Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 06/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 06/11/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. 'Jiragen ruwa biyu sun kama da wuta bayan taka nakiya a mashigar Hormuz'

    Rundunar juyin juya halin Iran, IRGC taa ce wasu jiragen ruwa na dakon mai biyu da ke kokarin wucewa ta mashigar Hormuz sun kama da wuta bayan sun taka wata nakiya.

    Sashen rundunar sojin ruwa ta IRGC ya ce tankokin biyu sun kashe "dukkan na'urorinsu na bibiyarsu da tantancewa", kuma suna shirin bi ta mashigar ne ta wata hanyar da suka bayyana a matsayin "wadda ba a amince da ita ba".

    Sanarwar da IRGC ta fitar ba ta bayar da ƙarin bayani game da ƙasashen da suka mallaki jiragen ba.

    Iran ta ce wajibi ne jiragen su ratsa ta mashigar Hormuz ta hanyar da ƙasar ta tsara ta kuma amince da ita.

    Rahotanni sun ce wasu jiragen ruwa da na dakon mai na amfani da wata hanya da aka ƙirƙiro a 'yan makonnin nan domin kauce wa takunkuman da Iran ta sanar.

    Mashigar Hormuz na ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin sufurin makamashi a duniya.

    Kafin fara yakin Amurka da Isra'ila da Iran a watan Fabrairun wannan shekara, kusan kashi ɗaya cikin biyar na cinikin ɗanyen mai da iskar gas na duniya na bi ta mashigar.

  2. Dilolin wayoyin hannu a Najeriya na son NCC ta dakatar da dokar tantance wayoyi

    Ƙungiyar masu sayar da wayoyin hannu ta jihar Kano ta bayyana damuwa kan matakin hukumar NCC na aiwatar da wani sabon shirin tantance wayoyin hannu da sauran na’urorin sadarwa a ƙasar.

    Yayin da ya rage ƴan kwanaki hukumar ta NCC ta fara aiwatar da tsarin, ƙungiyar ta bayyana matakin a matsayin abin da zai kawo matsalolin da za su ta yi gagarumar asara da haifa da matsalar rashin aikin yi ga matasa.

    Tun da farko dai NCC ta saka wa'adin 7 ga watan Nuwamba a matsayin ranar ƙarshe da za ta rufe duka wayoyin da ba ta tantance ba a faɗin ƙasar.

    To amma ƙungiyar masu sayar da wayar ta ce ba duka nau'o'in wayoyin da take sayarwa ne hukumar ke tantancewa ba.

    ''Duka nau'o'in wayoyin da ba sabbi ba d ake kira London yus ba sa cikin waɗanda hukumar ke tantancewa, mu kuma da dama su ne muke sayarwa'', a cewar Abubakar Ibrahim Ma'aji ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar.

    Ma'aji ya ƙara da cewa matakin NCC na zuwa ne bayan sun narka kuɗaɗensu masu yawa wajen sayo wayoyin, wani abu da ya ce zai sa su tafka muguwar asara idan dokar ta tabbata.

    Ya ƙara da cewa kaso mai yawa na wayoyin da suke sayarwa, a ƙasashe maƙwabta suke sayar da su ba Najeriya, wani abu d aya ce bai kamata dokar NCC ta shafe su ba.

    A nata ɓangare hukumar NCC ta ce ta ɓullo da tsarin tantance wayoyin ne da nufin magance matsalolin barazanar tsaro da kakkaɓe ayyukan masu damfarar intanet.

  3. Sojojin Najeriya sun musanta yin sulhu da Boko Haram

    Rundunar sojin Najeriya ta ce babu batun tsagaita wuta tsakaninta da ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi na Boko Haram da ISWAP.

    Wannan na zuwa ne bayan da wata kafar yaɗa labari ta ruwaito cewa gwamnatin Najeriya ta cimma yarjejeniyar sulhu da Boko Haram ɓangaren Bakura Doro, matakin da kafar ta ce ya taimaka wajen samun zaman lafiya a wasu sassan yankin arewa maso gabashin ƙasar.

    Da yake jawabi a wani taro kan harkokin leƙen asiri a babban birnin tarayya Abuja, kakakin rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar Samaila Uba, ya ce nasarorin da aka samu a baya-bayan nan, ciki har da kashe masu tayar da ƙayar baya da kama waɗanda ake zargi da kuma kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su sun isa ƙaryata iƙirarin.

