Man United na harin Balde, Madrid na zawarcin Verbruggen

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan Barcelona Alejandro Balde zai iya barin ƙungiyar a watan Janairu, wanda hakan ya sa Manchester United dakon sa, bayan da ta nuna shaawarta na ɗaukar ɗan wasan. (Record, via Marca - in Portuguese)

Idan Balde ya bar Barcelona, hakan zai iya bata damar ɗauko Lisandro Martinez daga Manchester United. (Mirror)

Liverpool na hangen ɗan wasan Nottingham Forest Murillo da ɗan wasan Borussia Dortmund Nico Schlotterbeck a matsayin waɗan da za su maye gurbin Virgil van Dijjk inda ya bar ƙungiyar. (Caught Offside)

Manchester United na iay siyar da Bruno Fernandes maimakon ta bari shi ya tafi bayan ƙarewar kwantaraginsa a kaka mai zuwa. (Mail - subscription required)

Real Madrid na nazarin mai tsaron ragar Brighton Bart Verbruggen a matsayin wanda zai maye gurbin takwaransa na ƙungiyar Thibaut Courtois. (Fichajes - in Spanish)

Ɗan wasan Manchester United Marcus Rashford na duba yiwuwar barin ƙungiyar idan bai sami gurbin wasa ba, idan ya dawo taka leda daga raunin da ya samu. (Football Insider)

Har yanzu Tottenham na son ɗauko ɗan wasan Nottingham Forest Morgan Gibbs-White, sannan ta na da yaƙinin ɗauko shi a watan Janairu. (Football Insider)

Barcelona da Real Madrid na zawawarcin ɗan wasan Sipaniya Pedro Porro, duk da kudin da Tottenham ke nema kan ɗan wasan na fam miliyan 62. (Sport - in Spanish)

Ɗan wasan Monaco Folarin Balogun zai iya barin ƙungiyar a watan Janairu zuwa Manchester United. (Teamtalk)

Arsenal na fuskantar gogayya daga AC Milan, Aston Villa da Roma wajen ɗaukar Endrick daga Real Madrid. (Calcio Mercato - in Italian)

Tottenham, Manchester City da Manchester United na cikin ƙungiyoyin da ke son ɗaukar ɗan wasan Villarreal Alex Freeman. (Football Insider)