Me ya sa ƴan cirani ke ci gaba da yunƙurin ratsa teku duk da hatsarin hakan?

    • Marubuci, Mamadou Faye
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Afrique
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Duk da yawaitar kifewar jiragen ruwa da asarar rayuka da ke jefa mutane cikin haɗari da iyalai cikin jimami, da kuma wayar da kai da hana yin ƙaura ba bisa ƙa'ida ba, ana ci gaba da samun ƙaruwar masu yunƙurin zuwa Turai ta teku.

Matasa 'yan Senegal na ci gaba da hawa ƙananan kwale-kwale tsofaffi da yawa domin ketare teku zuwa Turai.

Matsin tattalin arziki, rashin damar samun ci gaba a rayuwa, da kuma burin samun rayuwa mai kyau na daga cikin dalilan da ke ƙarfafa waɗannan tafiye-tafiye. Amma me ya sa duk da haɗarin rasa rai a teku ba ya hana su ci gaba da yin wannan yunƙuri?

Daga Niodior da ke tsibiran Saloum, da Saint-Louis, Kayar, Mbour, Joal, Tandji a Gambiya, Kafountine a yankin Casamance, da tsibiran Bidjogou na Guinea-Bissau, da sauran yankunan bakin teku, matasa daga mabambantan yankuna na barin Senegal domin neman kyakkyawar makoma a Turai.

A baya-bayan nan, an samun rahotannin kifewar kwale-kwale da ke ɗauke da 'yan cirani daga Senegal a hanyarsu ta zuwa Turai, inda mutane da dama suka rasa rayukansu.

Duk da irin waɗannan haɗurra da asarar rayuka, matasa da yawa na ci gaba da ɗaukar wannan kasada domin neman rayuwa mai kyau a ƙasashen Turai.

Duk da cewa an samu raguwar yawan masu wannan tafiya, akalla 'yan Senegal 4,918 ne suka isa tsibirin Canary Islands a shekarar 2025, idan aka kwatanta da 9,554 a shekarar 2024, wanda ke nuna raguwar kashi 48.5 cikin ɗari, a cewar Kwamitin Yaƙi da Hijira Ba Bisa Ƙa'ida ba (CILMI) da aka kafa a 2024.

Me ya sa kifewar kwale-kwale ba ya hana mutane ci gaba da yunƙurin ƙaura ta teku?

Duk da yawan kifewar kwale-kwale da asarar rayuka da ake samu, har yanzu ana samun ƙaruwar masu sha'awar yin ƙaura ta teku zuwa Turai.

Bayan kifewar wani kwale-kwale da ke ɗauke da 'yan cirani a ranar 8 ga Satumbar 2024 a gabar tekun Mbour, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 35 ciki har da mata da yara, Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya yi alƙawarin gudanar da abin da ya kira "farauta ba tare da sassauci ba" kan masu fasa ƙaurin mutane.

Ko da yake tun daga lokacin an kama mutane da dama, an gurfanar da su a gaban kotu tare da yanke musu hukunci, har yanzu akwai waɗanda ke ci gaba da yunƙurin zuwa cirani ba bisa ƙa'ida ba.

Duk da matakan sa ido da hukumomi suka ƙarfafa, matasa da yawa na nan daram kan aniyarsu ta barin ƙasar ko ta halin ƙaƙa.

A watan Oktoba, sashen yaɗa labarai na rundunar ƴansandan Senegal ya sanar da kama fiye da mutum 300 da ake zargi da yunƙurin yin hijira ba bisa ƙa'ida ba, tare da kwace kayayyaki masu yawa a tsibiran Saloum.

Shin matsin tattalin arziki ne babban dalilin da ke sa matasa zuwa cirani?

Ga mutane da dama a garuruwan masunta na Senegal, matsin tattalin arziki na daga cikin manyan abubuwan da ke tura matasa zuwa yin ƙaura ta teku, duk da haɗarin da ke tattare da hakan.

Maguèye Mbaye, wani mai sayar da kifi mai shekara 46 a garin Kayar, ya ce ya fahimci dalilin da ke sa matasa ɗaukar wannan haɗari domin shi ma ya yi irin wannan tafiya a shekarar 2006, inda ya samu isa Spain yana da shekara 26.

Sai dai ya ce yanzu ba zai sake gwada irin wannan tafiya ba saboda nauyin iyali da ke kansa. A cewarsa, yana cikin waɗanda gwamnatin Senegal ta taimaka wajen dawo da su gida, duk da cewa ya ce tallafin da aka ce za a ba su bai kai gare su ba.

Mbaye ya ce ƙarancin kuɗaɗen da ake samu daga sana'ar kamun kifi da rashin tabbas a samun kuɗin shiga na sa matasa da yawa neman mafita a ƙasashen waje.

"Wani lokaci akan shafe watanni tara kuɗin da na samu a kamun kifi, amma a ƙarshe ma'aikatan jirgin ruwa su karɓi CFA franc 200,000 kacal. Wasu ma ba sa samun komai," in ji shi.

A cewarsa, matasa masunta ba kansu kaɗai suke kula da rayuwarsu ba, su ne kuma ginshiƙin tattalin arzikin iyalansu.

Ya ce a wasu gidaje, kuɗin da ake kashewa a kullum kan kai tsakanin CFA franc 5,000 zuwa 7,000, kuma iyalai kan dogara ne da abin da ɗansu mai kamun kifi zai kawo domin su rayu.

