Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Man United ta ci gaba da kasa samun nasara bayan kunen doki da Leeds

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin kai tsaye a BBC Hausa daga 11 zuwa 18 ga watan Oktoban 2026.

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad

  1. Dakika 99 tsakanin kwallon farko da ta biyu da aka ci City

  2. Abin mamaki cikin ƴan mintuna kaɗan ga PSG!, Champions League

    Manchester City ta rikice gaba ɗaya a fannin tsaron bayanta, amma wannan yunkuri ne daga PSG.

    Desire Doue ya samu kwallo mai kyau ya saka kai ta fada raga, inda Ousmane Dembele ya buga masa kwallo.

    Masu gida sun yi matuƙar kaɗuwa.

  3. Aston Villa 1-0 Fenerbahce, Johan Manzambi

    Bugun da Matteo Guendouzi da ya yi kai ya sauka kai tsaye wurin Johan Manzambi, wanda ya fara sarrafa kwallon kafin ya buga.

    Ƙwallon ta karkace bayan ta buga Milan Skriniar, lamarin da ya ruda Ederson, kuma aka samu cin 1-0.

  4. Guardiola na kallon wasan karon farko da ya je Etihad

  5. Man City 0-1 PSG, Desire Doue

    Zakaran Turai sun fara cin kwallo!

    Desire Doue ya zura kwallo bayan PSG ta gina hari tun daga baya har zuwa gaba.

  6. Vinicius ba zai buga El Clasico ba da wasa uku, saboda jan kati, Real Madrid

    Dan wasan Real Madrid Vinicius Jr ba zai buga wasan El Clasico da Barcelona ba, bayan da aka dakatar da shi wasa hudu a La Liga.

    An kori dan wasan na Brazil bayan ya ja gashin Nathan Saliba a wasan da Real Madrid ta doke Villarreal da ci 1-0 a ranar Asabar da ta gabata.

    Dakatarwar na nufin zai rasa karawa da Sevilla ranar 18 ga watan Oktoba da na Barcelona ranar 25 ga watan Oktoba da na Racing Santander ranar 1 ga watan Nuwamba da na Valencia ranar 7 ga watan Nuwamba.

    Vinicius Jr ya shiga wasa ne a minti na 52 a karawar da Villarreal, kuma ya ci wata kwallo amma daga baya aka soke ta.

    Hakan ya biyu bayan da alkalin wasa ya sake duba yadda aka kai harin ta inda aka nuna a fili cewa Vinicius ya ja gashin Saliba kafin ya zura kwallon. Daga nan ne aka ba shi jan kati sannan aka soke kwallon.

    Kwamitin ladabtarwa na Hukumar Kwallon Kafar Sifaniya ya dakatar da dan wasan karawa biyu saboda "aikata laifin rashin da'a, sannan aka kara dakatar da shi wasu wasanni biyu saboda "kalubalantar alkalin wasa".

    Bayan wasan, kocin Real Madrid Jose Mourinho bai halarci taron manema labarai ba.

    Daga baya Vinicius ya nemi afuwa a wani sako da ya wallafa a kafafen sada zumunta, inda ya ce "yana neman gafara ga kungiyar da kuma magoya bayan Real Madrid."

  7. Bournemouth na shirin sayar da Scott a Janairu idan an yi tayi mai tsoka, Bournemouth

    Kungiyar Bournemouth ta ce a shirye take ta sayar da dan wasan Ingila, Alex Scott a kasuwar cinikaayyar 'yan wasa ta Janairu idan aka cika wasu sharudda.

    Dan wasan mai shekaru 23 ya dade yana neman barin kungiyar ta Vitality Stadium tun bayan da ya ki amincewa da sabunta kwantaraginsa sau biyu a karshen kakar wasan da ta gabata. Duk da haka, Bournemouth ta dage a lokacin hutun wasannin kasa da kasa cewa dan wasan ba na sayarwa ba ne.

    Sai dai, bayan karin tattaunawa da wakilansa, majiyoyi sun bayyana cewa Bournemouth za ta amince ta sayar da Scott idan an kawo tayi mai tsoka a watan Janairu.

    Wani muhimmin sharadi kuma shi ne matsayin kungiyar a teburin gasar Premier League. Idan Bournemouth na fama da barazanar faduwa daga gasar, mai yiwuwa ta yanke shawarar ci gaba da rike Scott domin taimaka mata wajen tabbatar da tsira daga faduwa a Premier League.

    Wannan sauyi ne mai girma idan aka kwatanta da yanayin bazarar da ta wuce, lokacin da Bournemouth ta yi watsi da tayin da kungiyoyi da dama suka yi wa dan kwallon. An yi imanin cewa dukkan kungiyoyin da ake kira manyan shida na Premier League sun tuntubi Bournemouth don neman bayani kan sayensa.

    An gargadi dukkan kungiyoyin kada su gabatar da tayi ko kuma su tuntubi dan wasan. Duk da haka, Chelsea ta gwada sa'arta da tayin fam miliyan 60, wanda zai iya kaiwa fam miliyan 64 tare da kari, amma Bournemouth ta yi watsi da tayin.

    Har yanzu Chelsea da Liverpool na nuna sha'awar son sayen Scott. Yayin da Manchester City, Manchester United da Tottenham Hotspur suka karkata hankalinsu ga wasu 'yan wasa a lokacin bazara.

