Zaɓi biyu da suka rage wa Atiku bayan soke takararsa

Atiku Abubakar
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

A ranar Alhamis ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke taƙarar Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC.

A hukuncin da mai shari'a Peter Lifu ya yanke, kotun ta ce kwamitin riƙon ƙwarya na ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata Mark, wanda ya shirya zaɓen fitar da gwani da ya haifar da Atiku a matsayin ɗan takara ADC, a matsayin haramtaccen kwamiti ne.

Hon Nafiu Bala Gombe ne dai ya shigar da ƙara a gaban kotun yana ƙalubalantar hanyar da David Marka ya zama shugaban riƙo na jam'iyyar.

Kotun ta ce ƙarar, Nafiu Bala Gombe na da tushe don haka ta yanke wannan hukunci.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyar ADC da ɗan takararta suke kaddamar da yaƙin neman zaɓe a jihar Sokoto.

Da ma dai ADCn ta daɗe suna zargin cewa ana yi musu bita da kulli da nufin hana su yin takara.

A yanzu dai ana ganin matakin zai iya kai wa Kotun Kolin Najeriya, wadda za ta yanke hukunci na ƙarshe kafin babban zaɓen ƙasar na watan Janairu.

To, wane mataki Atiku zai iya ɗauka a halin yanzu?

Ɗaukaka ƙara

Matakin farko da ɓangaren Atiku Abubakar zai iya ɗauka nan take shi ne ɗaukaka ƙara zuwa kotun ɗaukaka ƙara ta Najeriya, a cewar wani masanin shari'a, da ke Najeriya, El-Zubair Abubakar.

Ya ce ɗaukaka ƙarar zai yi ƙoƙarin dakatar da hukuncin da aka yanke na kotun tarayya.

"Idan aka dakatar da hukuncin, Atiku da jam'iyyar ADC za su samu damar ci gaba da ayyukan da suke yi na yaƙin neman zaɓe, su kuma gabatar da ƙorafe-korafensu," in ji masanin shari'ar.

Ya ƙara da cewa ba su da wani zaɓin mataki da za su ɗauka na nan take, illa ɗaukaka ƙara.

Ya ce bin doka shi ya kamata ba husuma ba, kuma ita ce hanyar da za su bi don bin kadin su.

Ko Atiku na da damar sauya jam'iyya?

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masanin shari'a ɗan asalin Najeriya mazaunin Birtaniya Audu Bulama Bukarti ya ce Atiku Abubakar na da damar sauya jam'iyya, sai dai idan ya sauya jam'iyyar ba zai iya tsayawa takarar shugaban ƙasa ba.

"Zai iya sauya jam'iyya, domin a kowane lokaci ana iya sauya jam'iyya, amma ba zai iya tsayawa takara ba".

Sashe na 77 na kundin dokar zaben Najeriya ya bayyana cewa wajibi ne mutum ya yi rajista da jam'iyya kwana 30 gabanin lokacin zaɓen fitar da gwani kafin ya samu damar fafatawa domin neman takara.

Haka nan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasar ta ayyana 23 ga watan Afrilu zuwa 30 ga watan Mayu a matsayin lokacin yin zaɓen fitar da gwani, wanda hakan ke nufin wajibi ne duk wani mutum da ke son yin takara ya shiga jam'iyyar kafin wannan lokaci.

Hakan na nufin idan mutum ya gaza yin hakan, ba ya da damar tsayawa takara a jam'iyyar.

"Atiku ba shi da zaɓin sauya sheƙa (don yin takara) idan bai samu nasara a kotu ba saboda dokar zaɓen 2026 da aka yi wa garambawul ba ta tanadi haka ba," in ji masanin shari'a Abubakar El-Zubair.

Ya aka yi ADC ta tsinci kanta cikin wannan dambarwa?

Jam'iyyar ta ADC ta shiga cikin rikici ne a shekarar 2025, bayan da manyan jiga-jigan siyasa suka yi ta turuwar shiga jam'iyyar.