"Yana da wahala a hana su tafiya"

Mbaye ya ce yawan matasan da ke ficewa daga ƙasar abin damuwa ne, amma matsalar ita ce babu sauƙin magance matsin tattalin arzikin da suke ciki.

"A yau yana da wahala, idan ba ma a ce ba zai yiwu ba, a hana su tafiya. A mafi yawan lokuta ma iyayensu ba sa sanin shirinsu na yin ƙaura."

A bakin teku da kuma ƙarƙashin bishiyoyi a yankunan da ke kusa da tekun Atlantika, ana iya ganin daruruwan mutane suna jiran lokacin da ya dace su hau kwale-kwale domin ƙetare teku zuwa Turai.

Masana na cewa wannan na nuna cewa ko da yake haɗarin mutuwa a teku da matakan tsaro suna ƙaruwa, talauci, rashin aikin yi da kuma bege na samun rayuwa mafi kyau na ci gaba da zama manyan abubuwan da ke ƙarfafa matasa su ɗauki wannan haɗari.

Me ya sa matakan da ake ɗauka ba sa tasiri?

Duk da wayar da kai da ake yi kan haɗarin ƙaura ba bisa ƙa'ida ba, tare da goyon bayan ƙungiyoyin matasa da mata, ana tsammanin yawan masu yin wannan tafiya zai ragu. Sai dai hakan bai faru ba. Matsalar ta fi ƙamari fiye da yadda ake gani a zahiri.

Maguèye Mbaye ya ce: "A wasu lokuta matasan da ke Turai suna bayyana wa abokansu a gida cewa abin da suke samu cikin watanni biyu ya fi abin da suka samu a tsawon watanni tara na kamun kifi lokacin da suke Senegal. Wannan na daga cikin manyan abubuwan da ke ingiza matasa yin ƙaura."

Ya ƙara da cewa: "Idan ka ga matasan da suka bar nan a 2023 sun dawo daga Sifaniya suna rabon kuɗi CFA 5,000 ko 10,000 ga 'yan uwa da abokai, suna yin aure kuma suna gina gidaje, za ka fahimci dalilin da ya sa wasu ke son tafiya su ma domin su samu irin wannan nasarar."

Ko da yake hukumomi na tare kwale-kwale, suna ƙarfafa sintiri a teku tare da ƙaddamar da shirye-shiryen horaswa da tallafa wa matasa don samun sana'a, har yanzu da dama na ganin cewa nasara a rayuwa ba za ta samu ba sai a Turai.

Ɗan ƙungiyar masu sana'ar kamun kifi, Amsatou Ndiaye, ya ce: "Yawan matasan da ke fita yanzu ya zarce na shekarar 2006, har ma da abin da aka gani cikin shekaru uku da suka gabata, domin babban dalilin da ke sa matasa barin ƙasar shi ne rashin fata game da makomarsu."

Mene ne ya kamata a yi domin magance matsalar?

A cewar Boubacar Sèye, shugaban ƙungiyar Horizons Without Borders, ranar zaman makoki ta ƙasa saboda mace-macen masu ƙaura bai kamata ta kasance wani lokacin jimami kawai ba, a'a ya kamata ta zama wani mataki na ɗaukar alhaki, saƙo mai ƙarfi da kuma mafarin haɗin kai na ƙasa kan batun ƙaura.

Mai binciken ya ce lokaci ya yi da za a wuce daga nuna alhini da fushi kawai zuwa samar da mafita mai ɗorewa ga matsalar.

Ya ba da shawarar a kira tarukan ƙasa kan ƙaura ta ƙasashen waje, waɗanda za su haɗa gwamnati, hukumomin ƙananan hukumomi, ƙungiyoyin farar hula, masana, masu bincike, iyalan masu ƙaura da kuma abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa.

A ganinsa, irin waɗannan taruka ya kamata su kai ga kafa wata hukuma mai zaman kanta ta ƙasa mai kula da harkokin ƙaura, wadda za ta tantance muhimman wuraren da ake buƙatar ɗaukar mataki kafin da bayan tafiyar ƙaura.

Ya ce aikin wannan hukuma zai kasance nazarin tushen matsalolin da ke sa mutane barin ƙasarsu, gabatar da hanyoyin magance su, ƙarfafa wayar da kan al'umma, da kuma sauya wasu al'adu da tunanin da ke ƙarfafa ƙaura ba bisa ƙa'ida ba.

Daga cikin abubuwan da ya ce ya kamata a mayar da hankali a kansu akwai matsin lambar al'umma da ke danganta nasara da tarin dukiya da kuma yadda wasu ke ɗaukar tafiya zuwa Turai a matsayin hanya mafi sauƙi ta samun nasara.

Sèye ya kuma ce wannan hukuma za ta yi aiki kan kare haƙƙin masu ƙaura, tallafa wa iyalansu da kuma taimaka wa waɗanda suka dawo gida su sake shiga cikin rayuwar al'umma.

A cewarsa, matsalar ba ta tsaya kawai kan hana mutane yin tafiya ba, sai dai fahimtar dalilin da ya sa matasa da yawa ke kallon ƙaura a matsayin wata mafita da ba za su iya kauce wa ita ba.