Manyan alƙawura huɗu da Tinubu zai yi kamfe da su a 2027

Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bayyana irin alƙawuran da za ta nemi goyon bayan ƴan ƙasa da su domin neman ƙuri'un ƴanƙasar kan sake zaɓen shugaba Bola Tinubu a karo na biyu.
A wani taro da jam'iyyar ta gudanar, shugabanninta sun ƙaddamar da kundin manufofin da ta yi wa take da ''Sabunta fata karo na biyu'' (Renewed Hope II) da suka ce zai zama tushen kamfen ɗin shugaban ƙasar domin neman wa'adin mulki na biyu.
Jam'iyyar ta ce manufofin nata sun ta'allaƙa ne kan abin da take ganin an cimma a shekaru huɗun farko na gwamnatin Tinubu, musamman a ɓangarorin tattalin arziki, tsaro, samar da ababen more rayuwa da kuma ƙirƙirar ayyukan yi.
Kundin na ƙunshe da manyan alƙawura takwas da jam'iyyar ta ce shugaban zai yi wa ƴan ƙasar.
Inganta tsaro
Jam'iyyar ta ce za ta ɗauki ƙarin jami'an soji 28,000 tare da tura su aiki domin ƙarfafa yaƙi da ta'addanci da ayyukan ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane a faɗin ƙasar.
APC ta kuma ce tana da shirin horaswa da sabbin ƴan sanda 50,000 da za a ɗauka, tare da ƙoƙarin tabbatar da cewa akwai ɗan sanda ɗaya ga kowane mutum 400 a Najeriya.
APC ta kuma yi alƙawarin samar da tsarin aikin 'yan sandan jihohi da na al'ummomi cikin yanayi mai gaskiya da ɗaukar alhaki, ta hanyar yin gyaran kundin tsarin mulki da wasu dokoki.
Bugu da ƙari, jam'iyyar ta ce za ta ƙarfafa sa ido a kan iyakokin ƙasar tare da tura jami'an tsaron dazuzzuka (Forest Guards), da jami'an kare gonaki da albarkatun ma'adinai.
Kundin ya kuma ƙunshi sabunta ayyukan tsaro ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuƙa na musamman (drones), na'urorin tattara bayanan sirri da kuma kayan yaƙi da za a ƙera a cikin gida.
Ilimi da lafiya
A ƙarƙashin ginshiƙi na biyu na takardar manufofinta, jam'iyyar APC ta yi alƙawarin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta zuwa rabin adadinsu nan da shekarar 2031.
Haka kuma ta ce za ta ɗauki ƙarin malamai 20,000 tare da horas da su, musamman domin aiki a yankunan da ke fama da ƙarancin malamai da kayayyakin ilimi.
Jam'iyyar ta kuma yi alƙawarin inganta tsaron makarantu, da faɗaɗa damar samun ilimin kimiyya, fasaha, injiniya, lissafi da na zamani (STEM da ilimin dijital), tare da ƙarfafa koyar da sana'o'i da horon fasahohin hannu.
A fannin kiwon lafiya kuwa, APC ta ce tana da burin ƙara yawan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da ke aiki yadda ya kamata daga kashi 53 cikin 100 na yanzu zuwa kashi 90 cikin 100 nan da shekarar 2031.
Tattalin arziki da makamashi
Jam'iyyar APC ta ce za ta bai wa samar da ingantacciyar wutar lantarki muhimmanci domin tallafa wa harkokin kasuwanci, masana'antu da ci gaban tattalin arziki.
Haka kuma jam'iyyar ta yi alƙawarin faɗaɗa samar da iskar gas ta CNG domin rage kuɗaɗen sufuri da jigilar kayayyaki.
APC ta kuma ce za ta zuba jari a hanyoyin mota, layukan dogo, tashoshin jiragen ruwa da filayen jiragen sama domin sauƙaƙa zirga-zirga.
Kundin ya kuma tanadi faɗaɗa fannonin noma da masana'antu, haƙar ma'adinai, ayyukan fasahar zamani da kuma fitar da kayayyakin da ba na man fetur ba zuwa ƙasashen waje.
Inganta harkokin mulki
Jam'iyyar APC ta kuma yi alƙawarin aiwatar da wasu sauye-sauye da za su ƙarfafa harkokin gwamnati, inganta ayyukan hukumomin gwamnati.
Jam'iyyar ta ce za ta mayar da ayyukan kotuna zuwa tsarin zamani na fasahar sadarwa, ta hanyar amfani da tsarin sarrafa shari'o'i ta yanar gizo da kuma gabatar da takardun ƙara da sauran takardun shari'a ta hanyar intanet a dukkan kotunan tarayya.
A yaƙi da cin hanci da rashawa kuwa, APC ta yi alƙawarin ƙarfafa hukumomin yaƙi da cin hanci, inganta bincike da gurfanar da masu hannu a laifukan rashawa gaban kotu, da kuma dawo da dukiyoyin gwamnati da aka wawure.
A fannin hulɗa da ƙasashen waje kuwa, jam'iyyar ta ce za ta ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro a yankin Afirka ta Yamma da sauran yankuna.
Ta yaya APC za ta aiwatar da alƙawuran?
Kundin manufofin ya kuma bayyana hanyoyi huɗu na aiwatar da alƙawuran idan jam'iyyar ta yi nasara.
Hanya ta farko ita ce daƙile zurarewar kuɗaɗen gwamnati, domin samun ƙarin kuɗin gudanar da ayyukan raya ƙasa.
Sai kuma bayar da fifiko ga kammala ayyukan da aka fara tun da farko kafin ƙaddamar da sababbin ayyuka, domin kauce wa yawaitar ayyukan da ba a kammala ba.
Wani muhimmin ginshiƙin da jam'iyyar ta bayyana shi ne bai wa 'yan ƙasa damar bibiyar yadda gwamnati ke aiwatar da ayyukanta.
Kundin ya kuma yi alƙawarin cikin kwanaki 100 na farko bayan rantsuwa, gwamnati za ta wallafa cikakken bayanin manyan manufofinta.
Shin APC za ta iya aiwatar da manufofin?
Masu sharhi da bibiyar al'amuran siyasar Najeriya na ganin cewa babu abin da ya sauya kan manufofin yaƙin neman zaɓen jam'iyyar na baya da kuma waɗannan.
Farfesa Abubakar Umar Kari malami a Jami'ar Abuja, kuma mai sharhi kan al'amuran siyasar ƙasar ya ce kusan a iya cewa irin manufofin da APC ke fitarwa ne tun 2015 waɗanda ya ce an kasa aiwatar da su.
''Ƴan Najeriya sun yi tunanin cewa APC za ta faɗa musu me za ta yi a zahiri, ko kuma me ta yi a ƙasa'', in ji shi.
Masanin siyasar ya ce wannan magana ce ta fatar baki, abu ne da ƴansiyasar suka kasa aiwatarwa.
Ya ce alƙawura ne da kusan duka jam'iyyaun siyasar ƙasar ke ta maimaitawa tun 1999, amma ba sa aiwatar da su.
''Manufofi ne tun da jam'iyyar PDP, a lokacin Umaru [Musa Yar'adua]ya maida su 7 poinst Agenda, sannan aka sake karkaɗe su lokacin Buhari, su din ne dai har yanzu'', in ji Farfesa Kari.



























