Me sakamakon zaɓen Amurka ke nufi ga ƙasashen duniya?

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
Jam'iyyar Democrat ta samu nasarar lashe kujeru a majalisar dattawa da ta wakilai ta Amurka, inda ta karɓi ikon tafiyar da majalisar dokokin ƙasar har zuwa ƙarshen wa'adin shugabancin Donald Trump.
Wannan gagarumin sauyi a fagen siyasar Amurka ya zama babban koma-baya ga shugaban ƙasar. Trump ya amince cewa yaƙin Iran da kuma tashin farashin kayayyaki sun taimaka wajen janyo kayen da da dama daga cikin 'yan takarar jam'iyyar Republican suka sha.
Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, ya ce: "Yaƙin Iran ne dalilin da ya sa muka faɗi."
BBC ta yi bayanin abin da sakamakon zaɓen ke nufi ga sauran ƙasashen duniya, daga yaƙe-yaƙen Ukraine da Gabas ta Tsakiya zuwa alaƙar kasuwanci da China.
Iran

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Ghoncheh Habibiazad, wakilin BBC Persia
Jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya ce waɗanda ke ganin cewa sauyin da aka samu a siyasar Amurka zai kawo sauyi kan "ƙiyayyar Amurka ga Iran" sun yi babban kuskure.
Khamenei ya kuma yi barazanar cewa idan Amurka ta sake kai hari kan Iran, martanin ƙasar zai fi na baya muni matuƙa.
Ba a ga Mojtaba Khamenei wanda ya gaji mahaifinsa, Ali Khamenei, a matsayin jagoran addinin Iran bayan kashe shi a hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai wa ƙasar a ranar 28 ga Fabrairu a bainar jama'a ba tsawon watanni.
Ya bayyana hakan ne a cikin wata wasiƙa mai shafi shida da aka fitar ranar Laraba, wadda ta yi daidai da ranar tunawa da mamaye ofishin jakadancin Amurka da aka yi a birnin Tehran a shekarar 1979.
Ƙasashen Larabawa na Tekun Fasha

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Frank Gardner, wakilin BBC na ɓangaren tsaro
A bisa ƙa'ida, rashin nasarar da aka samu a zaɓen tsakiyar wa'adin shugabancin Amurka, wanda ya zama koma-baya ga shirin Trump a wasu lokuta zai iya zama koma-baya ga ƙasashen Larabawa na Tekun Fasha.
Hakan ya faru ne saboda shugaban Amurka da iyalinsa na da kusanci ta fuskar hulɗar kasuwanci da ta kashin kai da dama daga cikin waɗannan ƙasashe.
Akwai filin wasan golf mai suna Trump International Golf Course a Dubai. Ita kuwa Qatar ta ba shi kyautar jirgin sama da darajarsa ta kai dala miliyan 400, yayin da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Qatar da Saudiyya suka zuba jarin biliyoyin daloli a kamfanin Affinity Capital na Jared Kushner, surukin Donald Trump.
Haka kuma, Trump ya zaɓi birnin Riyadh a matsayin wurin da ya fara kai ziyara a ƙasashen waje a wa'adinsa na farko a shekarar 2017.
Musamman Saudiyya ta taɓa samun rashin jituwa mai tsanani da magabacinsa daga jam'iyyar Democrat, Joe Biden. A tuna yadda suka gaisa da Yariman Saudiyya a shekarar 2022, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.
Haka kuma, shugabannin ƙasashen Larabawa na Tekun Fasha sun nuna rashin gamsuwarsu da tsohon shugaban Amurka, Barack Obama, bayan ya ƙi ɗaukar mataki kan shugaban Syria, Bashar al-Assad, duk da amfani da makamai masu guba da ya yi.
Sai dai yaƙin Iran na bana ya sauya yadda mutane ke kallon Trump.
Kamar yadda wani mai sharhi kan al'amura ya bayyana, "Shugaba Trump ne ya haddasa rikicin da ta baibaye ƙasashen Tekun Fasha" a ranar 28 ga Fabrairu, kuma har yanzu akwai fargabar cewa zai iya sake tayar da yaƙin.
Hakan na iya sa Iran ta mayar da martani ta hanyar kai munanan hare-hare kan muhimman ababen more rayuwa na ƙasashen, waɗanda suke da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikinsu.

