KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 8/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Lahadi 8 ga watan Nuwamban 2026.

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. Ruwan sama ya mamaye tantinan 'yan gudun hijira a Gaza

    Ruwa

    Ruwan sama mai ƙarfi ya mamaye dubban tantuna da mutanen da suka rasa matsugunansu ke zaune a cikinsu a Gaza, yayin da wani jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce kusan kowa da kowa a yankin na buƙatar agaji.

    Mazauna yankin sun yi amfani da tukwane da kwanoni wajen kwashe ruwa daga tantunansu da ambaliyar ruwa ta mamaye, inda wasu suka ce yanzu ba su da wani matsuguni.

    Jonathan Veitch, wakilin UNICEF a Falasɗinu, ya ce halin “matsanancin ƙunci” da ake ciki yana ƙara taɓarɓarewa sakamakon takunkumin da Isra’ila ta sanya kan shigar da manyan injuna da kayayyaki kamar man injina.

    Kusan kashi 90 cikin 100 na mazauna Gaza sun rasa matsugunansu sakamakon yaƙin Isra’ila da Hamas, kuma da yawa daga cikinsu sun yi ƙaura sau da dama, tare da ƙarancin samun tsaftataccen ruwa da hanyoyin tsaftar muhalli.

    Ƙungiyoyin agaji sun ce ana sa ran lamarin zai ƙara muni da zarar damina da sauka.

    Da yake zantawa da BBC daga Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza, Veitch ya ce: “Abin yana da matuƙar muni kuma mutane sun shiga matsanancin hali.

    “Muna ba da duk irin taimakon da za mu iya, amma a yanzu ma ana tare mu a kan hanya yayin da muke tafiya saboda mutane suna roƙon mu da mu taimaka musu.”

    Gwamnatin Gaza da Hamas ke jagoranta ta ce kusan tantuna 70,000 ne ambaliyar ruwa ta shafa.

    Wani mai magana da yawunta ya ce “rushewar daruruwan bango da rufin gidaje da suka riga suka tsage” ya jawo raunuka ga mutane, wasu daga cikinsu masu tsanani ne.

    Veitch ya kuma ce an samu ƙarancin kwalta masu hana ruwa, robobin rufewa da kuma tantuna a Zirin Gaza sakamakon rage kasafin kuɗin Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Yara

    Ya ce: “Dole ne mu kasance masu zaɓin wuraren da za mu mayar da hankali wajen ba da tallafi.

    “Amma abin takaici, ambaliyar ruwan da aka gani da safiyar yau na nufin kusan kowa da kowa yana buƙatar taimako.”

    Isra’ila ta ce tana takaita shigar da wasu kayayyaki zuwa Gaza ne saboda ana iya amfani da su wajen ayyukan soja.

    Maryam Odeh mai shekara 34, wadda ke zaune tare da ‘ya’yanta a Deir al-Balah, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa:

    “Ba mu ƙara sanin yadda za mu kare ‘ya’yanmu ba.

    “‘Ya’yana suna tambayata inda za mu kwana yau da dare, amma ba ni da amsa.”

    Khaled al-Najjar mai shekara 41 ya kuma shaida wa AFP cewa:

    “Muna fargabar abin da zai samu ‘ya’yanmu ba kawai saboda ambaliyar ruwa da ta mamaye tantuna ba, har ma saboda sanyi da kuma yawaitar cututtuka.”

  2. Harin Saudiyya ya kashe mutum 33 - Houthi

    Yaro

    Kafofin yaɗa labarai masu alaƙa da ƙungiyar Houthi a Yemen sun ce aƙalla mutane 33 ne suka mutu, ciki har da mata da yara, sakamakon hare-haren sama da Saudiyya ta kai.

    Har yanzu ƙawancen sojin da Saudiyya ke jagoranta, wanda ke mara wa gwamnatin Yemen da duniya ta amince da ita baya, bai fitar da wata sanarwa ba game da lamarin.

    Hotunan bidiyo kai tsaye da tashar talabijin ta Al Masirah, wadda Houthis ke gudanarwa, ta nuna masu ceto suna tono gawawwaki daga ƙarƙashin baraguzan gine-gine da dama a garin al-Shariyah da ke gabashin babban birnin ƙasar, Sanaa.

    An kuma ga gawarwakin ƙananan yara cikin mutanen da aka ciro daga cikin baraguzan.

    Tashar talabijin ɗin ta kuma nuna wasu da suka jikkata ana ɗaukarsu kan gadon marasa lafiya zuwa asibiti.

    Kamfanin dillancin labarai na Saba, wanda shi ma Houthis ke gudanarwa, ya ce Saudiyya ce ta kai harin a ranar Asabar. Ya ƙara da cewa mutane 39 sun jikkata.

    Saudiyya na jagorantar ƙawancen soja da ke yaƙi da Houthis fiye da shekara goma domin tallafa wa gwamnatin Yemen da ƙasashen duniya suka amince da ita.

    Yaƙin Yemen ya yi sanyi na wasu shekaru, amma ya sake rikiɗewa sakamakon yaƙin Iran.

    Tsagaita wutar da ake yi ta fara rushewa ne bayan Saudiyya ta kai hari filin jirgin saman Sanaa, wanda Houthis ke iko da shi, domin hana wani jirgin Iran sauka a wurin.

    Daga baya Houthis da ke samun goyon bayan Tehran suka kai hari filin jirgin saman Abha a Saudiyya, sannan suka fara kai hare-hare kan jiragen ruwa na Saudiyya da ke amfani da Tekun Maliya a gabashin Yemen a matsayin wata hanyar fitar da mai maimakon mashigin Hormuz.da aka kai a Yemen.

  3. Barka da hantsi!

    Barka da shigowa shafin labaranmu BBC Hausa kai-tsaye, inda muke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ƙasashe maƙwafta da kuma sauran sassan duniya.

    Kada ku manta ku je shafukanmun na Facebook, X, Instagram da YouTube domin yin tsokaci kan labaran da muke kawo muku da kuma kallon bidiyo masu ƙayatarwa.

    Ku shiga zurenmu na WhatsApp domin samun labarai da ɗumi-ɗumi sannan ku sauke manhajar BBC Hausa.