Wane ne matashin da zai jagoranci yaƙin neman zaɓen Obi da Kwankwaso?

xxx
    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Yayin da siyasar Najeriya ke ci gaba da ɗaukar harama, da yadda ake ta kiraye-kirayen a riƙa ba matasa damar shiga ana damawa da su a harkokin siyasar ƙasar, hankali ya koma kan naɗa matashi a matsayin Darakta-Janar na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa.

Wannan na zuwa ne bayan jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta naɗa Ibrahim Hussain Abdulkarim, wanda aka fi sani da Mallam Ziter, a matsayin Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar.

Mallam Ziter ƙwararre ne a fannin fasahar sadarwa da tsarin bayanan taswira (GIS), sannan yana da gogewa a harkokin kasuwanci da siyasa. Naɗin nasa ya ja hankalin masu bibiyar siyasa, musamman ganin yadda ake kallon matasa a matsayin masu rinjaye a cikin yawan masu kaɗa ƙuri'a a Najeriya.

Masana na ganin wannan mataki wata alama ce da ke nuna yadda jam'iyyu ke ƙoƙarin sauya tsarin da aka saba na bai wa tsofaffin jiga-jigan siyasa manyan mukamai a kamfen.

Sai dai tambayar da ake yi ita ce ko matashi zai iya ɗaukar nauyin irin wannan babban aiki, musamman ganin ya shafi shirya yaƙin neman zaɓen babban ɗantakara irin su Peter Obi da mai mara masa baya Rabiu Musa Kwankwaso.

Naɗin Mallam Ziter ya zo a lokacin da ake ƙara matsa lamba ga jam'iyyun siyasa su bai wa matasa damar jagoranci. Duk da cewa shekaru kaɗai ba su isa su tabbatar da nasara ba, masana na ganin ƙwarewa, nagartar tsari da ikon haɗa mutane su zaɓi jam'iyya ne manyan ayyukan darakta-janar na kamfen.

Ibrahim Hussain Abdulkarim

Shin zai iya?

Masanin siyasa kuma malami a kwalejin sharar fagen shiga jami'a ta Kano, Kabiru Sufi, ya ce tun tuni ake kiraya-kirayen a riƙa ba matasa dama a manyan muƙaman siyasa saboda adadinsu a cikin masu zaɓe ya fi yawa.

"Dama dai an daɗe ana tunanin ya kamata a riƙa ganin irin wannan sauyi, domin idan aka duba ƙididdiga za a ga cewa matasa da mata suna da yawa a cikin masu zaɓe. Saboda haka ana ganin akwai buƙatar a riƙa ganin matasa a gaba-gaba na yaƙin neman zaɓe," in ji shi.

A cikin shekaru goma da suka gabata, an ga yadda matasa suka fara taka rawa a siyasar Najeriya, musamman a kafafen sada zumunta da kuma harkokin yaƙin neman zaɓe.

A zaɓen 2023, matasa sun taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa saƙonnin siyasa, tattara magoya baya da kuma wayar da kan masu zaɓe, musamman a manyan jam'iyyun siyasar ƙasar.

Kabiru Sufi ya ce akwai misalai da ke nuna yadda matasa suka sauya jam'iyyunsu ko kuma suka shiga sababbin jam'iyyu kuma suka yi fice, lamarin da ya nuna suna da damar kawo sauyi idan aka ba su dama.

"Ana ganin hakan ya nuna cewa matasa na iya yin wani abu idan aka ba su dama, har su yi tasiri" in ji shi.

A cewarsa, babban abin jira a gani a yanzu shi ne ko sabon Darakta-Janar ɗin zai iya cika tsammanin da ake yi masa.

"Yanzu abin da za a kula da shi shi ne ko zai iya abin da ake tsammani. Amma babu shakka ana kira ga matasa su samu dama, kuma ga wata babbar jam'iyya ta nuna hakan a aikace."

Shin muƙamin DG na da tasiri?

Ɗaya daga cikin abubuwan da ake yawan dubawa wajen naɗin Darakta-Janar na kamfen shi ne ƙarfinsa na kuɗi da kuma tasirinsa a cikin al'umma, musamman duba da irin muƙaman da ya riƙe a baya.