Asalin hoton, Getty Images
Tasirin yaƙin Iran kan sakamakon zaɓen
Rebecka Pieder, wakiliayr BBC a Washington DC
Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, ya ce yana ɗora alhakin gagarumin kayen da jam'iyyar Republican ta sha a zaɓen kan yaƙin da ake yi da Iran.
Yaƙin ya janyo tashin gwauron zabi a farashin kayayyaki ga Amurkawa, musamman man fetur a gidajen mai.
A lokacin yaƙin neman zaɓen wa'adinsa na biyu a shekarar 2024, Trump ya yi alƙawarin rage farashin galan ɗaya na man fetur zuwa ƙasa da dala biyu. Sai dai a watan Oktoba, matsakaicin farashin galan ɗaya ya kai dala 4.31.
Ya kuma yi alƙawarin cewa ba za a sake shiga wani sabon yaƙi ba idan ya koma Fadar White House.
Sai dai a ranar da ta gabaci zaɓen tsakiyar wa'adin, Amurka ta sake kai hare-hare kan wani tsibiri a Iran, kuma Trump ya shaida wa manema labarai cewa bai yi nadamar fara yaƙin ba.
Bayan sanar da sakamakon zaɓen, babban mai shiga tattaunawar Iran da Amurka ya ce Amurkawa sun bayyana matsayinsu ta hanyar cewa, "A'A ga yaƙi."
Sai dai jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa ba ya sa ran manufofin Amurka za su sauya sakamakon zaɓen.
A wata hira da CBS News, abokiyar hulɗar BBC a Amurka, Trump ya ce yaƙin zai ƙare ne "lokacin da na ce zai ƙare".
China

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Laura Bicker, wakiliyar BBC a China
Yayin da take samun labarin sakamakon zaɓen Amurka, China na iya ganin wata dama a cikinsa.
Dangantakar Beijing da Washington na ɗaya daga cikin manyan fafatawar ƙasashe masu ƙarfin iko a wannan ƙarni. Shugaban China, Xi Jinping, na iya ganin cewa yanzu yana da rinjaye a wannan fafatawa, yayin da yake shirin tarbar Donald Trump a China daga baya a wannan wata.
Trump ya kakabawa kayayyakin China haraji domin kare masana'antun Amurka daga kayayyakin China masu rahusa.
Sai dai shirin nasa bai haifar da sakamakon da ake so ba, domin Xi ya mayar da martani ta hanyar ƙaƙaba wa kayayyakin Amurka haraji mai tsoka.
Hakan ya sa farashin kayayyaki da dama ya ƙaru ga Amurkawa, ciki har da wasu ƙananan abubuwan jin daɗin rayuwa kamar kayan wasa da tufafi.
China ta kuma dakatar da sayen kayayyakin noma daga Amurka, lamarin da ya cutar da manoman da ke jihohin da ke goyon bayan Trump.
Wannan yaƙin cinikayya ya ƙare ne da yarjejeniyar tsagaita takaddama, wadda wa'adinta zai ƙare a ƙarshen watan Janairu.
China na iya ganin cewa Trump zai shiga tattaunawar neman sabuwar yarjejeniya ne bayan ya sha kaye a zaɓen tsakiyar wa'adin, kuma yana buƙatar cimma matsaya.
Xi zai iya ganin wannan a matsayin damar samun yarjejeniyar da za ta fi amfani ga China.
Russia

