Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Masana sun gano yadda za a haihu ba tare da saduwa ko dashe ba
A cikin shekaru goma da suka gabata, na yi hasashe mai ƙarfi game da makomar jima'i.
Ɗaya daga cikin hasashen da na yi shi ne cewa mutane za su ci gaba da yin jima'i na shekaru masu zuwa, amma ba domin samun yara ba kamar yadda aka saba. A maimakon haka, fasaha za ta canja yadda ake haihuwa da samun zuri'a.
Wannan ba yana nufin cewa mutane za su daina haihuwa gaba ɗaya ba. Sai dai hanyoyin samun yara zai sauya sakamakon cigaban kimiyya.
A zahiri, za a iya samun hanyoyi mafi sauƙi da aminci na haihuwa, wanda zai sa yadda muka saba fahimtar haihuwa ta hanyar jima'i ya sauya.
Har zuwa kimanin ƙarni guda da ya gabata, mutane suna samun ƴaƴa ne ta hanyar haɗuwar maniyyi da ƙwai cikin yanayi na ɗabi'a, wanda galibi ba a tsara sakamakonsa ba.
Daga baya, an fara amfani da hanyar saka maniyyi ta wucin gadi, sannan shekaru 45 da suka gabata aka samu hanyar dashen ɗan tayi wato IVF.
Ko da yake waɗannan hanyoyin sun taimaka wa mutane da dama, har yanzu sun dogara ne kan ƙwai da maniyyi da aka samo daga jikin ɗan adam. Amma da cigaban fasahar, ana sa ran hakan zai sauya.
Mataki na gaba shi ne fasahar da ake kira In Vitro Gametogenesis (IVG), wato samar da ƙwai da maniyyi daga ƙwayoyin fata.
Wannan fasaha na iya zama babban cigaba ga miliyoyin ma'auratan da ke fama da matsalolin haihuwa. Sai dai kuma tana haifar da tambayoyi masu wahala na ɗabi'a da zamantakewa.
Alal misali, idan za a iya samar da ƙwai daga ƙwayoyin fata, to mutum mai shekaru 90 zai iya zama mahaifi ko uwa ta hanyar gado.
Haka kuma yara masu shekaru tara, tayin da bai kammala girma ba, ko ma mutanen da suka mutu shekaru da dama da suka gabata amma aka adana ƙwayoyinsu, za su iya kasancewa iyaye ta fuskar gado.
Haka kuma, me zai hana a samar da maniyyi daga ƙwayoyin fata na mace, ko kuma ƙwai daga namiji?
Akwai yiwuwar hakan ya zama gaskiya nan ba da jimawa ba. A shekarar 2023, masana kimiyya a Japan sun sanar da cewa sun samar da ƙwai daga ƙwayoyin fata na ɓeraye maza, sannan suka yi amfani da maniyyi daga wani ɓera na daban suka haifar da ƙananan ɓeraye masu rai.
Haka kuma, za a iya samar da ƙwai da maniyyi daga mutum ɗaya, sannan a haɗa su domin samar da ƙwayoyin halitta na tayi.
Idan aka raya wannan ɗan tayin har ya zama jariri, za a iya samar da yaro wanda asalinsa na gado ya haɗa gudunmawar iyaye huɗu, ko takwas, ko ma goma sha shida ko fiye da haka.
Bunƙasar fasaha
Wata fasaha da za ta iya sauya yadda ake samun haihuwa a duniya ita ce damar da ake da ita ta gyara kwayoyin halitta na jariri tun yana cikin mahaifa.
An samu wannan dama ne bayan ƙirƙirar wata muhimmiyar fasaha a shekarar 2012 da ake kira CRISPR, wadda ke bai wa masana damar gyara wasu sassan ƙwayoyin halitta cikin sauƙi.
A watan Nuwambar 2018, wani masanin kimiyya ɗan ƙasar China mai suna He Jiankui, ya sanar da haihuwar tagwaye mata guda biyu, waɗanda aka yi wa ƙwayoyin halittarsu gyara ta hanyar tsarin CRISPR tun lokacin da suke a matsayin ƴan tayi.
Sai dai an bayyana cewa ya gudanar da wannan bincike ne a ɓoye, tare da karya ƙa'idojin binciken kimiyya da suka shafi ɗan'dam da kuma dokokin ƙasar China.
