Me ya sa Ghana ta janye dokar haramta auren jinsi?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Majalisar dokokin Ghana na shirin sake yin duba tare da soke amincewar da ta yi wa dokar da ta jawo cece-kuce kan masu auren jinsi (LGBTQ), wadda ta amince da ita a watan Mayun bana.

Kakakin majalisar, Alban Bagbin, ya ce an samu kura-kurai a tsarin da aka bi wajen amincewa da dokar, wanda hakan ya sa aka samu matsala game da sahihancin matakin.

Da yake jawabi a zauren majalisar a ranar 10 ga Nuwamba, Bagbin ya kuma bayyana cewa yadda aka amince da dokar bai nuna cikakkiyar goyon bayan jam'iyyu daban-daban ba, duk da cewa ana sa ran dokar za ta samu goyon bayan ɓangarorin biyu na siyasa.

Idan za a iya tunawa, a ranar 29 ga Mayu, majalisar ta yi wasu gyare-gyare ga wasu sassan dokar da ta amince da ita, duk da korafe-korafen da wasu 'yan majalisar adawa suka gabatar kan tsarin da aka bi wajen gudanar da aikin.

'Yan majalisar jam'iyyar New Patriotic Party (NPP) sun yi zargin cewa a lokacin da aka amince da dokar, adadin 'yan majalisar da ke zauren bai kai adadin da kundin tsarin mulki ya tanada domin gudanar da irin wannan zama ba.

Sun kuma zargi ɓangaren masu rinjaye na jam'iyyar NDC da sauya ainihin manufar dokar, tare da sassauta wasu daga cikin tanade-tanadenta.

Dan majalisa mai wakiltar Manhyia South, Nana Agyei Baffour, ya ce ɓangaren masu rinjaye bai shirya amincewa da dokar a ranar 29 ga Mayu ba, sai dai ya gaggauta gudanar da aikin ne bayan da ya samu labarin cewa masu ɗaukar nauyin kudirin na shirin gudanar da taron manema labarai domin nuna rashin amincewarsu da sauye-sauyen da aka yi wa dokar.

Ya ƙara da cewa an amince da dokar ne ba tare da cikar adadin 'yan majalisar da doka ta tanada ba, lamarin da ya bayyana a matsayin ƙarya kundin tsarin mulki.

A cewarsa, 'yan majalisar da ke zauren a ranar ba su kai 50 ba, lokacin da aka yi gaggawar amincewa da dokar.

Sauye-sauyen da aka yi wa kudirin dokar

A kudirin dokar na farko da majalisar Ghana ta amince da shi a watan Fabrairun 2024, duk wanda aka samu yana tallatawa, bayar da goyon baya ko kuma yaɗa manufofin ƙungiyoyin LGBTQ, zai iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekara biyar a gidan yari, ko kuma shekara 10 idan goyon bayan ya shafi yara.

Wannan tanadi ya shafi likitocin da ke taimaka wa mambobin ƙungiyoyin LGBTQ, 'yan jarida da ke bayar da rahotannin da suka shafe su, da sauran mutanen da ke amfani da kafafen yaɗa labarai wajen tattauna batutuwan da suka shafi ayyukansu.

Haka kuma, masu bincike da malaman jami'o'i da ke wallafa bincike kan ƙungiyoyin da ayyukansu za su iya fuskantar hukunci, kasancewar dokar farko ta ɗauki irin waɗannan ayyuka a matsayin goyon baya da ƙarfafa manufofin ƙungiyoyin.

Lauyoyi da sauran masu ba da shawarwari da ke gudanar da ayyukansu ga waɗannan ƙungiyoyi su ma za su iya zama masu laifi a karkashin tanadin dokar ta farko.

Sai dai a sabbin sauye-sauyen da aka yi wa kudirin, waɗannan mutane da suka haɗa da lauyoyi, 'yan jarida, likitoci, masu bincike, fastoci da masu ba da shawarwari, ba za a kama su da laifi ba idan suka ba da wata gudummawa ga ƴan LGBTQ.

Sai dai duk wanda ya ɗauki nauyin kuɗi ko kuma ya samar da kudaden tallata ayyukan kungiyoyin, zai ci gaba da aikata laifi, kuma zai iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekara biyar a gidan yari.

