Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Aston Villa na daf da tsawaita kwantiragin Emery, Trey Nyoni zai ci gaba da zama a LIverpool
Aston Villa tana tattaunawa mai zurfi da koci Unai Emery kan sabon kwangila, bayan raɗe-raɗin da aka yi kwanan nan da ke danganta shi da Manchester United. (Telegraph)
Ana sa ran ɗan wasan tsakiya na Liverpool, Trey Nyoni mai shekara 19, zai sanya hannu kan sabon kwangila da ƙungiyar, bayan da aka ƙi amincewa da tayin fam miliyan 30 da Nottingham Forest ta gabatar domin sayen ɗan wasan na Ingila a lokacin bazara. (Athletic)
Leeds United na iya daukar ɗan wasan tsakiya na Liverpool, Harvey Elliott mai shekara 23, a matsayin ɗan wasa na dindindin a watan Janairu, yayin da ƙungiyar Valencia ke shirin kawo ƙarshen zaman aro na ɗan wasan na Ingila a wurinta. (Football Insider)
Everton na zawarcin ɗan wasan gaba na Palmeiras ɗan ƙasar Brazil, Vitor Roque mai shekara 21, wanda ake hasashen darajarsa ta kai kimanin fam miliyan 42. (Sport)
Ƙungiyoyin Manchester United da Arsenal da Chelsea duk suna sanya ido kan ɗan wasan tsakiya na Galatasaray ɗan kasar Rasha, Aleksey Batrakov mai shekara 21. (Teamtalk)
Ɗan wasan baya na Como Jacobo Ramon, mai shekara 21, yana cikin waɗanda Manchester United ke sa ido a kai, amma za su iya fuskantar ƙalubale daga Chelsea wajen neman ɗan wasan na ƙasar Spain. (Teamtalk)
Tsohon kocin Liverpool da Chelsea, Rafa Benitez, na son komawa aikin horar da ƙungiya a gasar Premier League. (Talksport)
Ƙungiyar Flamengo na nuna sha'awar ɗaukar mai tsaron gidan Liverpool, Alisson Becker, mai shekara 34, duba da cewa kwangilar ɗan wasan na Brazil a Anfield za ta ƙare ne a watan Yuni. (Sport Witness)
Ba zai yiwu Barcelona ta ɗauki ɗan wasan baya na Inter Milan, Federico Dimarco, mai shekaru 28 ba, kasancewar kungiyar ta Italiya ta yi amfani da damar tsawaita kwangilarsa da ƙarin shekara guda. (Sport)
Ƴan wasan Newcastle sun shiga ruɗani game da abin da kocin ƙungiyar, Matthias Jaissle, ke so daga gare su. (Mail)