Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abu huɗu da za a iya binciken Trump a kai bayan rasa rinjaye a Majalisa
- Marubuci, Debosman Jr. brand
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, White House Correspondent
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Jam'iyyar Democrat a Amurka ta karɓe rinjaye a majalisar dattijai da ta wakilai bayan zaɓen tsakiyar zango.
Wannan rinjaye da jam'iyyar ta samu zai ba ta ƙarfin tursasa yin wasu abubuwa da kuma ta fannin kuɗaɗe.
Ƴan jam'iyyar Democrat na da ƙudurin ganin sun binciki wasu daga cikin jami'an gwamnatin Trump har ma da shi kansa.
Wasu da ke da masaniya kan wannan lamari sun ce an fara tattara bayanai domin gudanar da bincike, kuma ana duba wadanda za a iya gayyata gaban zauren majalisa domin bayar da bahasi.
Ga wasu daga cikin abubuwan da ƴan Democrat za su so cimmawa bayan samun rinjaye a majalisar dokokin ta Amurka.
Iyalan Trump da hada-hadar kuɗi
Ƴan Democrat sun bayyana ƙarara cewa idan suka samu dama za su binciki manyan ayyuka masu alaƙa da kasuwancin iyalan Trump.
"Za mu tababatr cewa ana kashe kuɗin al'umma yadda ya kamata ba wai a riƙa sacewa ko karkatarwa zuwa ga wasu mutane ta hanyar da ba ta dace ba," in ji Suhas Subramanyam, ɗan majalisar wakilai na jam'iyyar Democrat daga Virginia, kamar yadda ya shaida wa BBC.
Daga cikin abubuwan da za a bincika akwai alaƙar gwamnati da kamfanonin ƴan kasuwa, musamman waɗanda ke harkar kirifto, da kuma hada-hadar kasuwancin ƙasa da ƙasa na Jared Kushner, surukin shugaban ƙasar.
Akwai kuma wasu abubuwan bayan waɗannan, kamar batun jirgin saman alfarma wanda kuɗinsa ya kai dala miliyan 400, wanda masarautar Qatar ta bai wa Trump kuma ake amfani da shi a matsayin jirgin shugaban ƙasa (Air Force 1).
Sai kuma kwangilolin harkar tsaro da aka bai wa wasu kamfanoni masu alaƙa da iyalan Donald Trump.
"Anib da ke ba ni matuƙar mamaki shi ne, ba gwamnatin kaɗai ba, hatta jami'anta da shi shugaban ƙasar da kansa da kuma iyalansa sun tsunduma cikin harkar rashawa da son rai, kuma suna yin hakan ne da gadara, in ji Subramanyam.
Fadar White House ta sha musanta zargin tafka rashawa ko ayyukan da suka saɓa wa doka.
Hegsett da ma'aikatar tsaro
’Yan majalisa na jam’iyyar Democrat sun sha alwashin binciken sakataren tsaro Pete Hegseth kan yadda ya tafiyar da yakin Iran wanda aka fara a watan Fabarairu, daga cikin abin da za su bincika har da yawan mutane fararen hula da yakin ya rutsa da su, karancin makamai, kudin da aka kashe da kuma zargin rashin kyakkyawan shiri.
Wasu karin abubuwan da za a iya yin bincike a kai kamar tadda majiya ta tabbatar sun hada da kai hare-hare kan jiragen ruwa a yankin Karebiya, wadanda gwamnatin ta ce ta kai ne domin dakile ayyukan masu safarar kwaya da ke son shiga Amurak.
A watan Afrilu wani gungun ‘yan jam’iyyar Democrat a majalisar wakilai ya yi wani gagarumin yunƙuri na ƙaddamar da shirin korar Hegseth, bayan zargin shi da aikata "manyan laifuka" game da yaƙin Iran.
Tsigewa na buƙatar samun rinjaye ne kawai a majalisar wakilai, to amma samun mutum da laifi da kuma cire mutum daga muƙami na buƙatar samun amincewar kashi biyu cikin uku na ƴan majalisar dattijai.
Ba a taɓa cire wani mai riƙe da muƙamin siyasa ta irin wannan hanya ba.
Wasu masana na ganin cewa sukar da Hegseth ke sha daga majalisar dokoki za ta iya kai shi ga fuskantar kora ko kuma ya ajiye muƙamin.
