Fa'az: Sabon makami mai linzami na zamani da Pakistan ta ƙera

Asalin hoton, ISPR
A yaƙin sama na zamani, ba a auna ƙarfin jiragen yaƙi da ingancin na'urorin radar, saurinsu ko ƙwarewarsu ta tashi kaɗai ba. Ana kuma la'akari da nisan da za su iya gano jiragen abokan gaba da kuma irin makaman da za su iya amfani da su wajen kai musu hari.
A baya-bayan nan, Pakistan ta yi nasarar gwajin wani makamin linzami mai suna Fa'az, wanda sojojin ƙasar suka bayyana a matsayin na farko irinsa da aka ƙera a cikin gida.
A cewar hukumar hulɗa da jama'a ta rundunar sojin Pakistan (ISPR), wannan makami shi ne na farko da aka ƙera gaba ɗaya a cikin ƙasar.
An ƙera makamin ne da tsarin zamani na jagorantar sa a matakin ƙarshe na tafiyarsa, kuma yana da ƙarfin kai hari kan abubuwan da ke shawagi a sararin samaniya daga nesa.
Sojojin Pakistan sun ce ƙera wannan makami ya nuna ƙwarewar fasaha, ƙirƙire-ƙirƙire da kuma dogaro da kai da masana'antar kera makaman tsaron ƙasar ta samu.
Duk da cewa har yanzu ba a bayyana cikakkun bayanai kan fasaharsa da ƙarfin aikinsa ba, ana kallon ƙera shi a matsayin wani muhimmin mataki ga Pakistan wajen samar da makamai na zamani da fasahohin da suka shafi jiragen yaƙi a cikin gida.
Sai dai, waɗanne irin ƙwarewar fasaha ne makamin Fa'az yake da su? Shin zai iya bai wa rundunar sojin saman Pakistan wata sabuwar damar yaƙi idan aka kwatanta da makaman da take da su a yanzu?
Wace rawa zai iya takawa a fafatawar ƙarfin sojin sama tsakanin Pakistan da Indiya? Kuma mene ne muhimmancin ƙera wannan makami ga ƙoƙarin Pakistan na dogaro da kanta wajen kera makaman tsaro?
Wace fasaha ce aka yi amfani da ita wajen ƙere makamin Fa'az?

Asalin hoton, ISPR
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cewar Bilal Khan, wanda ya kafa kuma manazarci a dandalin sharhi kan harkokin tsaro na Quwa da ke birnin Toronto, makamin linzami na Fa'az wani nau'in makami ne mai dogon zango da ake amfani da shi wajen kai hari kan jiragen sama daga nesa (BVR).
Wannan na nufin makamin na iya kai hari kan abubuwan da ke shawagi a sararin samaniya, ko da kuwa sun wuce inda matukin jirgin zai iya ganinsu kai tsaye.
Da yake magana da BBC News Urdu, ya ce: "Akwai nau'o'i biyu na asali: na farko yana amfani da na'urar gano hoton zafin abu ta hanyar hasken infrared (IIR), yayin da na biyun ke amfani da tsarin radar mai gano manufa da kansa (ARH)."
Cibiyar kera makaman jiragen sama ta Pakistan (AWC) ta bayyana cewa makamin yana da zangon kai hari na kusan kilomita 100. Sai dai har yanzu ba a tabbatar ko wannan zangon ya shafi dukkan nau'o'in makamin ba.
A cewar Bilal Khan, gwajin da aka gudanar a ranar 3 ga Nuwamba ya yi amfani da wani nau'in Fa'az da ke amfani da na'urar gano hoton zafi ta infrared.
Da wannan tsarin, makamin ba wai kawai yana gano zafin da abin da yake hari ke fitarwa ba ne, har ma yana ƙirƙirar hoton zafin wannan abin.
A cewarsa, hakan yana rage yiwuwar makamin ya rikice ya bi dabarun karkatar da makamai daga kan jirgin da ake hari, kamar amfani da tarkunan harshen wuta (flares) da jiragen yaƙi ke fitarwa, idan aka kwatanta da makaman infrared na gargajiya.
Bilal Khan ya ce rundunar sojin saman Pakistan ta ƙiyasta cewa wannan na'urar infrared na iya gano abin da ake hari daga nisan kilomita 40 zuwa 45.
Idan aka harba makamin, radar ɗin jirgin da ya harba shi ne zai fara jagorantar sa zuwa inda abin da ake hari yake. Da zarar makamin ya kusanci abin da ake hari zuwa nisan kusan kilomita 40, na'urorin infrared ɗinsa za su fara aiki, inda za su karɓi ragamar gano abin da ake hari da kuma bin diddiginsa.
Wani nau'in na biyu na makamin Fa'az kuma na iya amfani da na'urar radar mai gano manufa da kanta (ARH).
Bilal Khan ya bayyana cewa wannan tsarin ainihin ƙaramin radar ne da aka sanya a cikin makamin. Irin wannan makami ma radar ɗin jirgin yaƙi ne ke fara jagorantar sa, amma da zarar ya kusanci abin da ake hari zuwa nisan kilomita 20 zuwa 25, na'urorin radar ɗinsa za su fara aiki domin gano abin da ake hari da kuma kulle shi a matsayin manufa.
A nasa ɓangaren, Hammad Walid, wani mai binciken makamai a Cibiyar Nazarin Dabarun Tsaro ta Strategic Vision Institute, yana ganin ya kamata a ɗauki Fa'az a matsayin jerin makamai masu linzami iri-iri, maimakon makami guda ɗaya.
Ya ce ana haɓaka waɗannan nau'o'in ne domin biyan buƙatun kai hari kan manufofi daban-daban da kuma yanayin yaƙi.
Da yake magana da BBC News Urdu, Hammad ya ce kamfanin Global Industrial and Defense Solutions (GIDS) ya riga ya gabatar da nau'o'in makamin da ke amfani da na'urorin radar da infrared, waɗanda ake cewa suna da zangon kai hari tsakanin kilomita 70 zuwa 100.
Sai dai ya ƙara da cewa ana sa ran nau'in da zai biyo baya, wato Phase-II, zai iya kaiwa nisan kilomita 180 ko fiye da haka.
Muhimmancin makamin Fa'az ga rundunar sojin saman Pakistan

