Me ke janyo kwaɗayin dare bayan cin abinci?

    • Marubuci, Nick Triggle
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Correspondant santé
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Shin ka taɓa cin abinci ka ƙoshi sosai, amma bayan awa guda ko minti talatin sai ka fara jin kwaɗayin cin wani abu, har ka nufi kicin kana neman abin da za ka saka a baki?

Bincike ya nuna cewa mutum ɗaya daga cikin kowane mutum uku kan ci kayan ƙwalama bayan cin abincin dare. Haka kuma, huɗu daga cikin kowane mutane biyar masu shekaru tsakanin 18 zuwa 24 ba sa iya daina wannan ɗabi'a.

Dr. Kristine Beaulieu, ƙwararriya a fannin abinci mai gina jiki, ta ce wannan matsala ce da ke ci gaba da ƙaruwa. Ta bayyana cewa akwai alamun da ke nuna cewa mutanen da ke yawan cin kayan ƙwalama kafin kwanciya barci na iya kasancewa cikin haɗarin yin ƙiba ko tara tumbi.

To ko waɗanne irin abinci ne aka fi kwaɗayin ci da dare? Kuma wane mataki mutum zai iya ɗauka domin biyan wannan buƙata ta cin abinci ba tare da yin illa ga lafiyarsa ba?

Lokacin da yunwa ta fi ƙaruwa shi ne da dare

Ko da yake mutum kan shafe sa'o'i da dama ba tare da cin abinci ba yayin barci, bincike ya nuna cewa sha'awar cin abinci kan ƙaru da yamma ko da kuwa mutum ya ci abinci sosai da rana.

Farfesa James Betts na Jami'ar Bath, wanda ke bincike kan yadda jiki ke sarrafa abinci da kuzari, ya ce wani babban dalili shi ne yawan sinadarin ghrelin, wanda ake kira "hormone na yunwa", kan ƙaru ne a ƙarshen yini.

Ya ce, "Ko da yake cin abinci kan rage jin yunwa, hakan ya fi faruwa ne bayan cin abincin rana, ba lallai ba ne bayan cin abincin rana ko na dare."

Nau'in abincin da mutum ya ci ma na da muhimmanci. Abincin da ke ɗauke da sinadarin furotin da fibre, kan sa mutum ya daɗe ba tare da jin yunwa ba.

Farfesa Betts ya ce idan mutum bai ci abincin dare mai gina jiki da gamsarwa ba, hakan na iya janyo abin da ake kira "kwaɗayin dare", wanda mutane da dama kan ɗauka a matsayin abin ƙwalama.

Ga wasu kuma, tsoron farkawa da yunwa da daddare ne ke taka rawa.

Farfesa Suzanne Higgs, ƙwararriya kan sha'awar cin abinci a Jami'ar Birmingham, ta ce idan mutum ya saba cin abin ƙwalama a irin wannan lokaci, abubuwan da ke kewaye da shi na iya fara tayar masa da sha'awar abinci.

Ta ce, "Misali, idan mutum ya saba cin abin ƙwalama yayin kallon talabijin, kallon talabijin kaɗai na iya sa ya fara jin kamar yana son ci."

An fi kwaɗayin kayan zaki da dare

Ba wai jin yunwa kaɗai ne ke ƙaruwa da dare ba. Bincike ya nuna cewa sha'awar cin abinci masu sa kuzari sosai, wato masu yawan sinadarin kalori ma, sukan ƙaru a wannan lokaci. Masana sun ce hakan ya fi alaƙa da tsarin jin daɗi da ke cikin kwakwalwa, ba wai saboda jiki na buƙatar ƙarin kuzari ba.

Dr Kristine Beaulieu, wadda ke aiki tsakanin Jami'ar Leeds da Jami'ar Moncton ta Kanada, ta ce sha'awar abinci masu ɗauke da mai mai yawa kan fi ƙarfi da yamma idan aka kwatanta da farkon rana.