"Idan har abin yana shafar mutuncin gwamnati da janyo suka daga kafafen yada labarai, akwai yiwuwar Trump ya cire mutumin daga muƙami domin ba zai so a ci gaba da ɓata sunan gwamnatinsa ba," in ji David Miller, farfesan kimiyyar siyasa kuma masani kan harkokin fadar shugaban ƙasa a jami'ar American University da ke birnin Washington.
"Wannan zai iya zama wata nasara ga ƴan Democrat," in ji shi.
Wani tsohon jami'in fadar White House a lokacin mulkin shugaban George W. Bush, Ricahrd Painter, ya shaida wa BBC cewa ya kamata kuma a sake duba batun yain Iran.
"Abu mafi muhimmanci shi ne ba majalisar dokoki ce ta amince a ƙaddamar da wannan yaƙi ba, ba batu ne na wane ne ke riƙe da muƙamin sakatare tsaro ba," in ji shi.
Painter ya ce "kundin tsarin mulkin Amurka ya ce majalisa ce take yanke shawarar zuwa yaƙi", kuma ya kamata majalisar ta "gayyato waɗannan mutane" domin su bayar da bahasi.
A wata sanarwa, mai magana da yawun ma'aikatar tsaro Kingsley Wilson ya kare ayyukan Hegseth, inda ya bayyana shi a matsayin jagora mai kawo sauyi wanda ya rage dogoyen matakai da ake bi wajen aikin soji.
"Idan aka yi duba na tsanaki, ma'aikatar tsaro a ƙarƙashin sakatare Pete Hegseth ta yi aiki fiye da lokutan baya," in ji shi.
Kamen baƙi
Manyan ƴan jam'iyyar Democrat, ciki har da ɗan jihar California, Robert Garcia wanda zai iya samun muƙamin shugabantar kwamiti a majalisar dokokin Amurka bayan rinjayen da jam'iyyar ta samu, sun bayyana batun baƙi a matsayin daya daga cikin abubuwa masu muhimmanci da ya kamata majalisa ta yi bincike a kai.
Binciken zai iya duba zarge-zargen aikata ba daidai ba da ake yi wa jami'an hukumar ICE lokacin da suka riƙa kai samame a faɗin ƙasar.
Sai dai wannan binicke zai iya zama mai wahala ko kuma mai sarƙaƙiya na siyasa.
Trump ya shiga takarar zaɓen 2024 ne tare da alƙawarin korar baƙi, wani abu da magoya bayansa suka yi maraba da shi.
Sai dai ƙuri'ar jin ra'ayi a baya-bayan har a tsakanin wadanda suka zaɓi Trump a baya, ta nuna cewa Amurkawa da yawa ba su jin daɗin tsarin da jami'an kwastams na ƙasar suka bi wajen kai samame a birane da dama na ƙasar a farkon wannan shekara.
Tsige Trump karo na uku
Akwai rarrabuwar kawuna tsakanin ƴan jam'iyyar Democrat kan yunƙurin tsige Shugaba Trump a karo na uku.
Wasu daga cikin su, kamar Alexandria Ocasio-Cortez sun goyi bayan batun, suna kafa hujja da akbin da suka bayyana haramtaccen yaƙin da ake yi da Iran da kuma wasu abubuwa da za a iya kafa hujja da su domin tsige shi.
A ɗaya ɓangaren kuma wasu na ganin cewa ya kamata a yi taka-tsantsan, inda suka ce ba lallai ne wannan haƙa ta cimma ruwa ba musamman game da batun cire Trump daga mulki.
Haka nan babu tabbas kan ko ƴan jam'iyyar ta Democrats za su samu wata hujja ɗaya da za su riƙe wajen yunƙurin cire Trump.
"Zan iya duk abin da na ga dama," kamar yadda Trump ya shaida wa ƴan jarida a ofishinsa da ke fadar White House a cikin watan Oktoba. Ya bayyana yunƙurin tsige shi da aka yi a wa'adinsa na farko da kuma kai shi kotu a matsayin abubuwa da suka "saɓa wa doka".
Babu tabbas kan yunƙurin ƴan jam'iyyar Democrats a game da tsige Trump zai kai ga ɗaukar wani ƙwaƙƙwaran mataki a kansa.
Sai dai Suhas Subramaniyam na ganin cewa ɗaukar wannan mataki zai isar da wani muhimmin saƙo.
"Idan muka ƙi daukar mataki saboda gudun abin da mutane za su ce, ko saboda muna ganin ba za mu yi nasara ba, ko saboda ɗayan ɓangaren zai yi katsalanda, hakan zai zama kuskure," in ji shi.