Waɗanne abubuwa ne a cikin ɗakin Ka'abah?

.
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A duk lokacin da ake magana kan Makka da aikin Hajji, ɗakin Ka'aba ce ke zuwa zuciyar miliyoyin Musulmi a duniya. Ita ce alƙiblar da Musulmi ke fuskanta yayin gudanar da sallolinsu, kuma tana tsakiyar Masallacin Harami a birnin Makka na Saudiyya.

Duk da shahararta da kuma yadda miliyoyin mahajjata da masu Umara ke zagaye ta a kowace shekara, mutane da dama ba su san abubuwan da ke cikin wannan ɗaki mai tsarki ba.

Samun damar shiga cikin ɗakin Ka'aba ba abu ne da kowa ke samu ba, domin ana buɗe ta ne a wasu lokuta na musamman ga wasu jami'ai da manyan baƙi.

Ɗaya daga cikin mutanen da suka samu damar shiga cikinta shi ne Abdullahi Muktar, tsohon shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON).

Ya kuma bayyana wa BBC wasu daga cikin abubuwan da ya gani a lokacin da ya shiga ɗakin na Ka'aba.

Turaku uku

...

A cewar Abdullahi Mukhtar, ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi ɗaukar hankali a cikin Ka'aba su ne turaku uku da aka yi da katako waɗanda ke riƙe da saman ginin.

Ya ce "Ɗakin Ka'aba ɗaki ne wanda ni'imar da ke cikinsa ba ta misaltuwa. Amma cikin shi akwai turaku guda uku, waɗanda suke riƙe da saman ɗakin."

Ya ce turakun suna tsaye ne daga ƙasa zuwa sama, kuma su ne ginshiƙan da ke tallafa wa rufin ɗakin.

Ya ƙara da cewa duk wanda ya shiga Ka'aba zai lura da su, kasancewar suna daga cikin manyan abubuwan da ke cikin ɗakin.

Daɓen dutse mai ƙyalli

Wani abu da tsohon shugaban NAHCON ɗin ya ce ya tuna shi ne daɓen da ke cikin ɗakin.

Ya bayyana ta a matsayin "wani dutse mai santsi kuma mai ƙyalli, wanda launinsa ya haɗa fari da kuma ruwan toka."

A cewarsa, "shimfiɗar na ɗaukar ido saboda tsafta da kyawunta."

Wannan shimfiɗar ce ke rufe kusan ilahirin ƙasan ɗakin Ka'aba inda baƙi ke taka ƙafafunsu yayin shiga.

Koren ƙyalle mai ɗauke da rubutu

....

Abdullahi Mukhtar ya ce idan aka shiga cikin ɗakin Ka'aba, akwai wani koren ƙyalle na musamman da ke rufe wasu sassan bangon da saman ɗakin.

Ya ce "daga saman ɗakin akwai koren ƙyalle da aka kawata da rubuce-rubucen ayoyin Alƙur'ani.

Ya bayyana cewa ƙyallen ya sauko daga saman ɗakin, abin da ya sa ya kasance cikin abubuwan da suka fi ɗaukar hankalinsa.

"Rubuce-rubucen ayoyin Alƙur'ani da ke jikin ƙyallen na daga cikin abubuwan da suka fi jan hankalin masu shiga wurin," in ji shi.

Fitilun azurfa da zinare

Wani abu da tsohon shugaban hukumar alhazai ya ce ya gani a cikin Ka'aba shi ne fitilu da aka rataye daga saman ɗakin.

A cewarsa, waɗannan fitilu na musamman an ƙera su ne da azurfa da kuma zinare kuma suna cikin abubuwan da suka ƙawata cikin ginin.

Ya bayyana cewa fitilun suna rataye ne daga sama, abin da ke ƙara wa ɗakin kyawun gani.

Ƙamshi

...

Ba abubuwan da ido kawai yake iya gani ba ne suka burge Abdullahi Muktar a lokacin da ya shiga Ka'aba. Ya kuma bayyana yadda wani ƙamshin turare na musamman ya mamaye cikin ɗakin.

A cewarsa, ƙamshin turaren yana da ban mamaki, kuma yana da wahalar misalta shi da wani ƙamshi.

Ya ce: "Akwai kuma wani ƙamshin turare mai ban mamaki da ke fita a cikin ɗakin wanda ba ya misaltuwa."

Matakalar zuwa sama

"Wani abu da ba kasafai mutane ke sani ba shi ne cewa akwai wata matakala ta musamman a cikin Ka'aba da ake amfani da ita wajen hawa zuwa saman ginin." in ji Abdullahi Mukhtar.

Ya bayyana cewa "akwai wata ƴar hanya ko matakala da ke kaiwa zuwa ƙololuwar saman ɗakin, wanda ake danganta shi da wata ƙofa da ake kira Bab al-Tawbah.

Ainihin Bab al-Tawbah ƙofa ce da ke cikin Ka'aba, a kusurwar arewa maso gabas, wadda ke kai wa zuwa matakalar hawa saman ginin.

Wannan hanya na daga cikin sassan Ka'aba da ba kasafai jama'a ke gani ba.

Ya ake ji idan aka shiga ɗakin Ka'aba?

...
Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Baya ga abubuwan da ido zai iya gani a cikin ɗakin Ka'aba, akwai kuma wani yanayi na musamman da mutanen da suka samu damar shiga cikinta ke ji.

Abdullahi Muktar ya ce kalmomi ba za su iya bayyana yadda mutum yake ji idan ya shiga wannan ɗaki mai tsarki ba.

A cewarsa, duk yadda mutum ya yi ƙoƙarin bayyana abin da ya ji bayan fitowa daga cikin Ka'aba, zai iya tuna wasu abubuwa ne kawai, amma ainihin yanayin da zuciyarsa ta shiga abu ne da kalmomi ba za su iya isarwa ba.

Ya ce: "Harshe ba zai iya bayyana yadda ake ji ba idan an shiga ɗakin Ka'aba, sai dai mu ce Alhamdulillah. Amma duk yadda mutum ya iya maka bayanin yadda ya ji bayan ya fito daga ɗakin, to sai dai ya faɗi abubuwan da kawai zai iya tunawa. Amma zuciya ce kawai za ta iya hango yadda ta ji."

Duk da cewa mutane da yawa na son sanin abin da ke cikin ɗakin Ka'aba, waɗanda suka samu damar shiga cikinta sun ce abin da ya fi ɗaukar hankali ba turakanta ba ne, ko fitilunta, ko ƙamshin turarenta amma yanayin nutsuwa da tsarkin zuciya da mutum ke ji ne ya fi tsaya masa a rai.