Ta ce: "Sha'awar irin waɗannan abinci na iya nuna alamun ƙoshi, ta yadda mutum zai ci abin ƙwalama ko kayan zaƙi duk da cewa ya riga ya ƙoshi."

Ko bayan cin isasshen abincin dare, abinci masu yawan sukari, mai ko gishiri kan ci gaba da motsa hanyoyin jin daɗi a cikin kwakwalwa. Wannan ne ke taimaka wa wajen bayyana dalilin da ya sa mutane da dama ke ci gaba da neman wani abin ci bayan sun gama cin abinci.

Saboda haka, idan ka tsinci kanka tsaye a gaban biskit da ƙarfe tara na dare, wataƙila ba gazawa ba ce. Tsarin halittar jikinka da yadda kwakwalwarka ke aiki na iya kasancewa abin da ke taka rawa wajen janyo maka wannan sha'awar.

Shin kayan zaƙi na hana barci da dare?

Amma abu ɗaya da ya bayyana shi ne cewa cin abinci da yawa a dare na iya shafar yadda jiki ke sarrafa abinci da kuma yadda mutum yake shirin shiga barci.

Amma idan aka duba nau'in abin da ake ci, akwai hujjojin da ke nuna cewa abincin da ke ɗauke da sinadarin carbohydrates da aka sarrafa sosai, da kuma waɗanda ke da yawan ƙarin sukari, kamar irinsu burodi da shinkafa ko biskit da kek, na iya haifar da rashin ingantaccen barci.

Masana na ganin hakan na faruwa ne saboda irin waɗannan abinci kan haddasa sauye-sauye masu yawa a aikin sukarin jini, sannan su sauya wasu sinadarai a jiki da ke taimaka wa wajen daidaita barci da kuma sha'awar cin abinci.

Sai dai babu tabbacin ko waɗannan abinci ne ke haddasa matsalar barcin kai tsaye.

Farfesa Jonathan Johnston, ƙwararre kan barci da motsa jiki a Jami'ar Surrey, ya ce rashin isasshen barci, yana ƙara kwaɗayin abinci masu ɗauke da kuzari mai yawa.

Saboda haka, a cewar Farfesa James Betts, yana da wuya a tabbatar da cewa abin ƙwalamar da aka ci da daddare ne kai tsaye ke haddasa matsalar rashin barci.

Ya ce, "A halin yanzu, hujjojin da ake da su ba su fito fili sosai ba, kuma mutane na amsawa ta hanyoyi daban-daban."

Yaya za a ci kayan ƙwalama yadda ya dace?

Da farko, yana da muhimmanci mutum ya fahimci abin da ke sa shi jin buƙatar cin abin ƙwalama da dare.

  • Idan yunwa ce, mutum zai iya a tabbatar da cewa ya ci abinci tun da wuri, kuma ya kasance mai gina jiki.
  • Idan cin abin ƙwalama ya zama jiki a gare ka, sauya jadawalin cin abinci da kuma shirya abin da za ka ci tun da wuri.

Ta ce, "Cin abinci yayin da mutum ke shagaltuwa da wani abu, kamar kallon talabijin, na iya sa ya ci fiye da yadda ya kamata saboda ba ya mai da hankali kan adadin abin da ya ci."

Sai dai Dr. Kristine Beaulieu ta ce;

  • Cin ɗan abin ƙwalama a gwargwadon kima.
  • Mutum ya fi cin abinci masu amfani kamar hatsi, kayayyakin madara da sauran sinadarai masu gina jiki.
  • Mutum ya ci cakuleti lokaci zuwa lokaci ba matsala ba ce.

"Abu ne da aka saba da shi, idan mutum ya riƙa cin irin waɗannan kayan zaƙi a wasu lokuta," in ji ta.

A cewarta, abin da ya kamata a fi mayar da hankali a kai shi ne cin abinci masu amfani ga lafiya.