Asalin hoton, ISPR
Domin fahimtar muhimmancin makamin Fa'az, yana da kyau a fara duba jiragen yaƙi da makaman linzami masu kai hari kan jiragen sama da rundunar sojin saman Pakistan ke amfani da su a yanzu, da kuma sauye-sauyen da ake sa ran za ta yi wa jiragenta a nan gaba.
Jiragen yaƙin F-16 na rundunar sojin saman Pakistan suna amfani da makaman linzami na AIM-120 da Amurka ta ƙera, yayin da jiragen JF-17 da J-10 ke amfani da makaman linzami na jerin PL da China ta ƙera.
Hammad Waleed ya ce makamin PL-15E na daga cikin manyan makaman linzami masu dogon zango da Pakistan ke da su. Baya ga haka, wasu jiragen yaƙin rundunar suna ɗauke da makaman AIM-9 Sidewinder, waɗanda ake amfani da su wajen kai hari daga gajeren zango.
A cewar Bilal Khan, ƙera makamin Fa'az na iya ƙara wa rundunar sojin saman Pakistan sassaucin amfani da makamanta, domin rundunar za ta samu ƙarin iko wajen zaɓar makaman da za a girka a jiragen yaƙinta.
Ya ce Pakistan na gudanar da wani shiri na zamanantar da jiragen yaƙinta na JF-17, wanda ya haɗa da ƙera sabon na'urar radar a ƙarƙashin shirin National Aerospace Science and Technology Project (NASTP).
A cewarsa, domin cin gajiyar wannan radar ta zamani, ana buƙatar makaman linzami da za su iya aiki da ita.
Bilal Khan ya ce a baya an yi la'akari da amfani da radar Grifo-E, wadda kamfanonin Italiya da Birtaniya suka ƙera, wajen girka ta a jiragen JF-17 Block 3. Wannan radar na amfani da fasahar gallium nitride (GaN).
Sai dai ya ce saboda Pakistan ba ta da cikakken damar samun bayanan asali na shirin ƙera radar da sauran muhimman bayanan fasaha da ake buƙata domin daidaita makaman linzami na China da ita, sai aka yi amfani da radar KLJ-7A ta China, wadda ke aiki da fasahar gallium arsenide (GaAs).
Hammad Waleed ya ce tsofaffin nau'o'in jiragen JF-17 Block One da Block Two suna da wasu matsaloli da suka shafi nauyin makaman da za su iya ɗauka, ƙarfin radar da kuma aikin injinansu.
Sai dai an inganta jiragen JF-17 Block Three ta hanyar sanya musu radar ta zamani mai amfani da fasahar AESA da kuma ingantattun na'urorin lantarki, lamarin da ya ba su damar amfani da manyan makaman zamani.
A cewarsa, yayin da ake ritayar tsofaffin jiragen yaƙi na F-7 da Mirage, tare da ƙara sabbin jiragen JF-17 da J-10C, akwai yiwuwar jiragen JF-17 su zama muhimmin ɓangare na rundunar sojin saman Pakistan a nan gaba.
Bilal Khan ya ce nau'in makamin Fa'az da ake da shi a yanzu bai kai makamin PL-15 na China ƙarfi ba. Sai dai muhimmancinsa yana cikin ilimi da fasahar da Pakistan ta samu yayin ƙera shi.
A cewarsa, fasahar injin roka da za a yi amfani da ita wajen ƙera Fa'az-II na iya taimakawa Pakistan a nan gaba wajen ƙera makaman linzami masu dogon zango, waɗanda za a iya amfani da su wajen kai hari kan jiragen sama ko kuma kare sararin samaniya daga hare-hare.
Sai dai sanarwar da hukumar hulɗa da jama'a ta rundunar sojin Pakistan (ISPR) ta fitar ba ta bayyana irin jiragen yaƙin da za su yi amfani da makamin Fa'az ba. Haka kuma, ba ta tabbatar da cewa an shigar da makamin a hukumance cikin jerin makaman rundunar sojin saman ƙasar ba.


























