Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kotu ta soke takarar Atiku Abubakar na jam'iyyar ADC
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta rushe shugabancin ADC tsagin Sanata David Mark.
Yayin yanke hukuncin alƙalin kotun Mai shari'a Peter Lifu ya kuma soke duk matakan da ɓangaren na David Mark ya ɗauka a madadin jam'iyyar.
Waɗannan matakan sun haɗa da tsayar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar a babban zaɓen shekarar 2027.
Atiku, wanda hukumar zaɓen ƙasar INEC ta riga ta wallafa sunansa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, daga baya ya zaɓi tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, a matsayin abokin takararsa.
Sai dai a hukuncin da Mai shari'a Peter Lifu ya yanke a ranar Alhamis, kotun ta ce kwamitin riƙon ƙwarya na ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata Mark, wanda ya shirya zaɓen fidda gwani da ya haifar da Atiku a matsayin ɗan takara ADC, a matsayin haramtaccen kwamiti ne.
Hon Nafiu Bala Gombe ne dai ya shigar da ƙara a gaban kotun yana ƙalubalantar hanyar da David Marka ya zama shugaban riƙo na jam'iyyar.
Kotun ta ce ƙarar, Nafiu Bala Gombe na da tushe don haka ta yanke wannan hukunci.
Nafiu Gombe ya jaddada wa kotun cewa bayan murabus ɗin tsohon shugaban jam'iyyar na ƙasa, Cif Ralph Nwosu, shi (Gombe) ne mutum na gaba da dokar jam'iyyar ta tadani ya zama shugabanta.
Saboda haka, daga cikin buƙatun da ya gabatar wa kotun akwai soke duk wasu matakai da aka ɗauka a madadin jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Sanata Mark.
'Za mu ɗaukaka ƙara'
Tuni dai ɓangaren Sanata David Mark ya ce zai ɗaukaka ƙara game da hukuncin.
Hon Faisal Kabir ɗaya ne daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar tsagin David Mark ya kuma shaida wa BBC cewa babu abin da wannan hukuncin zai sauya.
''Ai a baya wata kotun tarayyar mai matsayi iri ɗaya da wannan ta yi hukuncin da ya tabbatar da ɓangarenmu, don haka wannan hukunci ba zai sauya komai ba'', in ji shi.
Faisal Kabir ya ce dama tun ba yau ba ake yi wa jam'iyyarsu bi-ta-ƙulli.
''A ranar 30 ga watan Maris na wanann shekarar Atiku ya je Kano ya karɓi Kwankwanso yana dawowa Abuja kotu ta soke rajistar jam'iyyarmu, to yanzu ba jiya mun ƙaddamar da gangamin yaƙin neman zaɓe, kuma yau kotu ta rushe shugabancin jam'iyyar'', in ji shi.
Ya ce za su tunkari kotun ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar matakin a gabanta.
''Dama muna da hukuncin da yi daidai da wannan, za mu je kotun ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin, kuma muna da yaƙinin za mu yi nasara a can'', in ji shi.
Yanzu za mu fara yaƙin neman zaɓe - Nafi'u Bala
A nasa ɓangare, Hon Nafi'u Bala Gombe, wanda ya shigar da ƙarar ya ce ya yi maraba da hukuncin, kuma dama haka yake tsammani.
A hirarsa da BBC, Nafiu Bala ya ce yau rana ce ta farin ciki da alfahari a gare shi da magoya bayansa.
''Yau Allah ya tabbatar da gaskiya, wanda kuma dama hakan muka jima muna fata'', in ji shi.
Ya ce yanzu abin da ya rage masa shi ne fara yaƙin neman zaɓe gadan-gadan.
''Yanzu abin da ya rage mana ƴantakarkarun da muka tsayar za su fara yaƙin neman zaɓe domin tunkarar zaɓe mai zuwa'', in ji shi.
Dangane da batun ɗaukaka ƙara, Nafi'u Bala ya ce babu abin da zai sauya game da hukuncin kotun na yau.
''Ai ita gaskiya, duk inda take gaskiya, duk inda za su je su je, ko majalisar Dinkin Duniya suka je ina mai tabbatar maka babu abin da zai sauya'', in ji shi.
Me ya janyo rikicin jagoranci a jam'iyyar ADC?
A ranar 2 ga watan Yuli ne dai tsohon shugaban jam'iyyar ADC, kuma wanda ya kafa ta, Ralph Nwosu, ya sanar da rushe jagorancin jam'iyyar domin bai wa sabbin ƴan hamayya da suka shiga jam'iyyar dama.
Hakan ne kuma ya bai wa tsohon shugaban majalisar dattawan ƙasar, Sanata David Mark damar kasancewa shugaban jam'iyyar haɗakar ta ADC.
To sai dai kasa da wata ɗaya da yin hakan sai Nafiu Bala, wanda shi ne tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar ya riƙa ayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyyar haɗakar a yanzu.
Nafi'u wanda ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a Abuja ya zarki David Marka da sauran ƴankwamitinsa da ƙwace ragamar jagorancin jam'iyyar da kuma yi wa kundin tsarin jam'iyyar karantsaye.
Nafi'u Bala ya kuma sha alwashin ƙalaubalantar al'amarin da ya bayyana da "juyin mulkin siyasa ido biyu daga baƙi" a gaban kotu.
Tun daga wannan lokacin ne dai ɓangarorin biyu ke ta zariyar kotu daban-daban, kan mabambantan shari'o'in da suka shafi iko da jam'iyyar.