Ina makomar Netanyahu bayan shugaban Isra'ila ya bai wa ƴan adawa damar kafa gwamnati?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Shugaban Isra'ila ya ce zai ba wa shugaban jam'iyyar adawa Gadi Eisenkot, damar kafa sabuwar gwamnatin haɗaka.

Isaac Herzog, ya na tattaunawa da jam'iyyun siyasa bayan rashin samun rinjaye a majalisar Isra'ila wato Knesset bayan zabe a makon da ya gabata.

Eisenkot zai samu kwanaki 28 yanzu don ƙoƙarin kafa sabuwar gwamnati, tare da yiwuwar ƙarin tsawon kwanaki 14.

Tsohon shugaban sojojin ya rubuta a shafinsa na X cewar, "Yanzu lokaci ne na kafa gwamnatin gaggawa ta ƙasa. Zan yi duk abin da zan iya don tabbatar da cewa mun cancanta,"

Babu jam'iyyar siyasa a Isra'ila da ta taɓa samun rinjaye kai tsaye, ma'ana duk gwamnatin da aka kafa sai da ta nemi haɗin gwiwar jam'iyyun siyasa.

Jam'iyyar Likud ta Netanyahu da ƙawayenta masu tsattsauran ra'ayi sun samu kujeru 53 a cikin kujeru 120 na majalisar watau Knesset, yayin da jam'iyyar Yashar ta Eisenkot da sauran jam'iyyun adawa 3 na Yahudawa sun samu kujeru 48.

Jam'iyyun hadaka biyu da Larabawa ke jagoranta sun samu kujeru 19 a karon farko sakamakon karin da aka samu na Larabawa masu kaɗa ƙuri'a. Lamarin da ya sanya su a matsayin masu yanke hukunci a siyasa. Sai dai akwai jam'iyar Yahudawa guda ɗaya da ta dauki alwashin ba zata kafa gwamnati da Larabawa ba.

Herzog ya ce bayan ya tuntuɓar jam'iyyu cikin makon nan zai ba Eisenkot damar farko ta kafa gwamnati.

Wata sanarwa daga ofishin shugaban kasa ta ce ya shaidawa Eisenkot da Netanyahu shirin sa.

Bayan tattaunawa da wakilan sabbin ƴan majalisa, Eisenkot ya samu kashi 67 na goyon baya ya yin da Netanyahu ya samu 46.

Shugaban kasa na da ikon zaɓar wanda yake ganin nada damar kafa gwamnati ba dole ba ne sai ya zabi shugaban jam'iyyar data samu rinjaye a majalisa.

Sakamakon zaben ya bayar da zaɓi 3 don kafa gwamnatin: shugabancin hadin kan kasa wanda zai hada Netanyahu da Eisenkot, da hadin kan masu tsattsauran ra'ayi da Netanyahu da wadanda suka sauya sheƙa daga jam'iyyar Eisenkot, da kuma gwamnatin da Eisenkot zai jagoranta wadda jam'iyyun Larabawa za su goyi baya.

Eisenkot da duk membobin jam'iyyarsa sun ƙi amincewa da hadin gwiwa da jam'iyyun Larabawa amma ana ganin akwai yiwuwar cimma wata yarjejejiya.

Haka kuma zai iya kokarin ƙulla yarjejeniya da jam'iyyu masu tsauraran ra'ayi sai dai akwai yi wuwar ya fuskanci ƙalubale.

Mece ce makomar Netanyahu?

Farfesa Tukur Abdulkadir masanin siyasar duniya kuma Malami a Jami'ar Jihar Kaduna ya ce '' Dama wannna batu abu ne da ake saran zai faru, illa dai ba za a ce tsakanin Netanyahu da Eisenkot da sauransu waye za a zaba ba., don ba abin mamaki bane."

"Idan aka yi la'akari da bambance-bambance da suka wakana tsakanin Eisenkot da Netanyahu, sanann a baya ma ya taba yin aiki da Netanyahu, saboda haka a yanzu sun samu baraka da rarrabuwa ga kuma matsaloli na cikin gida wanda bahsi da nasaba da hakkoki ko 'yancin Falasdinawa, illa dai wasu abubuwa ne da suka shafi akidu na Yahudawa suke kawo rarrabuwar kai a tsakaninsu." In ji shi.

