Najeriya ta lashe kofin duniya na mata

Flamingos
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Tawagar mata ta Najeriya yan kasa da shekara 17 da ake wa lakabi da Flamingos sun lashe gasar kofin duniya bayan doke Japan da ci 2-1 a gasar ta Fifa da aka yi a Morocco.

Flamingos wadda ta kafa tarihin zama kasar Afirka ta farko da ta kai wasan karshe a gasar, yanzu ta sake kafa tarihin zama ta farko daga Afirka da suka lashe ta.

Duk da damarmaki da tawagar ta Najeriya ta rika samu, kungiyar ba ta samu damar zura kwallaye da yawa ba saboda yadda tawagar Japan ke wasa da zafin nama.

A minti ma 39 da fara wasa ne ‘yar wasan Najeriya Awawu Bashiru ta zura kwallon Najeriya ta farko.

Daga nan kuma sai a minti na 47 Okuebubue Umejiaku ta zura kwallo ta biyu bayan dage golar Japan Yamanaku.

Najeriya ta ci gaba da rike wasan a haka har na kimanin mintuna 80 kafin Japan ta rage tazarar kwallayen lokacin da ta zura wa Najeriya kwallo daya.

Japan ce ta buga kwallo sosai kafin zuwa hutun rabin lokaci sai dai ‘yanwasan nata sun yi sanyi bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Wannan ne karo na farko da kasashen biyu suka kara a wata gasa ta kasa da kasa.

Yanzu dai Najeriya ta kafa tarihin zama kasar Afirka ta farko da ta lashe kofin.