Da gaske duniya za ta tashi ranar 13 ga watan Nuwamba?

Dunida
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Yayin da wannan rana ke ƙara gabatowa, ana sake tattauna fargabar "ƙarshen duniya" sosai a kafafen sada zumunta da kuma wasu kafofin yaɗa labarai.

Wannan rana tana da alaƙa da wani binciken kimiyya da aka wallafa shekaru 66 da suka gabata, wanda ya yi ƙoƙarin hasashen makomar yawan al'ummar duniya.

Masu bincike uku ne suka rubuta wannan bincike, kuma an wallafa shi a mujallar kimiyya ta Amurka mai suna Science a ranar 4 ga Nuwamba, 1960.

Taken binciken shi ne: "Doomsday: Friday, November 13".

Masu binciken sun bayyana a cikin nazarinsu cewa idan yawan mutanen duniya ya ci gaba da ƙaruwa da irin saurin da bayanan da suka nazarta na kusan shekara 2,000 suka nuna, to bisa ga hasashensu, yawan al'ummar duniya zai kai matakin da ba za su iya rayuwa a duniyar ba zuwa watan Nuwamba na shekarar 2026.

Sai dai, shin da gaske masu binciken suna magana ne a kan bacewar bil'adama?

Shin wannan rana tana da wata muhimmiyar ma'ana ta kimiyya da ke nuna yiwuwar wata babbar masifa ko wani lamari na duniya da zai iya jawo ƙarshen rayuwa a doron ƙasa?

Daga ina wannan labarin ya samo asali?

Sheeko
Bayanan hoto, Maqaal uu Michel Tekla ku qoray wargeyska Masar ee Watani

Wannan bincike ya samo asali ne daga masanin kimiyyar lissafi nan haifaffen Austria, Heinz von Foerster, mazaunin Amurka.

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya gudanar da wannan bincike tare da wasu mutum biyu, Patricia Mora da Lawrence Amiot. Dukkansu uku mambobi ne na Sashen Injiniyan Lantarki na University of Illinois da ke Amurka.

Masu binciken sun yi amfani da kimantawa ta tarihi kan yawan al'ummar duniya. Bayanansu sun kunshi kimantawa 24 da aka tattara daga farkon zamanin Miladiyya har zuwa shekarar 1958.

Sun yi amfani da wadannan bayanai domin fahimtar yadda yawan jama'ar ɗan'adam ya karu a tsawon tarihi.

Masu binciken ba su gina nazarin nasu kan hasashen cewa yawan mutanen duniya na karuwa ne da daidaitaccen kaso ba.

Maimakon haka, sun gabatar da wani tsarin lissafi da ya dogara da manufar karuwar jama'a mai tsanani, wadda aka sani da suna Hyperbolic Growth.

A cikin wannan tsarin, ba wai yawan jama'a kadai ke karuwa ba, har ma da saurin karuwar yana dada habaka yayin da lokaci ke tafiya.

Wannan tsarin lissafin ya ginu ne kan ra'ayin cewa ikon ɗa'adam na mu'amala da wasu, taimakon juna da kuma kulla hadin gwiwa yana taimaka masa wajen shawo kan wasu daga cikin kalubalen muhalli.

Hakan na kara wa dan Adam karfin rayuwa da haihuwa.

Bayan amfani da wannan ka'idar lissafi kan bayanan tarihi, masu binciken sun kammala cewa tsarin nasu zai kai wani matsayi da ake kira singularity a shekarar 2026. Wannan lokacin zai kasance a tsakiyar watan Nuwamban 2026.

Saboda haka ne ranar 13 ga watan Nuwamban 2026 ta zama wani bangare na taken binciken.

Bisa ga tsarin lissafin, a wannan ranar ne yawan mutanen duniya zai kai matakin da ba shi da iyaka a bisa ka'ida idan har aka ci gaba da amfani da irin wadannan sharudda da hasashen ba tare da wani canji ba.

A kallon farko, taken binciken na iya zama kamar wani hasashe ne game da karshen duniya, amma hakikanin ma'anarsa ta bambanta gaba daya.

Masu binciken ba su yi hasashen cewa wani babban dutse zai bugi duniya daga sararin samaniya ba, ko cewa rana za ta fashe, ko kuma girgizar kasa da aman wuta za su haddasa gagarumin bala'i.

Haka kuma ba su ayyana wata ranar da dan Adam zai bace sakamakon wata masifar halitta ba.

A hakikanin gaskiya, sun yi amfani da kalmar "doomsday" ne domin bayyana wani yanayi na lissafi da ake hasashe, inda yawan jama'a zai kai matakin da ba shi da iyaka bisa ga ka'idarsu.