Manyan ƴan siyasar da suka koma ADC sun haɗa da Sanata David Mark, Rauf Aregbesola, Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai da kuma tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi.

Rikicin shugabancin jam'iyyar ya fara ne bayan murabus ɗin tsoffin shugabannin jam'iyyar karkashin jagorancin Mista Nwosu da kuma samun sabbin shugabanni karkashin David Mark ranar 29 ga Yulin 2025.

Lamarin ya ta'azzara bayan da Nafi'u Bala, tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar ya shigar da ƙara gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda yake neman kotu ta amince da shi a matsayin halastaccen shugaban jam'iyyar.

Lamarin ya kai har kotun koli inda ta tabbatar da shugabancin David Mark, ta kuma bai wa INEC umarnin kada ta saurari kowa sai ɓangaren Mark.

Sai kotun koli ta ce gundarin shari'ar ta koma ga mai sharia Peter Lifu wanda ita ce aka yi hukuncin a kanta.

A watan Yulin 2025 ne gamayyar wasu jiga-jigan ƴansiyasa a Najeriya da ke hamayya da gwamnatin jam'iyyar APC suka amince da African Democratic Congress (ADC) a matsayin jama'iyyar da za su ƙulla ƙawancen haɗaka a cikinta.

Ƴansiyasar sun ce sun amince da ADC ne da nufin haɗa ƙarfi da ƙarfe a cikinta da nufin kawar da jam'iyyar APC daga mulkin Najeriya a zaɓen 2027.

Bayan amincewa da ADC a matsayin jam'iyyar haɗaka ne jiga-jigan ƴan siyasar na hamayya suka zaɓi tsohon Shugaban Majalisar Dattawan ƙasar David Mark a matsayin shugaban jam'iyyar.

Sai dai daga baya abubuwa sun dagule bayan da Nafiu Gombe, ɗaya daga cikin shugabannin jam'iyyar gabanin yin haɗaka ya bayyana cewa ba ya cikin shugabannin jam'iyyar da suka ajiye muƙami.

Wane ne Atiku Abubakar?

Atiku Abubakar gogaggen dan siyasa ne da ya shafe shekaru da dama yana jan zaren. Hasalima yana daga cikin jiga-jigan mutanen da suka kafa jam'iyyar PDP.

An haifi Atiku Abubakar ranar 25 ga Nuwamban 1946 a Jihar Adamawa da ke Arewa Maso Gabas, kuma ya kasance jigon dan siyasa kuma hamshakin attajiri a Najeriya.

Tun bayan da Najeriya ta dawo mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, Atiku Abubakar ya kasance mataimakin shugaban kasar Najeriya na 11, a mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo a tsakanin 1999 zuwa 2007.

Atiku Abubakar ya tsunduma harkokin sisaya a 1989, kuma yana cikin makusantan tsohon mataimakin shugaban kasa na mulkin soji, Janar Shehu Musa Yar'adua.

Ya shiga jam'iyyu daban-daban tun da ya shiga harkokin siyasa.

An zabi Atiku Abubakar a matsayin gwamnan gwamnan Jihar Adamawa a 1998, ko da yake daga bisani Cif Obasanjo ya zabe shi domin kasancewa mataimakinsa.

Daga wancan lokacin zuwa yanzu, wannan ne karo na uku da Atiku Abubakar ke tsayawa takarar shugaban kasa, ko da yake ya tsaya zaben fitar da gwani sau da dama.

A shekarar 2007, jam'iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) ta tsayar da shi takara inda ya sha kaye a hannun dan takarar PDP, Umaru Musa Yar'adua.

Kazalika a shekarar 2019 ya fafata da Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC amma bai yi nasara ba.

A 2023 ya fafata da Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa, inda ya zo a matsayi na biyu.

A yanzu yana neman sake yin takara a zaɓen 2027, inda zai sake karawa da Bola Tinubu wanda ke kan mulki a yanzu.