Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manchester United ta tuntuɓi Deschamps, Arsenal na zawarcin Tresoldi
Manchester United ta tuntuɓ tsohon kocin tawagar Faransa, Didier Deschamps, yayin da makomar koci na yanzu, Michael Carrick, ke cikin shakku. (Foot Mercato)
Duk da haka, wasu shugabannin Manchester United na goyon bayan Carrick, inda ake kallon wasan ranar Lahadi da za su fafata da Aston Villa a matsayin wani muhimmin mataki. (Sky Sports)
Arsenal na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin Turai da ke nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan gaba na Club Brugge, Nicolo Tresoldi, mai shekara 22, wanda kuma ke buga wa tawagar matasan Jamus ƴan ƙasa da shekara 21 wasa. (Tuttomercato)
Tottenham ta na da damar biyan kuɗi daidai da duk wani tayin da aka yi wa ɗan wasan gaba na Ingila, Harry Kane, mai shekara 33, a matsayin wani ɓangare na sabon kwantiraginsa a Bayern Munich. (Telegraph)
Arsenal da Manchester United na sa ido kan ɗan wasan tsakiya na Bournemouth, Marcus Tavernier, mai shekara 27. (Teamtalk)
Manchester United da Chelsea da Liverpool na sa ido kan ɗan wasan baya na Eintracht Frankfurt kuma dan ƙasar Jamus, Nnamdi Collins, mai shekara 22.(Fussball News)
Liverpool na shirin ƙara nuna sha'awarta kan ɗan wasan baya na ƙungiyar Fenerbahce, ɗan ƙasar Ingila Archie Brown, mai shekara 24. (Teamtalk)
Ƙungiyar Flamengo ta ƙasar Brazil, inda mai tsaron gidan Liverpool Alisson ya fito, na nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan mai shekara 34. (Sport Witness)
Newcastle United na da burin ɗaukar ɗan wasan gaba na Ingila, Ivan Toney, mai shekara 30, daga ƙungiyar Al-Ahli ta ƙasar Saudiyya a watan Janairu. (Football Insider)
Eintracht Frankfurt na da kyakkyawan fata na sake ɗaukar ɗan wasan gaba ɗan ƙasar Faransa, Arnaud Kalimuendo, mai shekara 24, wanda ke buga wa Nottingham Forest wasa. (L'Equipe)
Ɗan wasan gefe na Chelsea Ɗan asalin Ingila, Jamie Gittens mai shekara 22, yana ɗaya daga cikin waɗanda ƙungiyar Roma ke duba yiwuwar ɗauka domin ƙarfafa tawagarta a watan Janairu. (Gazzetta dello Sport)
AC Milan tana tattaunawa da ɗan wasan tsakiya ɗan kasar Faransa, Adrien Rabiot mai shekara 31, kan batun tsawaita kwangilarsa. (Gazzetta dello Sport)