    Sojojin sun ce jami'an tsaro na ci gaba da matsa wa ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai lamba.

    "Ina so na bayyana ƙarara cewa babu maganar tsagaita wuta ko kaɗan... idan aka yi la'akari da nasarorin da aka samu a dukkan ayyukanmu, a bayyane yake cewa ba mu sassautawa," in ji Uba.

    Ya kuma ce Najeriya na tattaunawa da ƙasashen makwabta na yankin Sahel da suka fice daga ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta ECOWAS kan haɗin gwiwar tsaro da harkokin diflomasiyya

  4. Gwamnatin Amurka ta musanta ajiye aikin sakataren tsaro na waje

    Fadar White House ta musanta jita-jitar da ke cewa Sakataren Tsaro Pete Hegseth da Sakataren Harkokin Waje Marco Rubio na iya yin murabus yayin da ake hasashen za a samu sauye-sauye a gwamnatin Donald Trump bayan zaɓe.

    Kafofin watsa labarai na Amurka sun ruwaito cewa an yi kira da a cire Pete Hegseth daga muƙaminsa, musamman saboda yadda ya tafiyar da yakin da Iran, wanda wasu ke ganin yana daga cikin abubuwan da suka jawo wa jam'iyyar Republican gagarumar shan kaye a zabukan.

    Wani ɗan majalisar dokokin Republican da ke shirin barin muƙaminsa ya yi barazanar gabatar da ƙudirin tsige Hegseth a mako mai zuwa.

    Sakataren Tsaron Amurka ya kuma fitar da wani bidiyo inda ya kare matakansa tare da yin Allah wadai da wannan yunkuri.

    "Kun gani, suna sukarmu, suna sukarmu ne saboda muna yin aiki yadda ya kamata. Waɗannan yunƙuri ba za su yi nasara ba. Ba za mu ja da baya ba," in ji shi.

    Yasmin Ansari, ƴar jam'iyyar Democrat kuma Ba'amurkiya mai asalin Iran da ke wakiltar jama'a a Majalisar Dokokin Amurka, ita ma tana kira da a tsige Pete Hegseth.

    A ɗaya ɓangaren kuma, Marco Rubio ya musanta rahotannin da ke cewa yana tunanin sauka daga muƙaminsa da nufin tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2028.

    A wata hira da jaridar New York Times, Mista Rubio ya ce ci gaba da aiki tare da gwamnatin Trump har zuwa ƙarshen wa'adin shugabancinsa "shi ne shirin da nake da shi tun farko."

    Fadar White House da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka sun musanta rahotannin da ke cewa Rubio na iya sauka daga muƙaminsa bayan shan kayen da aka yi a zaɓukan wannan mako, inda dukkansu suka bayyana rahotannin a matsayin "labaran bogi".

    A ranar Alhamis, kamfanin Bloomberg ya ruwaito, yana mai ambaton majiyoyin da ba a bayyana sunayensu ba, cewa Marco Rubio na tuntubar masu ba shi shawara kan makomarsa ta siyasa.

  5. 'Iran na gyara cibiyoyin makaman linzaminta da aka lalata'

    Wani binciken hotunan tauraron ɗan'adam da BBC ta gudanar ya nuna cewa Iran na gudanar da manyan ayyukan gine-gine kusa da muhimman wuraren ajiyar makamai masu linzami guda biyu, inda ta ke ci gaba da gyare-gyare a wasu cibiyoyin da aka lalata a lokacin rikicinta da Amurka.

    Masana sun bayyana cewa hotunan na nuni da yiwuwar cewa Iran na ɗaukar matakan ne don kare kanta daga sabbin hare-hare.

    Wakiliyar BBC ta ce ana gina sabbin rufi a gine-ginen da aka ruguza a wata cibiya da ke yammacin ƙasar, yayin da a wani sansanin soji da ke gabashin birnin Tehran aka kwashe duk wasu ɓaraguzan gine-ginen da suka rushe bayan luguden wutan da aka yi a yankin

    Binciken sashen tantance bayanai na BBC dai ya nuna cewa gyare-gyaren sun shafi aƙalla cibiyoyi 12.

  6. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin kallon kyawawan bidiyoyi da ƙayatattun hotunan, sannan ku yi yi tsokaci a kai.