Abubuwa biyar kan Sheikh Yahaya Masussuka

Asalin hoton, Sheikh Yahaya Masussuka/Facebook
Mutuwar Sheikh Yahaya Masussuka bayan harin da aka kai masa a gaban gidansa ta sa ana cigaba da tattaunawa kan rayuwarsa, tare da tafka muhawara kan fahimtarsa ta Qur'ani zalla.
Tuni wasu suka koma bincike kan rayuwarsa, koyarwarsa da kuma muhawarar da ya jawo a fagen addinin Musulunci a Arewacin Najeriya. inda wasu ke masa kallon mai janyo ce-ce-ku-ce, yayin da wasu ke masa kallon malamai mai son zaman lafiya da ɗabbaƙa fahimtar juna a tsakanin addinai.
A tsawon shekaru, Masussuka ya kasance ɗaya daga cikin fitattun malaman da suka janyo ce-ce-ku-ce saboda fahimtarsa ta "Ƙur'ani zalla", wadda ta bambanta da abin da mafi yawan malamai na Ahlus Sunna ke koyarwa.
A cikin takardar binciken da ya gabatar mai taken "Scripture, Science & Sense: A Neo-Quranist's Discourse in Northern Nigeria", malami a Jami'ar Bayero da ke Kano, Dokta Murtala Uba Mohammed, ya bayyana Masussuka a matsayin "ɗaya daga cikin manyan jagororin masu ra'ayin Alƙur'ani zalla na wannan zamani a Arewacin Najeriya."
Marubucin ya yi nazarin koyarwar malamin, tarihin tafiyarsa da kuma tasirin da ya yi a tattaunawar addini a yankin.
Ga wasu muhimman abubuwa biyar da ya kamata a sani game da Sheikh Yahaya Masussuka:
Ya fara wa'azi tun yana ƙarami
Ɗaya daga cikin abubuwan da suka bambanta Sheikh Yahaya Masussuka shi ne cewa ya fara harkar wa'azi tun yana ɗan shekara 13. Wannan na nufin ya shafe fiye da shekara 30 yana koyarwa da wa'azi kafin rasuwarsa.
Masussuka ya yi karatu a makarantun allo da tsangaya, kafin daga baya ya nemi ilimi a ƙasashen waje. A cewar bayanan da sakatarensa Dokta Mustapha Haruna ya tabbatar wa BBC, ya yi karatu a Jami'ar Al-Azhar da ke Masar da kuma ƙasar Oman.
Hakazalika, an ruwaito cewa ya yi karatu a hannun malamai da dama, ciki har da Sheikh Alhassan Lamido da Sheikh Usman Dangungu na Kaduna. Wannan ya sa ya samu tushen ilimin addini tun kafin ya fara gabatar da nasa fahimtar addinin Musulunci.
Yadda ya zama fitaccen mai ra'ayin "Alƙur'ani Kaɗai"
Babban abin da ya sa Masussuka ya yi suna shi ne ra'ayin da yake ɗauka na cewa Alƙur'ani shi kaɗai ya isa a matsayin tushen shiriya ga Musulmi.
Dokta Murtala Uba Mohammed ya ce: "Masussuka yana wakiltar ɗaya daga cikin fitattun masu fafutukar Alƙur'ani kaɗai a Arewacin Najeriya."
Marubucin ya bayyana cewa Masussuka yana ƙin dogaro da hadisai da kuma abin da ya kira tsarin malamai na gargajiya wajen fassarar addini.
A cikin takardar binciken, marubucin ya ce: "Yana amfani da Alƙur'ani a matsayin babban, kuma a mafi yawan lokuta shi kaɗai, tushen hujjojinsa."
Wannan fahimta ta sa ya shiga muhawara da malamai da dama, musamman kan batutuwan da suka shafi Hadisi, fikihu da sauran bangarorin koyarwar Musulunci da suka dogara da Sunnah.
Amfani da kafafen sadarwa

Asalin hoton, Masussuka/Facebook
Ba kamar wasu ƙungiyoyin da suka gabata ba, Masussuka ya rungumi damar da kafafen sadarwa da kafafen sada zumunta suka bayar wajen yaɗa ra'ayoyinsa.
A cewar binciken Dakta Murtala: "Ra'ayoyin suna yaɗuwa ta hanyar wa'azi ga jama'a, kafafen sada zumunta da kuma tattaunawa ta ilimi."
Marubucin ya ƙara da cewa Masussuka ya zama misali na yadda sabbin hanyoyin sadarwa suka bai wa daidaikun mutane damar yin tasiri kai tsaye ga jama'a ba tare da sun dogara kacokan ga cibiyoyin malamai na gargajiya ba.
A shekarun baya, darussansa da tattaunawarsa sun rika yawo a Facebook, YouTube da sauran dandamali, abin da ya taimaka wajen jawo masoya da kuma masu suka daga sassa daban-daban na Najeriya.
Jawo muhawara mai zafi
Masussuka ya kasance cikin malaman da suka fi jawo muhawara a Arewacin Najeriya, musamman a kan addini.
A cikin bincikensa, Dokta Murtala ya lura cewa Masussuka ya yi suka kan wasu koyarwar da ake ɗauka a matsayin ginshiƙan fahimtar Musulunci a wajen mafi yawan malaman Sunnah.
Misali, ya riƙa yin tambayoyi game da wasu koyarwa da suka shafi rayuwar kabari, azabar kabari da wasu al'amuran gaibu.
Sai dai duk da suka da martanin da yake fuskanta, marubucin takardar ya nuna cewa akwai wasu masu ilimi da suke ganin ya kamata a yi nazarin hujjojinsa maimakon a yi watsi da shi kai tsaye.
Zaman gidan yari
Rayuwar Sheikh Yahaya Masussuka ba ta rasa ƙalubale ba. Rahotanni sun nuna cewa ya fuskanci matsin lamba daga jami'an tsaro da kuma wasu daga cikin masu adawa da koyarwarsa.
An taɓa kama shi kuma aka tsare shi na wani lokaci kan wasu batutuwan da suka shafi wa'azinsa.
A cewar bayanan da aka tattara, an kuma taɓa ɗaure shi a gidan yari na tsawon watanni tara a jihar Katsina.
Duk da waɗannan matsaloli, ya ci gaba da gudanar da wa'azi da yada fahimtarsa har zuwa rasuwarsa.
Rasuwarsa ta zo ne bayan wasu ƴanbindiga sun harbe shi a ƙofar gidansa da ke yankin Dutsen-Ma. Lamarin ya jawo martani daga mabiyansa da kuma sauran al'ummar Musulmi, inda mutane suka ci gaba da muhawara kan rawar da ya taka a tarihin tattaunawar addini a Arewacin Najeriya.

























