Me ya sa ake kai wa tarukan jam’iyyun hamayya hari a Najeriya?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

A Najeriya siyasa na ci gaba da daukar zafi yayin da ‘yan siyasa ke son cin gajiyar kowace dakika gabanin babban zaben kasar na 2027.

Jam’iyyar APC mai mulkin kasar ta kaddamar da yakin neman zaben shugaba Bola Tinubu a wa’adi na biyu, yayin da ita ma babbar jam’iyyar hamayya ta ADC ta kaddamar da yakin neman zaben nata dan takarar shugaban kasar a garin Sokoto.

To sai dai wani abu da ya fito zahiri shi ne yadda aka rika samun tashin hankali a irin wadannan wurare na kamfe.

Waɗannan abubuwa da ke faruwa dai na yi wa dimokuraɗiyya barazana da kuma janyo rashin tabbas kan yadda zaɓuka za su gudana.

Jam'iyyun adawa sun bayyana damuwa kan abin da suka kira ƙaruwar muzgunawa mabiyansu da kuma 'yan takara da ake yi a faɗin Najeriya.

Sun yin zargin cewa ana amfani da 'yan daba wajen tarwatsa gangamin yaƙin neman zaɓensu, inda suka ce jami'an tsaro ba sa ba su isasshiyar kariya.

Haka kuma sun yi zargin cewa wasu gwamnatocin jihohi na tsauwala kuɗin haya na kama wuraren gangami domin hana su yaɗa manufofin 'yan takararsu, sai dai wasu daga cikin gwamnaticin jihohin sun musanta wannan zargi.

Waɗannan zarge-zargen na ƙara tayar da hankali ne saboda suna zuwa ne a daidai lokacin da ya kamata 'yan Najeriya su rika ganin cigaban dimokuraɗiyya da 'yancin siyasa, yayin da ƙasar ke tunkarar zaɓen 2027.

Jam'iyyun da aka kai wa hari

A baya-bayan nan, jam'iyyar ADC ta zargi gwamnatin jihar Sokoto da rufe daya daga cikin ofisoshinta na yaƙin neman zaɓe, tare da hana bayar da masaukin wakilan jam'iyyar, da kuma bari a kai wa mata masu goyon bayanta hari a yayin wani gangamin siyasa. Gwamnatin ta musanta wannan zargi.

A jihar Rivers kuwa, ADC da Zenith Labour Party sun yi zargin cin zarafin magoya bayansu da kuma yunkurin hana tarukan ƴan adawa.

Har ila yau, a can jihar Ekiti, jam'iyyar African Action Congress (AAC) da wasu ƙungiyoyin ƴan adawa sun ruwaito cewa an kai musu hare-hare, ciki har da far wa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar, Omoyele Sowore.

A ɗaya gefe, rahotanni sun bayyana cewa an far wa ayarin motocin yaƙin neman zaɓe na ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi a jihar Cross River, wanda ake zargin ƴan dabar siyasa da aikata wa.

A Neja ma, jam'iyyun adawa sun zargi jam'iyyar APC mai mulki da amfani da ƙarfin iko wajen musgunawa da kuma hana su tarukan yaƙin neman zaɓe.

Daya daga cikin masu magana da yawun jam’iyya ta APC, Bala Ibrahim, a wata tattaunawa da BBC, ya ce babu wata kwalkwarar hijja da ke nuna cewa tabbas jam’iyyar ce ke da alhakin hakan.

Barazanar da jam'iyyun adawa ke ciki

Waɗannan hare-hare da jam'iyyun adawa ke zargin ana kai musu, na ƙara nuna irin barazanar da suke ciki gabanin zaɓukan da ke tafe.

Zargin kai wa ƴan adawa hare-haren a faɗin yankunan Najeriya, na iya janyo damuwa matuka a tsakanin ƴan Najeriya, cibiyoyin dimokuraɗiyya da kuma al'ummomin ƙasashen waje.

Masana siyasa na ba da shawarar cewa ya kamata a ɗauki matakin da ya dace domin dakatar da abin da ke faruwa.

Sun ce akwai buƙatar mutunta doka da kuma yin adalci ga duka ɓangarori.

Babbar barazana ce idan aka bar irin waɗannan abubuwa suka ci gaba da faruwa, wanda zai iya jefa Najeriya cikin rikicin siyasa da tashin hankali har da zai kai ga jawo tsaiko a zaɓen da ke tafe, a cewar masana.

Sun ce ɗaya daga cikin ginshikan dimokuraɗiyya ita ce bai wa kowane ɗan ƙasa ƴanci da kuma jam'iyyun siyasa damar shiga zaɓe a dama da su, ba tare da musgunawa ba.

Jam'iyyun siyasa na da ƴanci na kundin mulki wajen shirya tarukan yaƙin neman zaɓe, tallata ƴan takara da kuma nema musu goyon baya a wurin jama'a.

Don haka ne masu sharhi suka ce, ba daidai ba ne magoya bayan jam'iyya mai mulki su ɓige da tashin hankali, yin barazana ko kuma janyo tsaiko ga tarukan kamfe na ƴan adawa.

Ko me kai waɗannan hare-hare ke nufi?

Wani masanin harkokin siyasa a Najeriya, Dakta Kabiru Sufi ya ce hare-haren da ake aki wa ƴan adawa wani sabon salo ne da ƴan siyasa suka fito da shi don nuna cewa jama'a ba su tare da mutum.

"A baya, ana iya yin haka amma mutane ne ke shiga cikin tawaga su yi ihun ba ma yi sai a sake a kafofin sada zumunta ya yi ta yawo don nuna cewa wani ɗan siyasa bai samu karɓuwa ba da ya je kamfe," in ji Kabiru Sufi.

Ya ƙara da cewa wannan sabon salo ne na farfaganda a juna da ƴan siyasa suka fito da shi, kuma ana yi wa duka jam'iyyu haka tun da zamani ne na amfani da kafofin sada zumunta.

Dakta Sufi ya ce waɗannan hare-hare na nufin cewa akwai matsalar tsaro a cikin al'umma gabanin zaɓen 2027.

"Far wa ƴan adawar zai iya kuma saka jama'a su ƙaurace wa duk abin da ya shafi siyasa ko zaɓe saboda tsoron kada abin ya rutsa da su.

"Duk abin da kuma zai janyo fargaba a zuƙatan al'umma ko ƴan siyasa ya zama babban nakasu ga al'amuran da ke faruwa a ƙasar," in ji Kabiru Sufi.

Wane mataki ya kamata a ɗauka?

Masanin harkokin siyasara ya ce ya kamata jam'iyya mai mulki da jam'iyyun hamayya su kyamaci wannan al'amari nan, tare da mutunta yarjejeniyar zaman lafiya, don kauce wa shiga yanayin da ba zai yi wa kowa daɗi ba.

Ya ce akwai buƙatar ƴan siyasar su hana magoya bayansu ta da fitina.

"Idan suka nuna ba su tare da abin da ke faruwa da hana magoya bayansu halartar taruka da ba na su ba, wannan zai saka a samu sauki," in ji Sufi.

Ya ƙara da cewa idan jama'a suka kyamaci irin hare-haren da ake kai wa ƴan adawa, sannan aka yi ƙoƙarin hana waɗanda ke yi ko miƙa su ga jami'an tsaro, za a samu saukin lamarin.

"Su ma dole jami'an tsaro su farka wajen hana afkuwar irin waɗannan hare-hare a lokacin tarukan yaƙin neman zaɓe.