Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An yanke wa Paul Mackenzie hukuncin shekara 200 saboda kashe mutum 191
Kotun Kenya ta yanke wa Fasto nan Paul Nthenge Mackenzie da ya janyo cece-kuce hukuncin ɗaurin shekara 200 a gidan yari saboda rawar da ya taka a kisan ƙiyashin Shakahola, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 191, ciki har da yara 190.
Babbar Kotun Mombasa ce ta yanke hukuncin a ranar Juma'a, matakin da ake kallon a matsayin wani muhimmin hukunci a shari'ar da ta shafi ɗaya daga cikin munanan misalan tsattsauran ra'ayin addini da aka taɓa gani a Kenya.
Mai shari'a Diana Kavedza ta samu Mackenzie da laifin tuhume-tuhume 191 na kisan kai da ke da alaƙa da mutuwar mutanen da aka samu a dajin Shakahola, da ke gundumar Kilifi, tsakanin Janairun 2021 da Satumban 2023.
Ana zargin Mackenzie, wanda shi ne ya kafa cocin Good News International Church, da shawo kan mabiyansa su bar gidajensu su koma dajin Shakahola, yana yi musu alƙawarin cewa killace yankin zai kusantar da su ga Allah tare da shirya su zuwa aljanna.
A cikin hukuncinta, Mai shari'a Kavedza ta ce an yi la'akari da girman laifuffukan da aka aikata, yanayin da ya kewaye mutuwar mutanen, da kuma irin tasirin da lamarin ya yi ga waɗanda suka tsira, iyalan waɗanda suka mutu da ma al'umma baki ɗaya.
Kotun ta yanke wa Mackenzie hukuncin ɗaurin shekara 100 saboda kashe-kashen da aka aikata ta hanyar yunwa da gangan, sannan ta ƙara masa wani hukuncin shekara 100 saboda kashe yara kai tsaye.
An tsara hukuncin ta yadda jimillar zaman gidan yarinsa ta kai shekaru 200.
Masu gabatar da ƙara sun buƙaci kotun ta yanke masa hukuncin kisa saboda girman laifuffukan da aka aikata.
Sai dai Mai shari'a Kavedza ta yi watsi da buƙatar, tana mai cewa hukuncin kisa zai kawar da yiwuwar gyaruwar hali da sauyin ɗabi'a ga waɗanda suka aikata laifin.
Kotun ta gano cewa Mackenzie ne ke ɗauke da babban alhakin laifin, saboda ya umarci mabiyansa da su yi azumi har sai sun mutu.
Mai shari'ar ta ce hukuncin ya dace kuma yana isar da saƙo ƙarara cewa irin waɗannan munanan ayyuka sun cancanci mafi tsanani daga cikin hukuncin da doka ta amince da shi.
Bisa ga shaidun da aka gabatar a kotu, wasu daga cikin mabiya sun yi imanin cewa Mackenzie "mai magana da yawun Yesu" ne, yayin da waɗanda suka yi adawa da koyarwarsa aka riƙa duka har ma da kashe wasu daga cikinsu.
Kotun ta kuma ce an gallaza wa wasu yara ta hanyar cin zarafi na jiki domin tilasta musu bin umarnin azumi.
Sakamakon binciken gawa da aka gudanar bayan gano gawarwakin ya nuna cewa mafi yawan wadanda suka mutu yunwa ce ta kashe su, yayin da wasu suka mutu sakamakon shakewa, rataya, ko raunukan da suka samu a kai.
A wasu lokutan kuwa, ba a iya gano musabbabin mutuwar ba saboda lalacewar gawarwakin.
Yadda lamarin ya faru
Binciken 'yan sanda ya fara samun ƙarfi a shekarar 2023 bayan gano kaburbura masu yawa a dajin Shakahola da ke kusa da Malindi.
Wannan ganowar ta bayyana abin da aka bayyana matsayin daya daga cikin mafi munin kashe-kashen da ke da alaƙa da wata ƙungiyar addini a Kenya, lamarin da ya ja hankalin duniya.
Yawan gawarwakin da aka tono ya zarce 400, inda binciken ƙwararru kan gawarwakin ya nuna cewa mafi yawan waɗanda suka mutu sun mutu ne saboda yunwa bayan sun bi umarnin yin azumi.
Wasu kuma sun mutu sakamakon shakewa, rataya ko raunukan da suka samu a kai.
A wasu lokutan, ba a iya tantance musabbabin mutuwar ba saboda lalacewar gawarwakin.
Wasu kuma sun mutu jim kaɗan bayan an ceto su saboda tsananin rashin abinci mai gina jiki da kuma raunin jiki.
A cikin cikakken hukuncinta na tsawon sa'o'i takwas da ta yanke a watan da ya gabata, Mai shari'a Diana Mochache ta ce mabiyan Mackenzie sun yi imanin cewa shi mai magana da yawun Yesu ne kuma sun bi koyarwarsa.
Kotun ta gano cewa mutanen ba su mutu ne saboda sun yanke shawarar yin azumi da kansu ba, illa saboda wani tsari ne na koyarwar addini da umarni da ya tilasta wa mabiyan shiga wannan azumi mai hadari.
Mai shari'ar ta ce an doke wasu mutanen da suka yi adawa da koyarwar Mackenzie har suka mutu.
Daya daga cikin waɗanda ake tuhuma tare da shi ya ce Mackenzie ya gaya wa mabiyansa cewa duk wanda ya ki bin umarnin azumi ya kamata a tilasta masa zuwa aljanna ta hanyar dukansa da nausawa.
A cewar bayanin Mai shari'ar, an sanya wa jana'izar wadanda suka mutu a dajin suna na biki, inda ake murnar mutuwar wadanda suka rasu tamkar sun auri Yesu.