Me ya sa sabon fim ɗin Salman Khan ya tayar da ƙura?

Asalin hoton, Salman Khan Films
"Idan waɗanda suke son ganin an yi yaƙi suka zo suka yaƙe mu, wannan yaƙin ba zai taɓa faruwa ba."
Wannan na ɗaya daga cikin kalaman da aka ji a cikin tallar sabon fim ɗin jarumin fina-finan Bollywood, Salman Khan, mai suna Maatribhumi: May War Rest in Peace. Da alama wannan shi ne babban saƙon da fim ɗin yake son isarwa.
Jim kaɗan bayan fitar da tallan fim ɗin a jiya, an fara muhawara mai zafi kan Salman Khan da sabon fim ɗin nasa. Yayin da wasu suka yaba wa jarumin, wasu kuma sun soki fim ɗin.
Bidiyon tallan fim ɗin mai tsawon mintuna huɗu da daƙiƙa 35 ya fara da wani rubutu a Turanci da ke cewa: "Mutumin da ya fi kowa ƙin yaƙi shi ne sojan da ya taɓa fuskantar sa, domin yaƙi yana ƙarewa ne kawai da mutuwar sojoji."
A wani ɓangare na bidiyon kuma, Salman Khan ya ce: "Me ya sa za a ji tsoron mutuwa? Ai abu ne da kowa zai fuskanta."
Haka kuma, fim ɗin ya ƙunshi wasu fitattun kalamai da mutanen da ke zaune a arewacin Indiya suka sani sosai.
Ɗaya daga cikinsu shi ne kalmar "Ek Bihari Soo Par Bhari", wadda Salman Khan ya furta a cikin fim ɗin.
Wani kalamin da ya yi a fim ɗin shi ne: "Ka tuna da abu guda; jarumtaka ba ta tsaya ga yin yaƙi kawai ba, har ma da iya dakatar da shi."

Asalin hoton, Salman Khan Films
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kafin wannan fim, an fitar da wani ɗan gajeren tallansa a ranar 27 ga watan Disamban bara, a lokacin da fim ɗin ke ɗauke da sunan Battle of Galwan. Labarin fim ɗin ya ta'allaka ne kan ƙazamin faɗan da aka yi tsakanin sojojin India da na China a kwarin Galwan a shekarar 2020.
Tun da farko, an tsara fara nuna fim ɗin a gidajen sinima a ranar 17 ga watan Afrilun 2026, amma daga bisani aka ɗage ranar.
Bayan fitar da tallar fim ɗin, kafar yaɗa labarai ta Global Times, wadda ake ganin tana da kusanci da gwamnatin China, ta soki fim ɗin, inda ta bayyana shi a matsayin farfagandar siyasa kan batu mai matuƙar muhimmanci.
Bayan cece-ku-cen da ya biyo baya, Salman Khan ya sanar a shafinsa na Instagram a watan Maris cewa an sauya sunan fim ɗin. Hakan ya sa masu amfani da shafukan sada zumunta da dama suka bayyana matakin a matsayin yunƙurin faranta wa gwamnatin India rai.
A cewarsu, gwamnatin India ba ta son fim ɗin ya ƙara dagula dangantakarta da China.
Sai dai Salman Khan ya yi watsi da rahotannin da ke cewa an sauya labarin fim ɗin ne sakamakon matsin lamba daga gwamnati, lokacin da yake fitar da sabon tallan fim ɗin.
Arangamar dai ta faru ne a kwarin Galwan a ranar 15 ga watan Yunin 2020, inda ta yi sanadin mutuwar sojojin India 20 da kuma aƙalla sojojin China huɗu.
Farkon fim ɗin ya nuna faɗa da arangamar da aka yi tsakanin sojojin Indiya da na China. Haka kuma, fim ɗin ya ƙunshi wasu hotuna da ke nuna rayuwar sirri ta sojojin, waɗanda wasu daga cikinsu ke ɗauke da yanayi mai matuƙar taɓa zuciya.

Asalin hoton, Salman Khan Films
Ba kasafai sabon fim ɗin da Salman Khan ya fito a cikinsa yake wucewa ba tare da ya dauki hankalin masu amfani da shafukan sada zumunta ba.
Tun bayan fitar da tallar fim ɗin, masu amfani da shafukan sada zumunta da dama sun yaba da kamannin Salman Khan a fim ɗin da kuma yadda ya taka rawar da ke ɗauke da yanayi mai taɓa zuciya.
Sai dai wasu sun yi tambayoyi kan ingancin hotunan da aka ƙirƙira ta amfani da na'urar kwamfuta, da kuma ko an yi amfani da basirar AI wajen samar da wasu sassan fim ɗin.
Wasu masu kallon fim ɗin na ganin cewa amfani da koren bango wajen ɗaukar hotuna, da kuma wasu hotuna da suka yi kama da na ƙirƙira, na iya rage ingancin fim ɗin baki ɗaya.
Wani mai suna Jatin Shah ya rubuta cewa: "Waƙar taken fim ɗin Maatribhumi tana da kyau. Sai dai yadda motsin bakin jaruman bai dace da kalmomin waƙar yadda ya kamata ba, da kuma yadda mutane biyu ke rera wasu sassan waƙar, sun rage tasirinta."

Asalin hoton, Salman Khan Films
Wani masoyin jarumin fim ɗin Shah Rukh Khan ma ya rubuta cewa: "Yayana, ba ka bar mana masoyan Shah Rukh Khan wani abin da za mu yi maka ba'a da shi ba."
Wani mai amfani da dandalin Reddit mai suna IC Display kuwa ya rubuta cewa: "Ina tsammanin fim ɗin zai zama abin kunya matuƙa kuma ya gaza samun karɓuwa gaba ɗaya. Amma abin da na gani ya kasance fim ne na matsakaicin inganci. Wataƙila hakan ya fi abin da nake tsammani. Sai dai da alama Salman Khan bai nuna ƙwarewa sosai wajen taka rawarsa a fim ɗin ba."
Ya kuma ƙara da tambaya cewa: "Shin za mu taɓa ganin yana magana cikin yanayin da ya dace da yadda ake magana a zahiri a cikin fina-finansa?"
Ana sa ran fara nuna fim ɗin a gidajen sinima a ranar 4 ga watan Disamba, kuma kamfanin Salman Khan Films ne ya shirya shi.
Tuni masoyan fina-finai suka fara tattaunawa kan ranar da za a fara nuna fim ɗin da kuma yadda za a gudanar da kallonsa na farko.
Yayin da wasu ke ganin fim ɗin ya cancanci a jira fitowarsa, wasu kuma na nuna shakku kan ingancinsa.
A cikin fim ɗin, Chitrangada Singh ce ta taka rawar matar Salman Khan.
Sauran jaruman da suka taka muhimman rawa a fim ɗin sun haɗa da Mukesh Rishi, Ankur Bhatia, Zain Shah da Abhilash Chaudhary. Shi kuwa Vijay Raaz ne ya bayar da muryar ba da labarin fim ɗin.




























