Su wane ne mutanen da za su jagoranci yaƙin neman zaɓen Tinubu, Atiku da Obi?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Yayin da aka kaɗa gangamin siyasa a Najeriya gabanin babban zaɓen Najeriya na 2027, jam'iyyun siyasa daban-daban sun duƙufa wajen samun goyon bayan jama'a.

Jam'iyyun sun fito da salo iri-iri na jan ra'ayin mutane domin ganin sun samu nasara a zaɓen da ke tafe.

Cikin irin dabarun da jam'iyyun ke fito da su har da naɗa manyan jiga-jiga don jagorantar yaƙin neman zaɓensu.

Manyan jam'iyyun ƙasar da suka haɗa da APC, ADC, NDC da sauransu sun naɗa fitattun mutane masu faɗa a ji don jan ragamar kamfen ɗin su a faɗin jihohi.

Dangane da haka, mun yi duba kan darektocin yaƙin neman zaɓen APC da ADC da NDC da kuma....

APC - Abdulaziz Yari

Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, ya zaɓi Abdulaziz Yari a matsayin darakta-janar domin ya jagoranci kamfen ɗin jam'iyyar a karshen watan Agusta.

Jam'iyyar ta zaɓi tsohon gwamna na jihar Zamfara saboda irin ƙwarewar da yake da shi a fagen siyasa.

Sanata Abdul'aziz Yari jigo ne kuma fitaccen ɗan siyasa a Najeriya, wanda a halin yanzu yake matsayin Sanata mai wakiltar shiyyar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawan Najeriya.

Ya yi gwamnan jihar Zamfara na tsawon wa'adi biyu, daga 2011 zuwa 2019, kuma ya kasance tsohon shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF).

Masana siyasa sun yi ittifakin cewa Yari yana da tasirin gaske da zai iya kawowa jam'iyyar kuri'u a zaɓe mai zuwa.

Ana yi wa Yari kallo a matsayin wanda ke yawan tallafa wa marasa ƙarfi a jiharsa, musamman a lokutan ibada da azumi, abin da ya ƙara masa zama mai tasiri.

An haife shi a 1968 a ƙaramar hukumar Talata Mafara da ke Jihar Zamfara.

Ya fara shiga harkokin siyasa ne gadan-gadan tun farkon Jamhuriya ta Huɗu a shekarar 1999.

Ya yi aiki a matsayin Sakataren jam'iyyar ANPP na Jihar Zamfara, sannan daga baya ya zama Shugaban Jam'iyyar ANPP na Jiha.

ADC - Sanata Austin Akobundu

Jam'iyyar ADC ta ɗora wa Austin Akobundu alhakin jan ragamar yaƙin neman zaɓen jam'iyyar, inda ta ce tana buƙatar ƙwarewarsa da kuma jajircewa na siyasa wajen kai jam'iyyar ga gashi.

Akobundu, wanda ke wakiltar mazaɓar Abia ta tsakiya a majalisar dattawa, ya karɓi matsayin ne da nufin tattara basirarsa wuri ɗaya na ganin nasarar jam'iyyar.

An haife shi ranar 10 ga watan Maris ɗin 1956, kuma ya kasance tsohon kanal na soja. Ya samu zuwa majalisar dattawa a 2023, bayan da kotu ta soke zaɓen wanda yake kan kujerar.

Ya taɓa zama karamin ministan tsaro a lokacin mulkin tsohon shugaba Goodluck Jonathan da kuma wasu mukamai daban-daban a cikin jam'iyyar PDP, sai dai ya yi murabus daga jam'iyyar zuwa ADC a Maris 2026.

Daga bisani ya nuna goyon bayansa ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, inda ya ce idan Atiku ya samu nasara zai tafi da kowa a cikin ƙasar ba tare da bambanci ba.

Ya kuma samu tikitin sake tsayawa takarar na sanata a 2027 a ADC.

Tarihinsa na zama soja da gogewarsa a harkokin tsari da gudanarwa a cikin jam'iyyar PDP, da kuma kasancewarsa ɗan Kudu maso Gabas tare da nuna cikakkiyar biyayya ga Atiku, sun sa ya zama ɗaya daga cikin mutanen da za su iya jan hankali wajen samar da daidaito tsakanin yankuna a cikin jam'iyyar da ke neman haɗin gwiwar siyasa.

NDC - Ibrahim Abdulkarim

Ita kuwa jam'iyyar NDC, ta amince da Ibrahim Abdulkarim wanda aka fi sani da Ibrahim Ziter, don ya jagoranci yaƙin neman zaɓen jam'iyyar.

Ya kasance ƙwararre kan ɓangaren sadarwar zamani wato ICT, ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa wanda aikinsa ya shafi bunƙasa fasaha,wayar da kan masu zaɓe, kirkire-kirkire da kuma ci gaban al'umma.

An haife Ibrahim Abdulkarim ranar 14 ga Oktoban 1976 a birnin Sakkwato.

A ɓangaren siyasa, Abdulkarim ya riƙe muƙamai daban-daban na gudanarwa da na bayar da shawara. Ya taɓa riƙe matsayin mai ba da shawara ga ƙungiyar Buhari Support Organisation (BSO), inda ya taka rawa wajen tsarawa da ƙirƙirar katin bayar da gudummawa ga takarar Buhari a 2015.

Ya kuma taimaka wajen daidaita rajistar masu bayar da gudummawa, ƙungiyoyin siyasa da kuma tsarin yaƙin neman zaɓe.

A baya-bayan nan, ya riƙe matsayin Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa na Obi-Datti mai Zaman Kansa. Haka kuma an naɗa shi a matsayin sakatare na Kwamitin Ba da Shawara na Obi-Datti na bayan Zaɓe.

Waɗannan matsayi da suka sun ba shi ƙwarewar da ta kamata, abin da ya sa ita jam'iyyar NDC ta ce ta ga dacewar naɗa shi darakta-janar na yaƙin neman zaɓenta.

AAC - Abdullahi Usman

A ɗayan gefe, jam'iyyar African Action Congress, ta ce Abdullahi Usman ne zai jagoranci kwamitin yaƙin neman zaɓenta a matsayin darekta-janar.

An ɗora masa alhakin janyo ra'ayin jama'a wajen sun mara wa jam'iyyar a zaɓen 2027.

Usman yana da ƙwarewa a fannoni daban-daban na siyasa, inda ake ganin ƙwarewar za ta taimaka wa jam'iyyar wajen samun nasara.

Ana sa ran zai yi amfani da dabarunsa na fasaha da tsarin aiki da wayar da kan al'umma a matakin ƙananan hukumomi domin tabbatar da cewa yaƙin neman zaɓen Sowore–Magashi ya isa ga 'yan Najeriya a kowane yanki na ƙasar.

Jam'iyyar dai ta ce tana son kamfe ɗin ta ya karaɗe manyan birane da kuma jihohin Najeriya har zuwa yankunan ƙarkara domin tallata manufofinta da kuma ɗan takararta.