Yadda za ku yi amfani da wayarku wajen neman rancen kuɗi daga Gwamnatin Najeriya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani shiri da zai bai wa 'yan Najeriya damar tara kuɗi domin sayen muhimman kayayyaki kamar abinci da biyan wutar lantarki da sauran ƙananan buƙatu ta hanyar wayoyinsu.

An fito da tsarin ne ƙarƙashin wani shiri mai suna Spark, wanda Hukumar Ba da Lamunin Kuɗi ga Masu Amfani ta Najeriya (Nigerian Consumer Credit Corporation), wadda aka fi sani da CrediCorp, ke gudanarwa, mutane za su iya samun rance ta amfani da lambobin USSD, ba tare da buƙatar wayar zamani ko sayen babban kunshin data ba.

A cewar hukumar, shirin zai bai wa mutanen da ba su taɓa karɓar rance a baya ba damar samun rance, lamarin da zai ba su damar fara amfani da tsarin lamuni a ƙasar.

Yadda ake samun rance ta shirin 'SPARK'

A cewar babban jami'in gudanarwa na kamfanin, Ngwu Nwagbala, a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin yanar gizon kamfanin mai alaƙa da shafinsa na X, shirin wata dama ce da za ta bai wa mutane damar tara ƙananan kuɗaɗen shigarsu domin biyan buƙatun iyalansu, kamar sayen abinci, samar da wutar lantarki ta hasken rana da sauran muhimman abubuwan buƙata.

Za su iya cin moriyar wannan shiri ta hanyar danna lambar *347*333# a wayoyinsu.

Ga matakai guda takwas da za ku bi domin cin gajiyar wannan damar samun rance.

1. Danna waɗannan lambobi: *5120# a wayarka domin yin rajista don samun tallafin.

2. Amince da sharuɗɗa da ƙa'idojin shirin.

3. Shigar da lambobi huɗu na ƙarshe na lambar BVN ɗinka.

4. Shigar da PIN mai lambobi huɗu da kake son amfani da shi wajen buɗewa ko kulle ayyuka ta hanyar USSD.

5. Zaɓi irin tallafin kuɗi da kake buƙata.

6. Karanta sharuɗɗa da ƙa'idojin shirin sannan ka amince da su.

7. Shiga ta amfani da bayanan asusun bankinka kamar yadda aka nuna a wayarka.

8. Za ka karɓi saƙo a wayarka, sannan a tura maka kuɗin rancen cikin mintuna biyu zuwa biyar.

Lura: Ka tabbatar da sahihancin waɗannan matakai ta hanyar CrediCorp kafin amfani da su. Kada ka shigar da BVN ko PIN ɗinka a wani shafin da ba ka tabbatar da sahihancinsa ba.

Su wa suka cancanci samun rancen kuɗin?

  • Dole ne mutum ya kasance ma'aikacin Gwamnatin Jiha ko ta Tarayya, ko kuma yana aiki a fannin koyarwa ko aikin soja.
  • Dole ne shekarunsa su kasance tsakanin 22 zuwa 58.
  • Ana buƙatar ya gabatar da takardar shaidar tabbatar da cewa ba shi da matsalar bashi daga Hukumar Kula da Tarihin Bashi ta Najeriya (Credit Bureau Nigeria).
  • Dole ne ya kasance yana da Lambar Tabbatar da Asusun Banki (BVN).
  • Dole ne ya kasance ya shafe aƙalla watanni uku yana aiki, kuma shekarunsa su kasance ƙasa da 34.
  • Dole ne kamfanin da yake aiki a cikinsa ya kasance cikin kamfanonin da Gwamnati ta amince da su domin shiga wannan shiri.
  • CrediCorp za ta tantance adadin kuɗin da kake kashewa wajen biyan buƙatunka na wata-wata.