Yadda Iran ta fara aikin sake gina cibiyoyin makamanta da aka lalata

- Marubuci, Shayan Sardarizadeh
- Marubuci, Benedict Garman
- Marubuci, Matt Murphy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Verify
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Da alama Iran na gudanar da manyan sabbin ayyukan gine-gine a kusa da aƙalla manyan sansanonin makamai masu linzami guda biyu, sannan kuma tana gyaran sansanonin da hare-haren sama na Amurka da Isra'ila suka lalata tsawon watanni, kamar yadda nazarin hotunan tauraron dan'adam ya nuna.
Shaidar ta tonon ƙasa da kuma sabbin gine-gine na bayyana a hotunan tauraron ɗan'dam da aka ɗauka a watan Nuwamba a sansanin soja na Garmdareh da ke Karaj kusa da Tehran, babban birnin ƙasar, ,= da kuma sansanin Shahroud da ke arewacin ƙasar.
Masana a kamfanin leƙen asiri na Birtaniya na MAIAR, waɗanda suka nazarci hotunan, sun shaida wa BBC Verify hakan.
Aƙalla wasu wuraren soja guda 12, ciki har da sansanonin makamai masu linzami da filayen jiragen sama na soja, suna nuna alamun gyare-gyare.
An sanya sabbin rufi a kan gine-ginen da aka lalata a sansanin makamai masu linzami na Kermanshah da ke yammacin Iran kusa da iyakar Iraƙi, yayin da aka kwashe ɓaraguzan gini a harabar soja ta Parchin da ke gabashin babban birnin ƙasar, wadda aka sha gyarawa duk da jerin hare-haren sama da aka riƙa kai mata.
Jim Lamson, tsohon manazarcin CIA wanda ke lura da al'amuran Iran, ya ce tonon ƙasar da ake yi a kusa da Shahroud na iya kasancewa yana da alaƙa da ƙera makamai masu linzami.
Ya ce tun da filin jirgin saman soja na kusa da Shahroud ya sha fuskantar hare-hare sau da dama a cikin 'yan shekarun nan, akwai yiwuwar rundunar Juyin Juya Halin Iran IRGC na ƙoƙarin nemo hanyoyin da za ta mayar da wuraren ƙera makamanta zuwa ƙarƙashin ƙasa.
Wani manazarci a kamfanin MAIAR ya lura cewa Iran na da "al'adar mayar da kayayyakin more rayuwa ƙarƙashin ƙasa domin kare su daga ƙarin hare-hare".
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mark Mellett, manazarcin harkokin tsaro kuma tsohon shugaban rundunar sojin Ireland, ya ce gina wurare a ƙarƙashin ƙasa na da wata ƙarin fa'ida, wato yana sa ya zama "mafi wahala ga masu sa ido daga waje su tantance girman ayyukan da ake yi da kuma yanayin shirinsu na aiki".
Hasashe ya ƙaru a 'yan makonnin nan cewa Amurka na iya sake kai hari kan Iran bayan zaɓukan rabin wa'adi da aka gudanar a farkon wannan mako.
Sai dai a ranar Laraba, Mataimakin Shugaban Kasa JD Vance ya danganta rashin farin jinin yaƙin a tsakanin masu kaɗa ƙuri'a da irin yadda jam'iyyar Republican ta yi rashin nasara a zaɓukan wannan mako, yana mai cewa hakan na iya sa jam'iyyarsa ta rasa ikon mallakar majalisar dattawa "tsawon shekaru shida masu zuwa".
A wuraren soja da dama a faɗin ƙasar, sojojin Iran sun mayar da hankali kan gudanar da ƙananan gyare-gyare a cibiyoyin da hare-haren sama suka yi wa mummunar ɓarna tun bayan fara yaƙin Amurka da Isra'ila.
Masana sun ce hotunan tauraron ɗan'adam na nuna cewa an kammala muhimman ayyukan gine-gine a cibiyar Taleghan 2 da ke harabar soja ta Parchin, inda aka daidaita gine-ginen da suka lalace tare da gyarawa da kuma ƙarfafa su da siminti wurin da harin ya shafa a wani wuri da ke ƙarƙashin kasa.
A Karaj da Shahroud, hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna alamun manyan ayyukan haƙar ƙasa.
A Karaj, an ga motoci da dama a cikin hotunan tauraron ɗan'adam, yayin da kuma ake ganin an gudanar da wasu gyare-gyare a sansanin jiragen sama da ke kusa.
Hotunan daga Karaj sun nuna abin da ya yi kama da "sabuwar ƙofar shiga wata cibiyar da ke ƙarƙashin ƙasa", in ji Sam Lair, mai nazari kan bincike a Cibiyar Foreign Policy Research Institute (FPRI), wadda ta yi nazari sosai kan abubuwan da suka faru a baya-bayan nan a wurare daban-daban na Iran.
Sean O'Connor, wani mai nazari a kamfanin tattara bayanan sirri na Janes, ya ce da wuya ayyukan ginin su kasance wani yunƙuri na yaudarar hukumomin leƙen asirin ƙasashen waje.
Ya ce irin wannan aiki "zai iya zama mai tsada kuma wataƙila ba zai haifar da wani babban sakamako ba."
Waɗannan abubuwan na faruwa ne bayan da Fadar White House ta sha ba da tabbacin cewa hare-haren Amurka da Isra'ila sun raunana rundunonin sojin Iran matuƙa, abin da Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana a matsayin "cikakkiyar ɓarna da rugujewa".
Tun da farko wani kakakin Pentagon ya ce Amurka ta "lalata kusan kashi 90 cikin 100 na masana'antar ƙera jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami da kuma kayayyakin rundunar ruwa na Iran", sannan ta "raunana sosai" ƙarfin ƙasar na ƙaddamar da hare-hare ta amfani da jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami.
Sai dai Iran ta ce har yanzu tana da ɗimbin tarin makamai masu linzami, kuma bidiyon da gidan talabijin na gwamnati ya watsa a wannan mako ya yi iƙirarin nuna ɗimbin makamai masu linzami a ƙofar wata cibiyar da ke ƙarƙashin ƙasa a kudancin Iran.
A watan Agusta kuma, wani bidiyo da gidan talabijin na gwamnati ya watsa ya yi ikirarin nuna makamai masu linzami ƙirar Khordad masu harbo jiragen sama suna fitowa daga wani rami kusa da birnin Bandar Abbas da ke kudancin ƙasar.

Wani manazarci a kamfanin MAIAR ya kuma gano sabbin ayyukan gine-gine da tonon ƙasa a wajen mashigar ramuka kusa da birnin Qom, da ke kusa da cibiyar tace sinadarin uranium ta ƙarƙashin ƙasa ta Fordo, wadda Amurka da Isra'ila suka sha kai wa hare-haren bama-bamai sau da dama.
Mark Cancian, manazarcin harkokin soja a shirin International Security Program na cibiyar Center for Strategic and International Studies (CSIS), ya ce ayyukan da suka shafi kadarorin soja na nuna cewa Tehran na shirin tunkarar yiwuwar ƙarin hare-hare daga Amurka da Isra'ila.
"Manufar ita ce ta ƙara inganta kariyarta daga duk wani hari da za a kai nan gaba," in ji shi.
"Haka kuma yana nuna cewa an ba da fifiko ga sake gina karfin soja maimakon farfado da tattalin arzikin ƙasar."



























