Wurare 5 da Aljanu ke zama a cikin gidajenmu

Wurare 5 da Aljanu ke zama a cikin gidajenmu
    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

A fahimtar addinin Musulunci, aljanu halittu ne da Allah Ya halitta daga wuta. Ba a da hujja tabbatacciya da ke nuna cewa dole suna zaune a wani takamaiman wuri na gidan kowa.

Sai dai a cikin hadisai an ambaci wasu wurare da aljanu ko shaiɗanu suke yawan zama ko taruwa, wanda a dalilinsu malaman addini ke cewa ana fama da matsaloli.

A wani jawabi da malamin addinin musulucni Farfesa Mansur Sokoto ya yi wa BBC, ya zayyano wasu bayanai daga Alƙur'ani da hadisai kan aljanu da wuraren da suke zama a cikin gidaje.

1. Barin shimfiɗa a buɗe

...

Farfesa Mansur ya ce duk shimfiɗar da aka barta a buɗe kuma aka ɗauki dogon lokaci, "aljanu za su zo su zauna a kai."

Don haka Farfesa Mansur ya ce duk shimfiɗar da aka gama amfani da ita, yana da kyau a nannaɗe ta a ajiye ta a wani wuri.

Wannan ya zo a Sunnah kamar yadda malamin ya ce a hadisi, Manzon Allah (S.A.W.) ya ce: "Shimfiɗa iri huɗu ce. Ta ɗaya, shimfiɗar da ake zama a kai, kamar kafet. Sai shimfiɗar da ake yi wa baƙo. Sai shimfiɗar maigida."

Malamin ya ƙara da cewa Annabi ya ce shimfiɗa ta huɗu, ta "aljanu ce". Saboda haka yana da kyau duk shimfiɗar da aka kammala amfani da ita a naɗe ta.

2. Banɗaki

Banɗaki

Makewayi ko banɗaki na cikin wuraren da Sheikh Mansur ya ce ya tabbata a hadisi cewa aljanu na zama a ciki.

"Komai tsaftar banɗaki, aljanu suna son sa kuma suna zama a wajen," in ji malamin.

Farfesa Mansur ya ce "a cikin duk shaidanun duniya babu hatsabibi kamar aljanin banɗaki", shi ya sa a cewarsa ake shan wahala wajen ruƙiyya idan aljanin banɗaki ya shiga jikin mutum.

Malamin ya ce makamin irin wannan shi ne addu'a, kamar yadda ya zo a hadisi cewa: "Waɗannan banɗakuna, aljanu suna zuwa cikinsu... Don haka duk wanda zai shiga banɗaki ake so ya yi addu'ar 'A'uzu billahi minal-khubusi...'."

3. Rataye kaya ba a saka ba

...

Farfesa Mansur ya ce duk lokacin da mutum ya cire kaya ya rataye su ba tare da ya sake saka su ba har na dogon lokaci, kuma ba a wanke su ba, akwai yiwuwar aljanu za su shiga cikinsu.

Malamin ya ce idan mutum ya cire kaya, ana son ya ninke su, ko da a cikin durowa ne.

Ya ce a hadisi an ruwaito Manzon Allah (S.A.W.) na cewa: "Ku riƙa naɗe tufafinku, domin sheɗan yana shiga cikin duk tufafin da ba a naɗe ba."

Saboda haka malamin ya ce yana da kyau iyalai su kula da rataye kaya a ko'ina ba tare da an saka su ba.

Idan kuma har sun daɗe ba a yi amfani da su ba, to malamin ya ce a riƙa tofa addu'ar "A'uzu billahi" a cikin kayan kafin ɗaukar wani abu.

4. Hotuna ko mutum-mutumi

Doll

Malamin ya ce a fahimtar addinin musulunci, ajiye hotuna masu suffar jiki ko mutum-mutumi masu siffar dabbobi ko mutane na janyo aljanu a wajen.

Ya ce ajiye irin waɗannan abubuwa na hana mala'iku shiga cikin gida, wanda hakan ke sa aljanu na samun wajen zama.

"Idan mala'ika bai shigo ba, shi kuma shaiɗan zai shigo ya sha inuwar wannan," in ji Sheikh Mansur.

5. Wajen da ake hura wuta

...

Malamin ya ce a fahimtar addinin Musulunci, ajiye hotuna masu siffar jiki ko mutum-mutumi masu siffar dabbobi ko mutane na janyo aljanu a wajen.

Ya ce ajiye irin waɗannan abubuwa na hana mala'iku shiga gida, wanda hakan ke sa aljanu samun wurin zama.

"Idan mala'ika bai shigo ba, shi kuma shaiɗan zai shigo ya sha inuwar wannan," in ji Sheikh Mansur.

Babban makami
Farfesa Mansur Sokoto
Bayanan hoto, Farfesa Mansur Sokoto

A cewar Sheikh Mansur Sokoto, babban makamin kariya daga aljanu da dukkanin sharrin shaidanu shi ne addu'a da yawan ambaton Allah.

Idan bawa ya kasance mai tsayawa kan addu'o'i da azkar na safe da yamma, yana samu kariyar Ubangiji daga duk wani sharri da ba a gani. Wannan yana kara kusanci tsakanin mutum da Allah tare da karfafa imaninsa.

Haka kuma, karatun Alƙur'ani, musamman Ayatul Kursiyyu da Suratul Baqarah, na daga cikin manyan hanyoyin da ke korar shaidanu da aljanu masu cutarwa.

Gidan da ake yawan karatun Alƙur'ani da zikiri yakan kasance cikin albarkar Allah, kuma shaidanu ba sa samun damar yin tasiri cikin sauƙi a cikinsa.

Saboda haka, Musulmi ya kamata ya dage da addu'a, istigfari, da ambaton Allah a kowane lokaci.