Sai dai Kabiru Sufi ya ce ba lallai ne arzikin mutum shi ne abin da zai tabbatar da nasararsa ba.

"Akwai masu tunanin cewa sai jagoran yaƙin zaɓen ya kasance mai kuɗi sosai. Amma yawanci kuɗin kamfen ba kuɗinsa ba ne. Kuɗaɗe ne da jam'iyya ta tara kuma INEC ta sahale su idan komai yana tafiya cikin tsarin doka," in ji shi.

Ya ƙara da cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne ƙwarewar mutum wajen sarrafa kuɗaɗen yaƙin zaɓen da aka sahale masa, sannan kuma ya dage wajen gudanar da aiki cikin gaskiya.

"Ko da kuwa shi ba mai kuɗi ba ne, idan yana da ƙwarewar sarrafa kuɗi ba tare da almundahana ba, hakan ba zai zama masa cikas ba."

Ko darakta-janar na da tasiri wajen cin zaɓe?

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masanin siyasar ya bayyana cewa Darakta Janar na kamfen yana da muhimmiyar rawa wajen tsara yadda yaƙin neman zaɓe zai gudana, daga kafa kwamitoci zuwa tsara yadda za a kai saƙon jam'iyya ga masu zaɓe.

"Suna da tasiri sosai saboda tsare-tsaren da suka zo da su da kuma irin mutanen da suka saka a kwamitoci su ne za su taimaka waje tallata jam'iyyar. Haka kuma yadda suka tsara gudanarwa da mutanen da za su riƙa ziyarta yana da matuƙar tasiri," in ji Sufi.

Ya ce a lokuta da dama ana zaɓar mutane masu suna ko masu kuɗi a waɗannan muƙamai saboda tasirin da za su iya kawowa a wajen jawo hankalin masu ruwa da tsaki.

"Yawanci ana saka manyan mutane ne domin akwai ziyara da ake kai wa masu ruwa da tsaki da shugabanni. Suna ganin hakan na ƙara wa kamfen daraja da ƙima wataƙila da karɓuwa."

Saboda haka, a cewarsa, wannan naɗi zai zama wata dama ta gwadawa ko matashi zai iya yin abin da ake tsammani a irin wannan babban matsayi, da suke daɗe suna kira da a ba su.

"Shi ya sa ake ganin dole a zuba ido a gani ko matashin zai fitar wa matasa kunya ko kuma zai tabbatar da cewa sun cancanci irin waɗannan manyan nauye-nauye."

Za a ba shi dama?

Duk da yabon da wasu ke yi wa wannan mataki, akwai masu tambayar ko da gaske jam'iyyar ta yarda da matasa ko kuwa wata dabara ce ta jan hankalin masu zaɓe kawai.

Sai dai Kabiru Sufi ya ce bai kamata a yi gaggawar zargin waɗanda suka yi naɗin ba, ba tare da a ga abin da ya faru ba.

"Ba za mu iya yanke hukunci kan waɗanda suka ba shi wannan dama ba yanzu. Za mu kyautata musu zato cewa da zuciya ɗaya suka yi hakan domin su kawo sauyi a yadda ake gudanar da abubuwa."

Ya ce lokaci ne kawai zai tabbatar da ko an ba shi cikakken iko ko kuma an yi amfani da shi ne a matsayin fuskar yaƙin neman zaɓe.

"Idan lokaci ya yi kuma muka ga an ba shi dama ya gudanar da aikinsa yadda ya kamata, za mu ce an yi wani sabon salo. Amma idan aka ga ba a ba shi dama ba, sai a ce tun farko akwai lauje cikin naɗi."

Kamar yadda Kabiru Sufi ya nuna, abin da ya rage a gani shi ne ko wannan matashi zai iya amfani da damar da aka ba shi wajen tabbatar da cewa matasa ba kawai masu kaɗa ƙuri'a ba ne, har ma masu iya jagorantar manyan ayyukan siyasa a Najeriya.