Me ya sa ƴan Spain ke yawan yin ‘kiss’?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A ƙasar Sifaniya, sumbata a bainar jama'a abu ne da aka saba gani. Ba wai sumbatar gaisuwa ta kumatu biyu kawai ba, har da ta masoya a wurare daban-daban.

Sau da dama mutum kan ga ma'aurata suna tsayawa a tsakiyar titi suna sumbatar juna. Haka kuma ana ganin samari da 'yan mata suna sumbata a wuraren shakatawa, ko kuma wajen shagali suna nuna soyayyarsu a lokacin bukukuwa. Har ma wasu mutane kan tura saƙonnin imel dinsu da kalmar "besos", ma'ana "sumbata".

Bayan fiye da shekara shida da zama a Sifaniya, na saba da irin waɗannan abubuwan da ke nuna soyayya a bainar jama'a. Sai dai wata kawata ta sake lura da hakan sosai ne bayan ta dawo daga wata tafiya zuwa Japan.

Da ta fito daga tashar jirgin ƙasa a Valencia, abu na farko da ta gani shi ne wasu masoya suna sumbatar juna a kan wani benci. Bayan zamanta a ƙasar da ba kasafai ake nuna soyayya a bainar jama'a ba, ganin hakan ya sa ta ji daɗin komawa gida.

Wannan ya sa na fara tambayar ko da gaske Sifaniya ce ƙasa ce ƙasar da aka fi yawan sumbata, da kuma abin yawan nuna soyayya a bainar jama'a.

Masana na ganin cewa yawan sumbata a bainar jama'a a Sifaniya na da nasaba da yadda mutane ke gudanar da rayuwarsu a wuraren taruwar jama'a. A sassa da dama na ƙasar, mutane kan cika lokutansu a tituna da gidajen abinci da wuraren shakatawa, inda suke yawan haɗuwa da mu'amala da juna.

Wani bincike ya nuna cewa mutanen Sifaniya na daga cikin al'ummomin da suka fi jin daɗin kusanci da juna yayin mua'amala, idan aka kwatanta da wasu ƙasashen Turai.

Ana iya ganin hakan a bayyane a filayen taro da wuraren shakatawa, inda abokai da iyalai ke zama kusa da juna suna hira da nishaɗi.

Malamar ilimin zamantakewa Amparo Lasén ta ce mutanen Sifaniya kan fi nuna damuwa ko farin ciki da sauran abubuwan da suke ji ta hanyar mu'amala ta jiki idan aka kwatanta da mutanen arewacin Turai.

Sai dai masana na cewa wannan ba yana nufin mutanen Sifaniya sun fi sauran mutane nuna soyayya ba ne. Abin da ya bambanta shi ne yadda suke kallon nuna irin wannan kusanci a bainar jama'a, domin suna ɗaukarsa wani abu ne na yau da kullum.

Haka kuma, tsarin zamantakewa na iya taka rawa. Akwai matasa da yawa da ke ci gaba da zama tare da iyayensu saboda tsadar gidaje. Hakan na sa su fi amfani da wuraren taruwar jama'a wajen ganawa da abokai da masoyansu.

Masaniyar zamantakewa, Lasén, ta ce ƙarancin samun keɓantaccen wuri a gida kan sa mutane su nemi damar nuna soyayya a wuraren jama'a.

Ta ce, "A Sifaniya muna fuskantar matsalar gidaje, wanda ya sa mutane suka fi saba haɗuwa da abokansu a waje, kamar mashaya ko gidajen abinci, maimakon a gidajensu." Ta ƙara da cewa hakan na sa ma'aurata su nemi wani wuri mai ɗan nisa da jama'a domin samun lokaci tare su kaɗai, ko da kuwa ba cikakkiyar keɓancewa ba ce.

Sai dai Lasén ta ce matsalar gidaje ba ita ce babban dalilin da ke sa nuna soyayya a bainar jama'a ya zama ruwan dare a Sifaniya ba. A cewarta, abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda al'umma ke kallon irin waɗannan abubuwa cikin sauƙi.

Ta ce, "Idan babu wanda zai yi maka kallon ƙyama ko kuma ba ka damu da ra'ayin mutane ba, hakan ne ke sa ya fi sauƙi a nuna soyayya a bainar jama'a."

Wata matashiya mai suna Isabel Nieto Tous, mai shekara 28, wadda ta koma zama tare da iyayenta shekara uku da suka gabata bayan ta dawo daga ƙasar waje, ta ce yin soyayya ba tare da samun isasshen keɓaɓɓen wuri ba na iya zama abin kunya.

Ta ce, "Ba na son in gaya wa iyayena cewa zan kwana a gidan wasu mutane, saboda abin yana da ɗan wahala. Saboda haka sai in ce zan kwana ne a gidan wata ƙawa ta."

Tous, wadda ta taɓa zama a Japan da Faransa da Jamus da Tunisia, ta yi imanin cewa yadda mutane ke fara soyayya a Sifaniya ya bambanta da sauran wurare.

Ta ce akwai wani irin kusanci da ɗumamar mu'amala da ke fara bayyana tun daga farkon haɗuwa.

A cewarta, "Mutane kan saba da juna cikin sauri kuma su fara nuna kusanci ba tare da ɓata lokaci ba. Wataƙila kun haɗu sau biyu kacal, amma tuni kuna riƙe hannun juna a bainar jama'a kuma kuna nuna kusanci sosai."

A cewar malamar ilimin zamantakewa Amparo Lasén, al'ummar Sifaniya ba sa ganin akwai wani babban abu tsakanin yadda ake nuna soyayya a gida da kuma a bainar jama'a. Saboda haka, sumbata ko sauran nau'o'in nuna kusanci abu ne da mutane da yawa ke yi ba tare da jin kunyarsa ba.

Sai dai wannan ba koyaushe haka yake ba. A lokacin mulkin kama-karya na Francisco Franco daga 1939 zuwa 1975, dokoki da ƙa'idojin addini masu tsauri sun takaita yadda mutane ke bayyana soyayya ko sha'awar juna a fili. Har ma akwai lokacin da ake kama mutane ko tarar su saboda sumbata a bainar jama'a, yayin da aka haramta luwadi.

Bayan mutuwar Franco a 1975, ƙasar ta shiga wani sabon zamani na sauye-sauyen al'adu.

Ga Paula Furió, wadda ta taɓa aikin ɗaukar hotunan bukukuwan aure a Valencia, ta ce yawan sumbata a bainar jama'a alama ce ta wani abu mafi girma a cikin al'ummar Sifaniya.

Ta ce duk da cewa har yanzu akwai ƙalubalen da ake fuskanta, sumbata wata alama ce da ke nuna irin 'yancin da mutane ke da shi na bayyana kansu da yadda suke ji.