Musulmai 9 da suka lashe zaɓen rabin wa'adi a Amurka

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

'Yan takara Musulmi sun kafa tarihi a zaɓen tsakiyar wa'adin shugabancin Amurka da aka gudanar ranar Talata, inda suka samu kujeru a Majalisar Dokokin ƙasar da kuma majalisun dokokin jihohi, duk da yaƙin neman zaɓen da ya gudana cikin ƙarin kalaman ƙiyayya ga Musulmi da hare-hare kan al'ummominsu.

Sakamakon zaɓen ya haɗa da zaɓen Sanatan Musulmi na farko a tarihin Amurka, wani likitan tiyata Ba'amurke dan asalin Masar wanda ya kula da Falasɗinawa da suka jikkata a Gaza, da kuma 'yan takara da dama masu asalin Falasɗinu.

Waɗannan nasarori sun zo ne bayan Shugaba Donald Trump da ƙawayensa na siyasa sun kai hari kan 'yan takara Musulmi, musamman Abdul El-Sayed na jihar Michigan, wanda ya fuskanci zarge-zargen da ba su da tushe da ke danganta shi da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi.

An ruwaito cewa aƙalla 'yan takara Musulmi bakwai ne suka samu nasarar shiga Majalisar Dokokin Amurka, ciki har da Sanata guda da wakilai shida a Majalisar Wakilai.

Ga wasu daga cikin fitattun 'yan takarar da suka samu nasara:

Abdul El-Sayed: Sanatan Amurka na farko musulmi

Abdul El-Sayed, mai shekaru 42, ɗan jam'iyyar Democrat mai asalin Masar, ya kayar da ɗan takarar jam'iyyar Republican, Mike Rogers, a jihar Michigan, inda ya zama Musulmi na farko da aka zaɓa a matsayin Sanata a tarihin Amurka.

El-Sayed likita ne kuma ƙwararre a fannin lafiyar al'umma. A lokacin yaƙin neman zaɓensa, ya mayar da hankali kan inganta harkokin kiwon lafiya, rage tsadar rayuwa da kuma rage tasirin manyan kamfanoni a harkokin siyasa.

Ya kuma soki tallafin soji da Amurka ke bai wa Isra'ila da Masar, tare da ƙaryata zarge-zargen da abokan hamayyarsa na siyasa suka yi na cewa yana da alaƙa da ƙungiyar 'yan'uwan Musulmi (Muslim Brotherhood).

Adam Hamawy: Likitan tiyata a Gaza da aka zaɓa zuwa Majalisar Dokokin Amurka

Likitan tiyata Ba'amurke mai asalin Masar, Adam Hamawy, ya kayar da ɗan takarar jam'iyyar Republican, Greg Mele, a zaɓen mazabar majalisa ta 12 ta jihar New Jersey, inda ya zama Musulmi na farko da ya wakilci jihar a Majalisar Dokokin Amurka.

Hamawy, wanda ya taɓa zama likitan tiyata a rundunar sojin ƙasar Amurka, ya taimaka wajen ceton ran Tammy Duckworth, wadda daga baya ta zama Sanata, bayan da aka harbo jirgin helikwafta da take ciki a ƙasar Iraƙi a shekarar 2004.

Daga baya, ya je Gaza a matsayin mai aikin sa-kai, inda ya kula da Falasɗinawa da suka jikkata sakamakon hare-haren Isra'ila, ciki har da yara da suka samu munanan raunuka.

Rashida Tlaib: 'Yar majalisar dokokin Amurka mai asalin Falasɗinu ta sake lashe zaɓe

Rashida Tlaib ta samu nasarar lashe wa'adinta na biyar a matsayin wakiliyar mazabar majalisa ta 12 ta jihar Michigan.

'Yar siyasar jam'iyyar Democrat mai asalin Falasɗinu, wadda ta kasance cikin mata Musulmi biyu na farko da aka zaɓa zuwa Majalisar Dokokin Amurka a shekarar 2018, ta ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin fitattun masu sukar yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza.