    A halin yanzu Scott ba ya taka leda saboda jinya a raunin da ya samu a wasan da Ingila ta lallasa Croatia da ci 7-0 a gasar Nations League, kuma ana sa ran ba zai buga wasa ba na akalla wata guda.

  8. Sakamakon wasannin da aka buga Talata

  9. Atletico ta doke Manchester United, Atletico Madrid 2-0 Manchester United

    An tashi wasan, kuma Manchester United mai 'yan wasa 10 a cikin fili ta sha kashi.

    Ko da yake ta nuna wasa mafi kyau idan aka kwatanta da na karshen mako, har yanzu kungiyar ta buga wasanni tara a bana kuma ta samu nasara biyu kacal.

  10. An tashi wasan Arsenal ta hada maki uku, Arsenal 3-0 Lille

    Arsenal ta ɗauki minti 64 kafin ta samu ƙwallon farko, amma tana karya lagon Lille, sai ƙofofin zura ƙwallaye suka buɗe.

    Ta samu nasara a cikin sauƙi ga ƙungiyar ta Mikel Arteta

  11. , Atletico Madrid 2-0 Manchester United

    Ademola Lookman

    Manchester United ba ta kula da cewar da yan wasa 10 take taka leda ba ta bari an kara mata na biyu a raga.

    Dan wasan da ya shiga canji Ademola Lookman ne ya ci kwallo ta biyu ta Atletico Madrid.

    Masu masaukin baki sun kai hari cikin sauri, inda bugun farko na Jonathan David mai tsaron gida ya ture, amma Lookman ya yi gaggawar karɓar ƙwallon da ta dawo kafin ya tura ta cikin raga.

    Atletico Madrid yanzu na jagorantar wasan da ci 2-0.

  12. An kori Olise daga wasan Viking, Viking 2-3 Bayern Munich

    Me ke faruwa a wannan wasa?

    Bayern Munich ta farke kwallayen da aka zura mata har ta kara cin wata a kai, amma yanzu an rage mata yawan 'yan wasa sun koma 10 a cikin fili bayan da aka nuna wa Michael Olise kati na biyu mai launin rawaya.

    An nuna masa katukan rawaya biyun ne cikin tazarar daƙiƙa 30 kacal.

    Sakamakon haka, Olise zai rasa wasan Bayern na gaba da Arsenal.

  13. , Atletico Madrid 1-0 Manchester United

    Manchester United tana sha wahala idan tana karawa da mutum 10 a cikin fili, don haka watakila za ta fi taka rawar gani da ace abokiyar karawa ce aka korar mata dan wasa.

    Tana da saura fiye da minti 10 kacal domin nemo kwallon daidaitawa.

  14. JAN KATI an kori Leny Yoro daga karawar, Atletico Madrid 1-0 Manchester United

    Alkalin wasa ya je domin kallon allon VAR kuma ya gamsu cewa ya kamata a kori Leny Yoro, inda nan take ya nuna masa jan kati.

    Yanzu Manchester United ta rage da 'yan wasa 10 a filin wasa.

  15. Diaz ya ci wa Bayern Munich kwalo na uku, Viking 2-3 Bayern Munich

    Harry Kane ya daga wata ƙwallo mai kyau zuwa cikin akwatin fanareti, inda Konrad Laimer ya same ta kafin ya miƙa wa Luis Diaz wanda ya ƙarasa ta cikin raga.

    Shin mafarkin Viking ya zo ƙarshe yanzu?

  16. Arsenal ta karya lagon Lille, Arsenal 1-0 Lille

    A ƙarshe dai Arsenal ta ci kwallo!

    Duk da cewa ƙwallayen da Noni Madueke ke aikawa cikin akwatin fanareti ba su yi tasiri sosai ba a tsawon wasan a wannan karon an samu abinda ake bukata.

    Arsenal yanzu tana jagorantar wasan da ci 1-0 yayin da Lille ke neman hanyar dawowa kafin ƙarshen wasan.

  17. Kane ya sake zura kwallo, Bayern ta farke kwallayen, Viking 2-2 Bayern Munich

    Cikin kankanin lokaci, Bayern Munich ta dawo daga baya ta farke kwallayen, kuma Harry Kane ne ya sake zama gwarzo da kwallonsa ta biyu a daren yau.

    Joshua Kimmich ya kutsa ta gefen dama kafin ya daga wata ƙwallo mai kyau zuwa cikin akwatin fanareti, inda kyaftin din Ingila Harry Kane ya yi amfani da kansa wajen tura ta cikin raga.

    Yanzu wasan ya koma 2-2, bayan da Bayern ta farfaɗo daga rashin nasara da ci 2-0.

    Kane ya ci kwallo ta biyu a wasan kuma yana ci gaba da nuna kwarewarsa a gasar Champions League.

  18. Kane ya ci wa Bayern kwallo, Viking 2-1 Bayern Munich

    Bayern Munich ta dawo cikin wasan, kuma wanda ya yi hakan ba kowa ba ne illa Harry Kane.

    Dan wasan na Ingila ya zura kwallon ne daga bugun fenariti, inda ya rage gibin da Viking ke da shi zuwa kwallo daya.

    Da wannan Kane ya samu zura kwallo a wasanni tara a jere da ya buga a gasar Champions League.

    Shin akwai karin abin da zai biyo baya a daren yau? Bayern tana nuna alamun dawowa fafatawar, yayin da Viking ke kokarin kare jagorancin da take da shi na ci 2-1.