Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid da PSG na hamayya kan Suzuki, Bayern na son tsawaita zaman Olise
Kyakkyawan yanayin da mai tsaron gidan Aston Villa, Zion Suzuki, ke samu a halin yanzu ya fara ɗaukar hankalin Paris St-Germain da Real Madrid; yayin da Arsenal, da Liverpool da Manchester City da Tottenham su ma suke sanya ido kan ɗan wasan na ƙasar Japan mai shekara 24. (Teamtalk)
Bayern Munich ta shirya mayar da hankalinta kan tsawaita kwantiragin ɗan wasan gefe na Faransa, Michael Olise mai shekara 24, bayan da ɗan wasan gaba na Ingila, Harry Kane, ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya tare da zakarun na Jamus. (Football Transfers)
Inter Milan na duba yiwuwar ɗaukar dan wasan baya na Crystal Palace kuma ɗan ƙasar Amurka, Chris Richards mai shekara 26, wanda kwantiraginsa da ƙungiyar ta Eagles zai ƙare a bazara mai zuwa. (Tuttomercatoweb)
Manchester United ba ta gamsu da tsohon kocin Newcastle United da Bournemouth, Eddie Howe, a matsayin wanda zai iya maye gurbin Michael Carrick a Old Trafford ba. (Independent)
Liverpool da Manchester United da Chelsea da Newcastle United da Tottenham da Leeds United da Brentford na daga cikin waɗnda ke sanya ido kan ɗan wasan baya na AC Milan, ɗan ƙasar Belgium mai shekara 24, Koni de Winter. (Caughtoffside)
Newcastle na zawarcin ɗan wasan gaba na Middlesbrough, ɗan ƙasar Ingila mai shekara 21, Will Lankshear, bayan bajintar da ya nuna a ƙungiyar da ke fafutukar samun gurbi a gasar Premier. (Talksport)
Har yanzu ba a fara tattaunawa ba kan yiwuwar mayar da yarjejeniyar aro ta dan wasan gaba na Jamus, Niclas Fullkrug—mai shekaru 33—daga West Ham zuwa Werder Bremen ta zama ta dindindin. (Sky Sports Germany - a harshen Jamusanci)
Barcelona na shirin kammala ƙulla sabuwar yarjejeniya da ɗan wasan tsakiya na ƙasar Spain, Marc Bernal, mai shekara 19, wanda wasu ƙungiyoyin gasar Premier League ke nuna sha'awar ɗaukar sa. (Mundo Deportivo)
Real Madrid na shirin tabbatar da cewa shigar JJ Gabriel cikin babban tawagar ƙungiyar ta kasance mai sauƙi da kwanciyar hankali—saɓanin irin wahalhalun da ɗan wasan tsakiya mai shekara 16, ya fuskanta a Manchester United—yayin da suke kammala ƙulla yarjejeniyarsa ta komawa Bernabeu. (Marca)
Shugaban Napoli, Aurelio de Laurentiis, na shirin gudanar da tattaunawa ta gaggawa tare da babban koci Massimiliano Allegri da ma'aikatansa, da ƴan wasa, domin gano musabbabin rashin samun tagomashi a farkon kakar wasa da ƙungiyar ta yi. (Football Italia)