Farfesan ya ce, "daga karshe za a iya kafa gwamnatin hadin gwiwar har da ma sauran jam'iyyun Larabawa."

''Idan gwamnatin adawa ta kafa gwamnati a Isra'ila, la'akari da yadda zabukan Amurka suka kasance mafiya yawan ƴan jam'iyyar Democrat basa goyon bayan yaƙi don haka akwai yiwuwar takun Isra'ila zai sauya musamman a yaƙin da ta ke yi da Falasɗin da Iran har ma da Lebanon kasancewar Amurka ce uwar ɗakin Isra'ila in ji Farfesa Abdulkadir.

Akwai tarihin kafa gwamnati haɗaka. A shekara ta 2020 bayan zaɓuka uku da aka samu sakamako iri ɗaya, Netanyahu da abokin hamayyarsa mai matsakaicin ra'ayi Benny Gantz sun amince da yarjejeniyar raba iko tsakaninsu.

Ya yin da ya ke tuntuɓar jam'iyyun, Herzog ya ce don magance zagaye na biyu a zaɓe da kuma samun damar kafa gwamnati mai ƙarfi, ya na son ''jam'iyyu da wakilansu su fahimci cewar ba kowanne alƙawari za a cika ba."

Tsakanin shekara ta 2019 zuwa 2022 an gudanar da zaɓe cike da rarrabuwar kai a siyasar Isra'ila inda aka gudanar da zaɓuka 5 ya yin da Netanyahu da abokan hamayyarsa ke fafutukar neman haɗin kai.

Ko Eisenkot zai iya kafa gwamnatin haɗaka?

Yanzu Eisenkot zai samu kwanaki 28 domin ƙoƙarin kafa sabuwar gwamnati, tare da yiwuwar ƙarin kwanaki 14 idan ya nemi ƙarin lokaci.

"Yanzu ne lokacin kafa gwamnatin gaggawa ta ƙasa. Zan yi duk mai yiwuwa don tabbatar da cewa mun cancanci wannan nauyi," in ji tsohon shugaban hafsoshin sojin a wani saƙo da ya wallafa a shafin X.

Babu wata jam'iyyar siyasa a Isra'ila da ta taɓa samun rinjaye kai tsaye a majalisa, don haka duk gwamnatocin ƙasar na kasancewa ne ta hanyar haɗakar jam'iyyu.

Jam'iyyar Likud mai ra'ayin mazan jiya ta Netanyahu tare da abokan haɗakarta na masu tsattsauran ra'ayi da Yahudawan Orthodox masu ra'ayin addini sun samu kujeru 53 cikin kujeru 120 na Majalisar Knesset.

A gefe guda kuma, jam'iyyar Yashar mai matsakaicin ra'ayi ta Eisenkot tare da wasu jam'iyyun adawa uku na Yahudawa sun samu kujeru 48.

Ƙungiyoyin siyasa biyu masu wakiltar Larabawan Isra'ila, wato United Arab List da Joint List, sun samu kujeru 19 gaba ɗaya, lamarin da ba a taɓa gani ba, bayan karuwar yawan masu kaɗa ƙuri'a daga al'ummar Larabawa.

Wannan ya sanya su cikin matsayin da za su iya taka muhimmiyar rawa wajen tantance wanda zai kafa gwamnati. Sai dai kusan dukkan jam'iyyun Yahudawa ban da guda ɗaya sun yi alƙawarin kafin zaɓen cewa ba za su yi haɗin gwiwa da su domin kafa gwamnati ba.

Herzog ya ce bayan shawarwari da dukkan jam'iyyun siyasa a cikin makon, ya yanke shawarar bai wa Eisenkot dama ta farko wajen kafa gwamnati.

Wata sanarwa daga ofishin shugaban ƙasar ta ce an sanar da Eisenkot da Netanyahu wannan mataki.