Duk da cewa 'yan majalisar adawa sun nuna rashin amincewarsu da sauye-sauyen da aka yi wa kudirin, majalisar ta amince da shi ta hanyar rinjayen kuri'u.

Da yake jawabi ga manema labarai a wajen zauren majalisar bayan amincewa da kudirin, Rabarane Ntim Fordjour, ɗaya daga cikin waɗanda suka ɗauki nauyin gabatar da kudirin, ya zargi gwamnatin NDC da sassauta dokar.

"Gwamnatin NDC ta yi amfani da rinjayenta a majalisa wajen sassauta kudirin dokar da muka fara gabatarwa. Yanzu ta amince da wata sabuwar doka wadda ba ta da tsauri kuma ba za ta yi wani tasiri mai karfi ba," in ji shi.

Dan majalisar ya ƙara da cewa manufar dokar ita ce daƙile goyon baya ga ƙungiyoyin LGBTQ. Saboda haka, cire laifin daga kan lauyoyi, likitoci, 'yan jarida, masu bincike da kuma sauran kwararru na nufin rage karfin dokar.

Ya kuma zargi 'yan majalisar da ke goyon bayan gwamnati da amincewa da dokar da aka yi wa gyare-gyare saboda muradun siyasa.

An mayar da kudirin dokar majalisa domin bin ka'idojin da suka dace

Dem go send am to di presidency make President John Mahama sign am into law.

For pipo from di LGBTQ community, weda dis fresh bill or di one dem pass for 2024, or di one dem go pass again afta di 'corrections', di value be di same.

Dem go kontinu to live in fear as dem dey do since tok-tok about di bill begin from 2024.

A ranar 2 ga Yuni na wannan shekara, Kakakin majalisar dokokin Ghana ya umarci 'yan majalisar da su sake duba kudirin dokar da suka amince da shi a ranar 29 ga Mayu.

Alban Bagbin ya ce duk da cewa kwamitin da ya nazarci kudirin ya gabatar da rahotonsa, inda ya bayyana cewa an cimma matsaya ɗaya tare da samun goyon bayan jam'iyyu daban-daban, abin da ya faru a zaman majalisar ranar 29 ga Mayu bai nuna irin wannan hadin kai ba.

Ya ce: "Irin wannan muhimmin kudirin doka ya kamata ya samu ingantaccen tushe, tare da goyon bayan 'yan majalisa daga dukkan ɓangarori. Haka kuma, dole ne a tabbatar da cewa an bi dukkan ka'idojin gudanar da ayyukan majalisa."

Kakakin majalisar ya ƙara da cewa idan kananan kura-kurai ne aka samu, ma'aikatan da ke kula da rubuta dokokin majalisa za su iya gyara su. Sai dai a wannan karon, ba za su iya yin hakan ba, saboda matsalar ta shafi shawarar da majalisar kanta ta amince da ita a ranar 29 ga Mayu.

Saboda haka, ya ce wajibi ne a mayar da kudirin gaban majalisa domin ta sake gudanar da aikin yadda ya kamata.

Bayan wannan sabon mataki, ana sa ran majalisar za ta sake duba kudirin daga matakin karatu na biyu.

Sai dai har yanzu ba a fayyace ko gyare-gyaren da aka yi wa kudirin a lokacin amincewa da shi a ranar 29 ga Mayu za su ci gaba da kasancewa ba, ko kuma majalisar za ta koma ga tanade-tanaden da ke cikin kudirin na farko, kamar yadda masu ɗaukar nauyinsa suka gabatar.

Idan majalisar ta sake amincewa da kudirin, wannan zai zama karo na uku da aka amince da irin wannan kudirin dokar da ta jawo cece-kuce kan 'yan LGBTQ a majalisar dokokin ƙasar.

Daga nan ne za a miƙa shi ga fadar shugaban ƙasa domin Shugaba John Mahama ya sanya wa kudurin hannu, don ya zama doka.

Sai dai ga mambobin LGBTQ, ko sabon kudirin ne, ko wanda aka amince da shi a shekarar 2024, ko kuma wanda majalisar za ta sake amincewa da shi bayan gyare-gyare, sakamakon bai bambanta ba.

A ganinsu, za su ci gaba da rayuwa cikin fargaba, kamar yadda suke yi tun bayan fara muhawara kan kudirin dokar a shekarar 2024.