Tafki mai mayar da dabbobi duwatsu

Asalin hoton, Getty Images
Ka ayyana tamkar kana tafiya a gefen wani tafki mai abin al'ajabi da ke arewacin Tanzaniya.
Kana ganin yadda ruwa ke bayar da launin ja da ruwan hoda da kuma rawaya ƙarƙashin hasken rana a gabanka.
Yayin da kake ci gaba da kallo tare da sha'awar yanayin mai jan hankali sai wata halitta mai kama da tsuntsu a tsaye kusa da iyakar tafkin ta ja hankalinka.
Kana matsawa kusa sai ga abin mamaki, wani tsuntsu ne mara rai kuma bai rube ba ya yi kama da butum-butumin dutse.
Wani abu ne mai kama da al'mara ko fim, amma kuma gaskiya ne. Wannan shi ne tafkin Natron da ke kusa da iyakar Kasashen Tanzaniya da Kenya, yankin da ya kwashe shekaru da dama yana daukar hankalin masana kimiyya da masu daukar hotuna da kuma yan yawon bude ido daga ko ina a fadin duniya.
Daga sama tafkin Natron ya yi kama da wani zane mai daukar hankali. Launukansa sun fidda wani abin sha'awa a tsakiyar tuddan Rift da ke tsakiyar Afrika. Kyawun wurin zai sa ka yi tunanin wurin na daga cikin yankuna da suka fi aminci a duniya.
Amma bayan kyau da wurin ke da shi yana kuma dauke da wani yanayi mai tsananin tsauri ga wasu halittu masu rai. Ruwan tafkin yana da sinadarin alkaline sosai, tare da sinadarai masu kama da wadanda ake aikin tsaftace muhalli da su. A lokacin rani, yanayin zafi a wurare marasa zurfi cikin tafkin na iya kaiwa kusan maki 60°C (140°F), yanayin da zai iya yin barazana ga rayuwar wasu halittu da dama.
Wannan yanayi na musamman ya samo asali ne sakamakon ma'adinan da aka fitar daga Ol Doinyo Lengai, wani dutse mai aman wuta da ke kusa da tafkin Natron. Dutsen da Kabilar Maasai suka fi sani da "Dutsen Allah," dutsen mai aman wuta yana fitar da ma'adanai da ke kwararowa cikin tafkin, wanda hakan ya ba ruwansa wani nau'in sinadari na musamman wanda ya bambanta shi da sauran tafkunan duniya.
Duk da kyawunsa daga nesa, tafkin Natron na ƙunshe da yanayi mai ban mamaki. Siffarsa mai ban sha'awa tana haɗe da gurɓataccen yanayin muhalli abin da ya mayar da shi wuri mai ban mamaki a Afrika.
Mene ne ya sa dabbobin da suka mutu a ciki suke kama da dutse?

Asalin hoton, Getty Images
Tafkin Natron wanda ya yi fice a matsayin wurin da ke mayar da dabbobi zuwa duwatsu ya samo asali ne daga samuwar wani yanayi na musamman.
Akwai tsuntsaye da jemagun da tsautsayi ya sa suka faɗa cikin tafkin mai haske kamar madubi yayin da wasu suka kasa tserewa saboda yanayinsa mai tsanani.
Idan irin waɗannan dabbobi sun mutu sai sinadaran cikin tafkin su lulluɓe gawarwakin tsuntsayen ƙarƙashin zafin ranar Afrika sai su bushe su zauna a haka lokaci mai tsawo.
Sakamako mai ɗaukar hankali domin jikin zai zauna a surarsa, sinadaran da suka makale a jikin ne ke mayar da shi tamkar butum-butumim dutse.
Hotunan wadannan tsuntsaye sun karade duniya har mutane da dama sun yi imani cewa tafkin Natron na da ikon mayar da halittu masu rai zuwa dutse
Amma dabbobin ba wai suna komawa dutse ba ne, abin da ke faruwa sinadaran cikin ruwan ne ke hana jikin tsuntsayen lalacewa har su yi kama da butum-butumin da aka sassaka da dutse.
Tafkin Natron a matsayin tushen rayuwa

Asalin hoton, Getty Images
Duk da shahararsa a matsayin tafki mai yanayi mai tsauri ga nau'o'in halittu daban-daban, yana ɗaya daga cikin muhimman wuraren kiwon tsuntsaye a Afirka.
Kowace shekara, miliyoyin ƙananan agwagin ruwa wato flamingos suna yin jerin gwano zuwa tafkin Natron don yin ƙwai da kuma kiwon. Ruwan da yake da shi mai dauke da sinadarin alkaline da wuri mai nisa yana taimakawa wajen kare su daga mafarauta da dama sannan wurin yana da aminci don kiwo.
Sakamakon haka, tafkin Natron yana taka muhimmiyar rawa a rayuwar waɗannan agwagin ruwa wato flamingos. An yi kiyasin cewa an haifi kaso mai yawa na kananan agwagin flamingos a duniya a wannan yanki, wanda ya sa ya zama wuri mafi mahimmanci ga rayuwar wasu nau'in halittu a duniya.
Abin da ya sa agwagin ruwa suke rayuwa a nan
Ga yawancin halittu masu rai yanayin tafkin Natron yana da matukar wahala a rayuwarsu, duk da haka ya zama mafaka mai kyau ga agwagin flamingos.
Ƙafafunsu masu ƙarfi suna taimaka musu su bi ta cikin ruwan mai sinadarin alkaline mai ƙarfi, bugu da ƙari laka mai zafi da ke kewaye da wuraren da suke zaune na taimaka wa dabbobin daji kamar kura da dila da kuma karnuka.
Wannan yanayi ya baiwa agwagin flamingos kyakkyawan yanayin da za su yi ƙwai, su yi kiwo kuma su bunƙasa. A wurinsu tafkin Natron wanda ya zama mai haɗari ga dabbobi da dama ya kasance mafaka ga rayuwarsu.
Yanayi mai girma
Masu ziyara zuwa tafkin Natron da dama na barin wurin cikin wani irin yanayi a zuciya.
A wani bangaren kuma akwai ragowar tsuntsayen da ma'adinan tafkin ke adanawa ta hanya mai ban mamaki, suna kama da butum-butumin dutse.
Akwai kuma agwagin flamingos miliyoyi da ke rayuwa cikin yanayin mai tsanani.
Bayan kasancewar sa tafkin dutse
Wataƙila abin da ya sa tafkin Natron ke da ban sha'awa ke nan.
Ba wuri ne kawai da ake adana ragowar dabbobi ba.
Tafki ne na bangarori biyu masu bambanci da juna. Wuri ne mai tsauri da rashin dadi amma kuma duk da haka yana taimakawa wasu dabbobin daji a Afrika.
Babban abin sha'awa a tafkin Natron shi ne tabbatar da gaskiyar maganar nan da ake cewa abincin wani gubar wani.
Yayin da tafkin yake barazana ga wasu dabbobi, wasu dabbobin kuma, nan ne mafakarsu.

