Daga bisani wata kotu a China ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan yari, yayin da wata kotun kuma ta zarge shi da aikata laifin karya doka.
(Yanzu waɗannan yara biyu sun haura shekara biyar da haihuwa, amma gwamnatin China ba ta fitar da wani bayani kan lafiyarsu ko kuma yadda ƙwayoyin halittarsu suke ba.)
Ana canza ƙwayoyin halittar da za su kasance a dukkan sassan jiki, lokacin da ake sauya ɗan tayi a farkon matakan samuwarsahar da ƙwayoyin haihuwa kamar ƙwai da maniyyi.
Sai dai abin da ya fi tayar da hankali, ko da yake ba shi da yuwuwar faruwa sosai, shi ne amfani da fasahar wajen ƙirƙirar "yara na musamman" masu basira ko ƙwarewa ta musamman, waɗanda kuma za su iya gado wa 'ya'yansu irin waɗannan siffofi.
Wasu mutane na ganin bai kamata a taɓa bai wa mutane damar sauya ƙwayoyin halitta ba saboda irin tasirin da hakan zai iya yi na dogon lokaci. Wasu kuma suna ganin bai kamata a yi amfani da fasahar yanzu ba domin har yanzu ba a tabbatar da ingancinta ba.
A shekarar 2017, masu bincike sun sanar da cewa sun samu nasarar raya jariran raguna da aka haifa mako guda ko biyu kafin cikar wa'adinsu a cikin wasu jakukkuna da aka cika da wani ruwa na musamman.
A baya-bayan na, Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Amurka (FDA) ta gudanar da taron tattaunawa kan ko ya kamata, yaushe, da kuma yadda za a fara gwajin irin waɗannan jakukkunan haihuwa a jariran da aka haifa kafin cikar lokacinsu.
Wannan ci gaba na iya zama abin farin ciki ga iyaye da jariran da aka haifa kafin lokaci, amma ba zai sauya rayuwar mafi yawan mutane sosai ba.
Amma me zai faru idan aka samar da mahaifa ta wucin gadi wadda za ta iya karɓar ɗan tayi mai kwanaki shida ko bakwai, ta kuma rene shi na tsawon watanni tara har ya zama cikakken jariri mai lafiya?
Hakan ba kawai zai maye gurbin wasu hanyoyin samun ciki ba, zai iya kawar da buƙatar mace ta ɗauki ciki. Wasu mutane za su yi maraba da wannan, yayin da wasu kuma za su ji tsoro ko nuna shakku.
A yau, wani babban fanni na bincike na amfani da ƙwayoyin jiki wajen samar da gaɓoɓin jikin ɗan'dam.
An fi mayar da hankali ne kan gaɓoɓi masu muhimmanci kamar ƙoda, hanta da zuciya. Amma idan za a iya samar da waɗannan, me zai hana a samar da mahaifa ma?
Alal misali, ka yi tunanin wata mahaifa da aka samar daga ƙwayoyin jikin mace, sannan aka haɗa ta da wata na'ura da ke samar da jini, sukari, iskar oxygen da sauran sinadarai, tare da wata tsarin tace dattin jiki. Daga nan sai a saka ɗan tayi a ciki.
Muna rayuwa ne a wani zamani mai ban mamaki a fannin likitanci da ilimin halittu.
Iliminmu na ƙaruwa cikin sauri. Ƙarfinmu na amfani da wannan ilimi yadda ya dace yana ƙaruwa a hankali. Sai dai fahimtarmu game da illolin sabbin fasahohi da kuma yarjejeniyar da ya kamata a yi kan iyakokinsu na ci gaba sannu a hankali.
Ƙirƙirar yara ta hanyar fasaha ba abu ne mai sauƙi ko marar muhimmanci ba. Ni na amince da shiga wani gwajin kimiyya tare da haɗuransa domin amfanin kaina ko domin cigaban kimiyya.
Amma yara ba za su iya amincewa da wannan ba, haka ma ƴan tayi.
Wannan ba yana nufin cewa bai kamata mu yi amfani da sabbin fasahohi wajen haihuwa da renon yara ba.
Sai dai, yana nuna cewa wajibi ne mu yi taka-tsantsan sosai, mu tabbatar an gwada waɗannan fasahohi yadda ya kamata, su kasance suna da kariya da kuma amfani ga yaran.