Ilhan Omar: Ba'amurka 'Yar asalin Somaliya da aka sake zaɓe karo na biyar

Ilhan Omar ta sake lashe zaɓe a matsayin wakiliyar mazabar majalisa ta biyar ta jihar Minnesota.

'Yar siyasar jam'iyyar Democrat mai asalin Somaliya, wadda ita ma tana cikin mata Musulmi na farko da suka shiga Majalisar Dokokin Amurka, ta sha sukar tallafin da Amurka ke bai wa Isra'ila, sannan ta fuskanci hare-hare da suka fito daga Shugaba Donald Trump.

Darializa Avila Chevalier: Musulma 'yar Latino ta farko da aka zaɓa 'yar majalisar dokoki

Darializa Avila Chevalier ta lashe zaɓen wakiltar mazabar majalisa ta 13 ta jihar New York.

An bayyana cewa 'yar siyasar jam'iyyar Democrat mai shekaru 33, wadda ta fito daga zuriyar 'yan ƙasar Jamhuriyar Dominika, ta zama mace Musulma 'yar asalin Latin Amurka ta farko da aka zaɓa zuwa Majalisar Dokokin Amurka.

Ta fara shahara ne sakamakon fafutukar kare haƙƙin bil'adama da kuma shiga zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu.

Andre Carson da Lateefah Simon

Wasu 'yan siyasa Musulmi biyu na jam'iyyar Democrat su ma sun samu nasarar sake lashe zaɓe zuwa Majalisar Wakilai.

Andre Carson ya sake lashe zaɓen wakiltar mazabar majalisa ta bakwai ta jihar Indiana, wadda yake wakilta tun shekarar 2008.

Ita kuwa Lateefah Simon, mai fafutukar kare haƙƙin bil'adama, ta samu nasarar lashe wani wa'adin a matsayin wakiliyar mazabar majalisa ta 12 ta jihar California.

Aber Kawas: Nasarar 'yar asalin Falasɗinu

An bayyana cewa Aber Kawas, wata mai fafutukar siyasa Ba'amurkiya 'yar asalin Falasɗinu, ta lashe zaɓen wakiltar mazabar majalisar dattawa ta 12 ta jihar New York.

An ruwaito cewa iyalinta sun rasa matsuguninsu a Falasɗinu a shekarar 1948, kafin daga bisani su zauna a Amurka.

A lokacin yaƙin neman zaɓenta, Kawas ta mayar da hankali kan samar da gidaje masu sauƙin arha, inganta harkokin kiwon lafiya, kare haƙƙin baƙin haure da kuma adawa da tallafin kuɗaɗen da Amurka ke bai wa Isra'ila domin yaƙin da take yi a Gaza, wanda ta bayyana a matsayin kisan kare dangi.

Abbas Alawieh: ɗan asalin Lebanon

An bayyana cewa Abbas Alawieh, ɗan siyasar jam'iyyar Democrat Ba'amurke mai asalin Lebanon, ya lashe zaɓen wakiltar mazabar majalisar dattawan jihar Michigan ta biyu, wadda ta haɗa da birnin Dearborn da sauran yankunan da ke kewaye da shi.

Alawieh na daga cikin waɗanda suka taimaka wajen kafa ƙungiyar Uncommitted Movement, wadda ta ƙalubalanci goyon bayan tsohon Shugaban Amurka Joe Biden ga Isra'ila a lokacin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2024.

Nabeela Syed

Nabeela Syed, 'yar siyasar jam'iyyar Democrat Ba'amurkiya Musulma mai asalin Indiya, ta kayar da ɗan takarar jam'iyyar Republican, Darby Hills, a zaɓen wakiltar mazabar majalisar dattawan jihar Illinois ta 26.

Syed, wadda a baya ta kasance 'yar majalisar wakilan jihar, ta samu nasarar lashe kujerar, lamarin da ya sauya ikon riƙe wannan kujera daga jam'iyyar Republican zuwa jam'iyyar Democrat.