Tarihi 8 da Cristiano Ronaldo ya kafa a Portugal

Asalin hoton, Getty Images
A duniyar ƙwallon ƙafa, akwai ƴanwasa da dama da suka yi fice wajen nuna bajinta, amma kaɗan ne suka nuna irin ƙwazon da Cristiano Ronaldo ya nuna a duniyar ƙwallon ƙafa a wannan zamani.
Tun bayan fara taka leda a matakin manya a ƙasar Portugal zuwa zama fitaccen tauraro a ƙungiyoyi irin su Manchester United da Real Madrid, Ronaldo ya shafe sama da shekara ashirin yana karya manyan tarihin da ake ganin za su daɗe ba a karya ba.
Ana ganin ɗanwasan, wanda aka haifa a birnin Madeira na ƙasar Portugal a matsayin wanda ya sauya tarihin ƙwallon ƙasarsa, sannan ya zama madubin tamaula a ƙasar da matasa ke koyi da shi.
Ronaldo mai shekara 41 a duniya ya sanar da yin ritaya daga buga wa ƙasarsa wasa, wadda ya ci wa ƙwallo 146 kuma ya buga mata wasa sau 234 - tun bayan fara buga wa ƙasar wasa a shekarar 2003.
A sanarwarsa ta ritaya, Ronaldo ya rubuta cewa, "Ya ku al'ummar Portugal, rana ta zo da zan mayar gadar da riga mai lamba 7 ga wani a cikin tawagar ƙasarmu," in ji Ronaldo a wani bayani da ya yi na bidiyo da ya wallafa a shafin Instagram.
"Dama ban taɓa tunanin cewa tawa ba ce ni kaɗai, amma ina alfahari da samun damar wakiltar ƙasata sama shekara 23."
A matakin nahiyar Turai kuwa, babu ɗan wasan da ya yi tasiri a gasar zakarun Turai ta UEFA kamar Ronaldo. Yana riƙe da mafi yawan ƙwallaye da kuma mafi yawan wasannin da aka buga a tarihin gasar, sannan yana jiran zura ƙwallo ta 1,000.
Manyan tarihin da ya kafa
Shekara 23 yana ci wa Portugal ƙwallo
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Fitaccen ɗanwasan ya fara ci wa ƙasarsa ƙwallo ne a shekarar 2004, sannan ya zura mata ƙwallo a wannan shekarar ta 2026.
Na farko da ya kai wasa 200 a matakin ƙasa da ƙasa na maza
Ronaldo ya zama ɗanwasa na farko da ya kai wasanni 200 a matakin ƙasashe na maza, lokacin da ya taka leda a wasan neman gurbin shiga gasar EURO 2024 da Portugal ta buga da Iceland.
Ƙwallo 100 a ƙasashen turai
Ronaldo ne ɗanwasa na farko da ya zura ƙwallo 100 a wasannin ƙasa da ƙasa ga wata ƙasa a Turai.
Ƙwallo uku rigis
Ronaldo ya kuma zama ɗanwasa na farko da ya ci ƙwallo uku rigis sau 10 a wasannin ƙasa da ƙasa, wani tarihi da daga baya Lionel Messi ya wuce lokacin da ya kai guda 11 bayan nasarar Argentina da ci 3-0 a kan Algeria a gasar cin kofin duniya.
Cin ƙwallo a gasar kofin duniya shida
A bara kuma, Ronaldo ya zama ɗanwasa na farko da ya taka leda tare da cin ƙwallo a gasar cin kofin duniya shida daban-daban. Ya fara fitowa a gasar a wasan da Portugal ta buga da Angola a 2006, sannan ya ci ƙwallonsa ta farko a gasar a wasa da Iran.
Ƙwallonsa ta ƙarshe a Kofin Duniya ita ce bugun fenariti da ya ci a wasan zagaye na 32 da Croatia a gasar 2026.
Ya samu nasarar cin ƙwallo a kofunan duniya na 2006, 2010, 2014, 2018, 2022 da 2026.
Mafi tsufa da ya ci ƙwallo a wasannin neman gurbin kofin duniya
Bugu da ƙari, ya zama ɗan wasa mafi tsufa da ya ci ƙwallo a wasan zagayen fitar da gwani na Kofin Duniya, yana da shekara 41 da kwanaki 147.
Mafi yawan gasar EURO
Ronalo ne ɗanwasan da ya fi buga gasar nahiyar turai ta EURO, inda ya buga gasar sau shida.
Mafi yawan ƙwallaye a wasannin neman gurbin Kofin Duniya
Ya ci ƙwallo 41 a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.
Kyautar Ballon d'Or sau biyar.
Daga tsibirin Madeira zuwa ɗaya daga cikin manyan ƴan ƙwallon duniya
An haifi Cristiano Ronaldo dos Santos Aveiro a ranar 5 ga Fabrairu 1985 a Funchal, babban birnin tsibirin Madeira na ƙasar Portugal. Ya taso ne a gida mai ƙaramin ƙarfi, amma tun yana ƙarami ya fara nuna alamar zama babban ɗanwasan ƙwallon ƙafa.
Ya fara taka leda a ƙungiyar Andorinha, kafin daga bisani ya koma Nacional, sannan ya koma sashen horar da ƴanwasan ƙwallon ƙafa ta Sporting CP yana da shekara 12.
A lokacin yana matashi, an gano yana da wata matsala ta zuciya wadda ka iya kawo cikas ga burinsa na zama ɗanwasa. Sai dai bayan an yi masa tiyata, ya ci gaba da da taka leda tare da bunƙasa har ya kai ga fara bugawa babbar ƙungiyar Sporting CP wasa a shekarar 2002.
Bajintar da ya nuna ta ja hankalin kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson, wanda ya saye shi a shekarar 2003. A Ingila ne Ronaldo ya fara zama fitaccen tauraro, inda ya taimaka wa United lashe kofunan Premier League uku da kuma UEFA Champions League a 2008.
A wannan shekarar ce kuma ya lashe kyautar Ballon d'Or ta farko, wadda magoya bayan ƙwallon ƙafa suka zaɓa a matsayin kyautar da ta fi armashi wato BOAT.
A shekarar 2009 ya koma Real Madrid a cinikin da ya kasance mafi tsada a duniya a lokacin. A can ne ya cimma kololuwar nasarorinsa, inda ya zama mafi yawan cin ƙwallaye a tarihin kulob ɗin da ƙwallo 450 cikin wasa 438. Ya kuma taimaka wa Madrid lashe gasar zakarun Turai sau huɗu da kuma gasar La Liga sau biyu.
Daga baya ya koma Juventus a Italiya, inda ya lashe kofin Seria A, kafin ya sake komawa Manchester United.
A watan Janairun 2023 kuma ya koma ƙungiyar Al-Nassr ta Saudiyya, inda har yanzu yake taka leda, inda har yanzu ake kallonsa a cikin ɗaya daga cikin fitattun ƴanwasa a duniya duk da ya haura shekara 41.
Manyan kofunan da ya lashe
- Kofin Turai na EURO 2016 tare da Portugal.
- Gasar UEFA Nations League a 2019 da 2025.
- Gasar UEFA Champions League sau 5.
- Gasar Premier League sau 3 tare da Manchester United.
- Gasar La Liga sau 2 tare da Real Madrid.
- Gasar Serie A sau 2 tare da Juventus.
- Gasar Firimiyar Saudi da Al Nassr
- Kyautar Ballon d'Or sau 5.

