Wannan kuwa ba abu ne mai yiwuwa a zahirin duniya ba.

A wasu kalmomi, wannan adadin da ba shi da iyaka ba yana nufin cewa yawan mutanen duniya zai kai wannan adadin da gaske ba ne.

Yana nufin sakamakon lissafi ne kawai da ke fitowa idan aka yi hasashen gaba bisa zaton cewa dukkan sharuddan da aka gina tsarin a kansu za su ci gaba da kasancewa yadda suke ba tare da wani sauyi ba.

Karanta ainihin binciken ya nuna cewa masu binciken sun fahimci cewa ba za a iya amfani da wannan hanya yadda ya kamata ba tare da la'akari da tasirin muhalli, albarkatu da sauran yanayin da ke kewaye da al'umma ba.

Wadannan abubuwa ne da za su iya yin tasiri ga yawan haihuwa da mace-mace, tare da sauya alkiblar karuwar yawan jama'a.

Mece ce alaƙar binciken da muƙalar da aka wallafa a 1964?

Dunida

Jaridar Masar mai suna Waddani ta kuma wallafa wani hoto da aka dauko daga wata tsohuwar jarida mai dauke da kwanan watan 29 ga Nuwamban 1964.

An sanya wa labarin hannu da sunan wani marubuci mai suna Michel Tecla, kuma kanun labarin ya yi iƙirarin cewa duniya za ta kare a ranar 13 ga Nuwamban 2026.

Bayan haka, wasu kafafen yada labarai na Masar sun sake wallafa hoton wannan tsohon labari.

Hakan ya sa wannan batu ya sake fitowa fili fiye da shekaru sittin bayan haka.

Sai dai yana da muhimmanci a bambanta tsakanin rubutun da aka wallafa a kafar yada labarai da kuma ainihin binciken kimiyya.

Binciken da ya shafi ranar 13 ga Nuwamban 2026 an wallafa shi ne a shekarar 1960 daga Heinz von Foerster tare da wasu abokan aikinsa biyu masu bincike, ba daga Michel Tecla ba.

Kafafen yada labaran da suka sake tabo wannan batu a baya-bayan nan su ma sun gabatar da abin da ke cikin labarin Tecla ta hanyoyi daban-daban.

Wasu rahotannin sun danganta rubutun da binciken da ya shafi karuwar yawan jama'a, yayin da wasu suka ambaci hasashe da suka shafi ayyukan rana, sauyin yanayi da kuma bala'o'in halitta.

Saboda haka, ba daidai ba ne a dauki duk wadannan hasashe a matsayin wani bangare na ka'idar kimiyya guda daya, ko a ce su ne sakamakon binciken Von Foerster, har sai an samu cikakken rubutun asalin labarin kuma an kwatanta shi da abin da binciken kimiyyar ya kunsa.

Ayyukan rana

Qorraxda

Wasu rahotannin kafafen yada labarai da suka danganci makalar Michel Tecla sun kuma yi ikirarin cewa za a samu wani sabon yanayi na musamman a harkar ayyukan rana a ranar 13 ga watan Nuwamban 2026.

Wadannan rahotanni sun haifar da fargabar cewa hakan na iya jawo tangarda ga filin maganadisu na duniya tare da haddasa bala'o'in kasa da na halitta.

Sai dai yana da muhimmanci a bambanta tsakanin guguwar rana da ke faruwa a zahiri da kuma ikirarin cewa za a samu guguwar rana a wata takamaimiyar rana.

Ayyukan rana wani sanannen lamari ne na halitta.

Rana tana da zagayowar lokaci da matakin ayyukanta ke canzawa.

A lokacin wadannan zagayowar, wani lokaci ana samun manyan fashewar abubuwan da ke fitowa daga rana da kuma walƙiyar rana, wadanda za su iya yin tasiri ga filin maganadisu na duniya.

Guguwar rana mai karfi na iya jawo cikas ga hanyoyin sadarwa, tauraron dan adam da tsarin kewayawa. Haka kuma tana iya shafar hanyoyin samar da wutar lantarki.

Sai dai wadannan hadurran ba sa nufin cewa rana za ta hallaka duniya a wata takamaimiyar rana.

Binciken da aka wallafa a mujallar Science a shekarar 1960 game da karuwar yawan jama'a bai gabatar da wata hujja da ke alakanta ranar 13 ga watan Nuwamban 2026 da ayyukan rana ko kuma bala'o'in karkashin kasa da na yanayi ba.