Ronaldo ya yi ritaya daga buga wa Portugal wasa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ɗan wasan Portugal Cristiano Ronaldo ya sanar da yin ritaya daga buga wa ƙasarsa wasa.

Ronaldo mai shekara 41 a duniya ya ci wa ƙasarsa ƙwallo 146 kuma ya buga wa ƙasar wasa sau 234 - tun bayan fara buga wa ƙasar wasa a shekarar 2003.

Ɗan wasan ya fice daga sansanin atisayen Portugal a watan da ya gabata bayan da aka faɗa masa cewa ba za a fara wasa da shi ba a karawar da ƙasar za ta yi da Denmark a gasar Nations League.

"Ya ku al'ummar Portugal, rana ta zo da zan mayar da riga mai lamba 7 ga tawagar ƙasarmu," in ji Ronaldo a wani bayani da ya yi na bidiyo da ya wallafa a shafin Instagram.

"Ban taɓa tunanin cewa (lambar) mallakina ce, ni kaɗai ba, amma na samu karramawar amfani da ita tsawon shekara 23, inda na riƙa amfani da ita a filayen wasanni na faɗin duniya.

"Yau rana ce da zan miƙa ta ga masu tahowa. Wannan mataki bai zo min cikin sauƙi ba, domin wasu matakan da mutum ke ɗauka ba da tunanin kawai ake yi ba, ana yi ne daga cikin zuciya.

"Wannan tafiya da ta faro daga watan Agustan 2003, wadda ta sauya rayuwata, ta zo ƙarshe."

A ranar Juma'a ake sa ran Portugal za ta sanar da tawagarta da za ta buga wasannin gasar Nations League na watan Nuwamba – inda za ta kara da Denmark a gida sannan kuma ta ziyarci Wales.

Sai dai a wani saƙo da ta fitar, hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Portugal ta ce ba za ta bari "wannan tafiya ta wakana ba tare da girmamawar da ta dace ba".

Sanarwar ta ce: "Muna da matuƙar aniyar tsarawa da shiryawa da halarta da kuma haɗa hannu wajen girmama gudumawar Cristiano Ronaldo, ta yadda masoya da ƙasa za su yaba da karrama ɗan wasan da ya bayar da gagarumar gudumawa."

A watan Oktoban da ya gabata ne abokin gogayyar Ronaldo, wato Lionel Messi ya yi ritaya daga buga wa ƙasarsa Argentina wasa, inda aka yi masa karramawa ta girmamawa.