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Steve Rosenberg, shugaban BBC a sashen Russia
Mai magana da yawun shugaban Rasha, Vladimir Putin, Dmitry Peskov, ya shaida wa kafafen yaɗa labaran ƙasar cewa: "Muna fatan da gaske Donald Trump zai ci gaba da ƙoƙarinsa na samar da zaman lafiya."
Peskov ya ce akwai wasu dabaru da ake nazari a kai, kuma "nan ba da jimawa ba za a sake gudanar da wani zagaye na tattaunawar ɓangarori uku".
Yana magana ne kan shirin tattaunawar da ake sa ran Rasha, Ukraine da Amurka za su yi a Abu Dhabi a mako mai zuwa.
Ya kuma ƙara da cewa: "Mun ga nasarorin ƙoƙarin jinƙai da Melania Trump ta yi na samar da zaman lafiya." Yana nufin wani aikin jinƙai na baya-bayan nan da aka gudanar a Oleshky, yankin da Rasha ta mamaye a Ukraine.
Ya ce suna fatan duk waɗannan ƙoƙarin za su ci gaba.
Sai dai idan ƙoƙarin samar da zaman lafiyar bai yi nasara ba, akwai yiwuwar Moscow ta ɗora alhakin hakan kan Ukraine da ƙasashen Turai, kamar yadda ta saba yi a baya.
Haka kuma, tana iya fara ɗora alhakin hakan kan jam'iyyar Democrat da sakamakon zaɓen tsakiyar wa'adin Amurka.
Amma da wuya ta ɗora wa Donald Trump laifi, domin fadar Kremlin ta zuba jari sosai wajen gina kyakkyawar alaƙa da shi. Kuma a bayyane yake cewa Moscow na fatan bunƙasa haɗin gwiwar tattalin arziki da gwamnatin Trump.
Yadda kafafen yaɗa labaran duniya suka ɗauki sakamakon zaɓen

Asalin hoton, Tehran Times
BBC Monitoring
Ga al'ummar Ukraine da Iran da kuma ƙasashen Gabas ta Tsakiya, zaɓen tsakiyar wa'adin shugabancin Amurka ya fi shafar batun cikin gida, domin sun fi mayar da hankali kan abin da sakamakon zai iya haifarwa ga yaƙe-yaƙen da ake ci gaba da yi a yankunansu.
A Ukraine, masu sharhi sun fi mayar da hankali kan yadda Trump ke tafiyar da yaƙin ƙasar. Wani ɗan jarida, Roman Tsymbalyuk, ya yi tsokaci cewa shugaban ya "warware duk yaƙe-yaƙe amma ya kasa warware nasa", yana nufin ikirarin da Trump ya sha yi na cewa zai kawo ƙarshen rikice-rikice a duniya.
Yayin da Rasha ke ci gaba da kai hare-hare kan muhimman ababen more rayuwa na makamashi a Ukraine, wasu a Kyiv na fatan nasarar Democrat za ta ƙara ƙarfafa goyon bayan ƙaƙaba wa Moscow takunkumi mai tsauri.
Sai dai wasu na fargabar cewa rashin samun matsaya tsakanin jam'iyyun siyasa a Washington zai iya ƙara kawo rashin tabbas kan manufofin Amurka game da Ukraine.
A Moscow kuwa, fadar Kremlin ta bayyana fatan cewa Trump zai ci gaba da ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin, inda ake sa ran sake gudanar da tattaunawar Rasha da Ukraine a cikin wannan wata.
Sai dai wasu masu goyon bayan yaƙin a Rasha sun yi gargaɗin cewa ikon da Democrat za ta samu a majalisa zai iya takaita damar Trump na cimma wasu yarjejeniyoyi da fadar Kremlin a nan gaba, ko kuma sassauta takunkumin da aka ƙaƙabawa Rasha.
A gefe guda kuma, shugabannin Iran da kafafen yaɗa labaran da ke da alaƙa da gwamnatin ƙasar sun bayyana nasarar Democrat a matsayin alamar cewa Amurkawa sun nuna rashin amincewarsu da manufofin Trump na yaƙi.
Kafafen yaɗa labaran Iran sun kuma mayar da hankali kan yadda suka bayyana ƙarin tsadar siyasa da Amurka ke fuskanta sakamakon arangamar sojojinta da Iran.


























