Offside)

Manchester United na zawarcin ɗan wasan Rennes Mahamadou Nagida, sakamakon neman zaƙaƙuran ƴan wasa da suke yi don ingnata ƙungiyar. (Teamtalk)

Al-Hilal sun yi wa ɗan wasan Liverpool Jeremie Frimpong tayin komawa ƙungiyar watanni 18 bayan da ɗan wasan ya bar Bayer Leverkusen zuwa Liverpool ɗin kan fam miliyan 29.5. (Winwin via Goal)