Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko lantarkin Najeriya ya bunƙasa a lokacin Tinubu?
Jam'iyyar APC ta kare alƙawarin da Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya yi kafin zaɓen 2023 cewa zai kawo ƙarshen matsalar wutar lantarki a ƙasar cikin shekaru huɗu na farkon wa'adin mulkinsa.
APC ta mayar da martani ne kan sukar da kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC, ya yi wa shugaban ƙasar na gaza kawo ƙarshen matsalar lantarkin da ya yi alƙawari.
Wutar lantakar dai na daga cikin manyan matsalolin da ke damun ƴan Najeriya.
A lokuta da dama shugabanni da ƴansiyasa kan yi alƙawuran magance matsalar a lokutan yaƙin neman zaɓe daban-daban.
Me ADC ta ce?
Jam'iyyar ADC mai hamayya ta soki shugaban ne bisa abin da ta kira gaza cika alƙawarin da Shugaba Tinubu ya yi kan wutar lantarki a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023.
Cikin wata sanarwa da darakta yaɗa labaran kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar, Kola Ologbondiyan ya fitar, ya ce ''Tinubu ya shaida wa 'yan Najeriya a lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2023 cewa, kada ku zaɓe ni a karo na biyu idan na gaza samar da wutar lantarki," a cewar sanarwar.
Ologbondiyan ya ce wannan wani ƙwaƙƙwaran alƙawari ne da Shugaba Tinubu ya yi a matsayinsa na ɗan takarar da ke neman amincewar al'ummar ƙasar, yana mai cewa 'yan Najeriya na da haƙƙin auna aikin gwamnatinsa bisa wannan alƙawarin.
ADC ta ƙara da cewa "Babu wani gyara ta zaɓen wasu sassan magana, ƙara wasu sakin layi ko amfani da dabarun nahawu da za su iya gogewa wannan alƙawari daga tunanin 'yan Najeriya."
Ta kuma yi zargin cewa maimakon gwamnatin Tinubu ta inganta samar da wutar lantarki da rage wa masu amfani da ita raɗaɗi, gwamnatin ta sa ido ne kan ƙarin kuɗin wutar lantarki, ci gaba da yawaitar katsewar wuta da kuma ci gaba da amfani da tsarin ƙiyasta yawan wutar da aka samar.
Martanin APC
To sai dai a martanin da jam'iyyar APC ta Shugaba Tinubu ta mayar ta ce Shugaba Tinubu ya yi bakin ƙoƙarinsa wajen tabbatar da cika alƙawarinsa kan wutar lantarkin.
Cikin wata sanarwa da kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu, Dele Alake ya fitar ya fitar, ya ce ya kamata a duba cikakken alƙawarin da Tinubu ya yi a 2023 kan wutar lantarki, ba wai kawai ɓangaren da ya ce zai samar da wuta ba.
Alake ya ce ADC ta manta ɓangaren da Shugaban Tinubun ya ce idan bai cimma ba zai yi wa 'yan Najeriya cikakken bayanin dalilin hakan.
''Matsalar wutar lantarki a Najeriya ta wuce shekaru 50, don haka ba za a magance ta cikin ƙanƙanin lokaci ba'', a cewar Alake.
APC ta ce gwamnatin Tinubu ba ta kauce daga alƙawarin da ta yi ba, kuma tana ci gaba da ƙoƙarin gyara ɓangaren wutar lantarki.
Sanarwar ta jaddada cewa Najeriya ta samu ci gaba a ɓangaren samar da wutar lantarki tun bayan zuwan gwamnatin Tinubu.
APC ta yi nuni da sanya hannu kan Dokar Wutar Lantarki ta 2023, wadda ta bai wa jihohi damar shiga harkokin samarwa da rarrabar da wutar lantarki.
Ta ce wasu jihohi sun riga sun fara cin gajiyar dokar ta hanyar kafa hukumomin kula da wutar lantarki da jawo jarin masu zaman kansu.
Dele Alake ya ce gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakan biyan tarin basussukan da suka addabi kamfanonin samar da wuta da na iskar gas.
Yaya yawan lantarki a mulkin Tinubu?
Gwamnatoci da dama kan yi iƙirarin samar da ci gaba a fannin samar da wutar lantarki a zamaninta.
Kan haka ne BBC ta tuntuɓi Dr Abdurrahman Umar Lawan, ƙwararren masanin makamashin wutar lantarki a Najeriya, kuma malami a Jami'ar Bayero da ke Kano don jin ko an samu ci gaba a fannin wutar lantarkin a zamanin mulkin Tinubu.
Masanin ya ce an auna ci gaban wutar lantarki ne kan abubuwa huɗu, da suka haɗa da sauye-sauye da aiwatarwa da wutar da ake samarwa da wadda ake rarrabawa.
Malamin Jami'ar ya ce ta fuskar sauye-sauye an samu ci gaba, domin a cewarsa gwamnati ta ɓullo da sauye-sauyen masu inganci, waɗanda aiwatar da su zai taimaka matuƙa.
''Ta wannan fuska akwai tsare-tsare da gwamnatin Najeriya ta yi tun lokacin mulkin Buhari, waɗanda sun taimaka wajen inganta harkokin lantarkin'', in ji shi.
Ya ce sanadiyyar waɗannan sauye-sauyen an samu jihohi 17 da suka yi dokokin samar da wutar lantarki a jihohinsu.
To sai dai Dr Abdurrahman ya ce a ɓangaren aiwatarwa ba a samun ci gaba.
Ta fuskar faɗuwar babban layin wutar lantarki na ƙasar, masanin ya ce a wannan shekarar an samu ci gaba idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Alƙaluman lantarki daga 2022 zuwa 2026
Alƙaluman babban kamfanin samar da lantarki ta Najeriya, NERC sun nuna cewa an samu ƙaruwar wutar lantarki da ƙasar ke samarwa daga 2022 zuwa 2026, wanda ke nuna zamanin mulkin Tinubu.
A cewar alƙaluman wutar da ake samarwa ta ƙaru daga GWh 34,942 a 2022 zuwa GWh 39,209 a 2026.
Dangane da batun faɗuwar babban layin wutar lantarkin kuwa NERC ta ce sau shida ya faɗi a 2022, yayin da a 2024 ya faɗi har sau tara, yayin da 2025 ya faɗi sau biyu kacal.
Haka ma alƙaluman sun nuna cewa an samu faɗuwar babban layin lantarkin sau biyu a farkon rubu'in 2026.